1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Uncategories » Rasuwar Kwamishinan Zaben Kano Da Iyalinsa: Boyayyun Bayanan Da Ba A Sani Ba

Rasuwar Kwamishinan Zaben Kano Da Iyalinsa: Boyayyun Bayanan Da Ba A Sani Ba

By Abdul Mk
Add Comment
Monday, 13 April 2015

A karshen makon jiya ne al’ummar Kano ta wayi gari cikin jimami da alhinin rasuwar Kwamishinan Zaben Jihar, Alhaji Abdullahi Munkaila da iyalansa baki daya a cikin mummunan gobarar da ta auku a gidansa, da ke Lamba 2, kan titin Sir Kashim Ibrahim, a rukunin gidajen masu kudi na Nasarawa GRA, wanda har lokacin da wakilanmu ke harhada wannan rahoton, ba a san dalilinta ba. Sahihan rahotanni sun tabbatar cewa sananin zafi da hayaki ne suka yi sanadiyyar mutuwar kwamishinan tare da matarsa da kuma ‘ya’yansa mata guda biyu a take.

Gobarar dai, kamar yadda LEADERSHIP HAUSA ta gano, ta tashi a gidan Kwamishinan ne cikin taltainin dare, lokacin da suke barci. Tun da farko, kamar yadda wakilanmu suka ruwaito, har an fara yada jita-jitar cewar watakila ko wani shiri ne aka yi na kashe kwamishinan hukumar zaben mai alaka da siyasa. Sakamakon haka jami’an rundunar ‘yan sandan Jihar Kano suka gayyaci manema labarai zuwa wurin da al’amarin ya faru domin karyata jita-jitar da ake yi.

Kwamishinan ‘yan Sanda na jihar Kano, Ibrahim Idris ya bayyana cewar sakamakon binciken farko ya nuna cewar hayakin wutar ne ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen. Kwamishinan ‘yan Sandan ya bayyana cewar yau juma’a da misalin karfe hudu na yamma, ‘yan sandan dake aiki a gidan Kwamishinan zaben suka lura da wuta daga jikin wata na’urar sanyaya daki ta falon gidan. Duk kokarin da suka yi na tuntubarsa ta gagara ta hanyar buga kofa da kuma karya wasu tagogin ban-dakin gidan, amma ba su samu jin komai daga gare shi ba. Karshe dai, kamar yadda hukumar ‘yan sandan suka sanar, jami’an ‘yan sandan da ke gadin gidan tare da hadin gwiwar wani mai gadin gidan, suka karya kofar falon suka iske hayaki ya turnuke falon. Daga nan suka karya kofar dakin mai gidan, amma ba su iske shi ciki ba, sai suka shiga ban-daki, inda nan suka kuma iske shi da matarsa tare da ‘ya’yansa biyu cikin halin mutu-kwakwai-rai-kwakwai.
A daidai lokacin ne suka garazaya da su babban asibitin kwararru na Murtala, wato asibitin Murtala, inda likiotci suka tabbatar da rasuwarsu sakamakon zafi da hayaki.

Guda daga cikin masu gadin, wani mai suna Habibu Yusif, ya bayyanawa wakilinmu cewar cikin dare suka hangi hayaki na fitowa daga wata na’urar sanyaya daki, hakan ta sa suka firigita tare da neman hanyar shiga gidan, amma duk kofofoin a kulle. Ya ce, “Tun daga waje muka hangi wuta ta fara ci daga na’urar A/C na gidan, muka gaggauta neman hanyar kashe ta, amma abin ya gagara, muka ci gaba da neman yadda za mu shiga gidan, sai gatari mu ka sa, mu ka karya kofar shiga falon gidan, amma saboda tsananin hayaki, abokin aikina, daya daga cikin ‘yan sanda da ya yunkura don shiga, ya kasa, sau uku yana faduwa saboda zafi da kuma hayaki.

“Wallahi wannan mutuwa ta mai gidana, ta gigita mu, mutumin kirki, kullum duk fitar da ya yi idan ya dawo sai ya shigo mana da dan abin sha’awa ya raba mana,” in ji Habibu mai gadi.

Wakilanmu sun yi sa’ar tattaunawa da daya daga cikin makwabtan kwamishinan, kuma mataimaki na musamman ga Gwamna Kwankwaso, Alhaji Nafi’u Dan Kura, inda ya bayyana cewa, “Duk da wannan bawan Allah bai jima da tarewa a wannan gida ba, amma ko shakka babu mutumin kirki ne mai kaunar zumunci da taimakon duk wanda ke aiki tare da shi da sauran jama’a.” Nafi’u Dan kura ya yi addu’ar Allah ya gafarta kura-kuransa.

Shi ma wani ma’aikacin hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Kano, wanda kuma ke aiki kai tsaye da Kwamishinan ya bayyana marigayin da cewar mutum ne wanda irinsa ba su da yawa cikin al’umma. Ya ce, “Alal hakika irin su Alhaji Munkaila ba su da yawa a cikin al’umma a yau. Sam bai damu da matsayinsa ba, kullum fatansa me zai yi ya kyautatawa jama’ar da yake jagoranta, wallahi mun yi babban rashi, musamman a daidai wannan lokacin da ake tsananin bukatar irinsa.” Bayan tababtar da rasuwar tasu ne kwamishina ‘yan sandan jihar Kano ya jagoranci gawar mamatan zuwa Dutsen jihar Jigawa wanda nan ne mahaifarsa inda aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Islama ya tsara. Babban limamin Dutse ne ya salalci gawar mamatan. Wakilanmu sun ruwaito mana cewa cikin wadanda suka shaida wannan jana’izar, har da shugaban hukumar Zabe ta Kasa, Farfesa Attahiru Jega, Gwamna Sule Lamido, Sakataren gwamnatin jihar Kano Injiniya Rabiu Sulaiman Bichi da sauran manyan mutane.

Daya yake amsa tambayoyin manema labarai, Farfesa Attaahiru Jega, ya bayyana Marigayi Abdullahi Munkaila da cewa daya ne daga cikin jami’an hukumar zaben da ya gamsu da aikinsu. Jega ya ce, “Rasuwar Alhaji Munkaila ta tayar mini da hankali kasancewar sa nagartaccen ma’aikaci mai gaskiya da sanin ya kamata, ina masa fatan samun kyakkyawar tarba a cikin kabarinsa, Allah ya kyautata makwancinsa a cikin Aljannar Firdausi,” in ji Farfesa Jega.

A lokacin da LEADERSHIP HAUSA ta gana da daya daga cikin abokai kuma aminan marigayin, Alhaji Haruna Bello Gantsa, wanda tare suka taso tun daga makarantar Furamare, har zuwa ranar da Abdullahi Munkaila ya koma ga mahaliccinsa, ya bayyanawa wakilinmu yadda suka taso da kuma cikakken halinsa. Ya ce, “Tun shekara ta 1969 tare muke domin garinmu daya Furamaren mu guda. A shekara ta 1969 ne muka rabu shi, ya tafi makarantar Furamare ta kwana a Rano, ni kuma na tafi Kwalejin Rumfa na Kano. Abdullahi Munkaila ya fara aiki a 1975 a ma’aikatar jin dadi da walwalar jama’a, inda aka fara tura shi makarantar kurame ta Tudun Maliki da ke jihar Kano. Ya halarci Kwalejin Kimiyya da Fasaha na Kaduna, har ya samu takardar shaidar kammalawa a 1978.

“A lokacin Gwamna Rimi, aka mayar da shi makarantar lura da nakasassu dake Mariri. Haka kuma a watan Satumbar 1991 aka Kirkiri Jihar Jigawa, daidai lokacin ne Abdullahi Munkaila ya kasance daga cikin mutane na farko, wadanda suka koma Jigawa da iyalansu. Ya zama darakta daga nan kuma Gwamna Sule Lamido ya yi masa Sakataren dindindin, matakin da yake kai har lokacin da ya yi murabus daga aiki a shekara 2012.

“Wata rana muna cin abinci da Gwamna Sule Lamido, sai ya ce da Abdullahi Munkaila da ya je wajen Shugaban ma’aikata, bayan ya je wurinsa ne ya tabbatar masa da cewar an bayar da sunansa a matsayin Kwamishinan zabe daga jihar Jigawa. Bayan halartar tantancewa ne aka fara tura shi Jihar Kebbi a matsayin Kwamishinan hukumar zabe mai zaman Kanta. Daga baya aka dawo dashi jihar Kano a matsayin Kwamishinan hukumar Zabe. Bayan sanar da sakamakon zaben shugaban Kasa da kwanaki biyar da misalin Karfe shida da minti ashirin da hudu, Isa Garba Gantsa ya kira ni tare da yi min ta’aziyya cewar Abdullahi Munkaila rai ya yi halinsa,” in ji aminin marigayin. Ya kara da cewar yana kwadayin cikawa irinta amininsa Abdullahi Munkaila, musammam saboda kyawawan halayensa. “Da farko a iya sanina Abdullahi Munkaila ko mai wankin kaya ba shi da shi dakan sa yake wanki, sannan kuma duba kaga sakon karta kwanansa na karshe da ya turo min, wanda kuma duk juma’a sai ya turo sakon, ka ganshi: “A PERSON‘S HEART PLAN HIS HIS WAY , BUT ALLAH DIRECTS HIS STEPS. MAY ALLAH IN HIS INFINITE MERCY DIRECT YOUR STEPS TO THE BEST OF ALL DIRECTIONS. JUMA’AT MUBARAK.” Allah sarkin iko! Ka ji fa irin kalamansa. Bayan haka, ni ne na yi masa babban aboki a aurensa na fari kuma ni na yi masa wankan gawa. Bayan Allah ya karbi abinsa, muna yi masa wanka wallahi kamar wanda ke barci, sannan kuma babu ko da tabon Kunar Wuta a jikinsa, in banda hayaki da muka sa sabulu muka wanke shi tas,” in ji Haruna Gantsa.

Marigayin ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya ‘ya goma. Amaryar ce da ‘ya’yanta biyu, Allah ya karbi ransu tare, amma tare suka zo Kano har da uwargidan domin halartar wani biki, ita uwar gidan na can gidan bikin lokacin da lamarin ya faru, sannan kuma akwai wasu a kasan gidan, ciki har da guda cikin ‘ya’yan uwar gidan, Allah ya fitar da su, kamar yadda wakilanmu suka ruwaito mana.

A daren ranar Juma’ar makon da ya gabata ne wata mummunar gobara wadda har zuwa yanzu ba’a gano musabbabinta ba ta yi sanadiyyar halakar kwamishinan zabe na jihar Kano Alhaji Munkaila Abdullahi tare da matarsa da kuma ‘ya’yanta mata guda biyu.

Leadership hausa ta tattauna da dan uwa kuma kanen dake bin marigayar wato amaryar marigayi Alhaji Munkaila Abdullahi yadda ya bayyana alhininsa tare cikakken bayanin kowacece marigayar.haka kuma ya fara da bayyana mana sunan kamar haka: A yayin da yake furta alhinin da ke zuciyarsa, dan’uwan mai dakin kwamishinsa, Malam Auwal Dalha ya bayyana cewa ‘yar’uwarsa, Zulaihatu, wadda ta rasu tare da mijinta da ‘ya’yanta, tana da shekaru 32 ne a duniya. “Ina mai jimamin sanar da ku cewa yayata, Zulaihatu Dalha ta bar duniya tana da shekaru 32 tare da ‘ya’yanta biyu.
“Mahaifinmu kuma dan asalin garin Majiya ne dake karamar hukumar Taura a Jihar Jigawa, amma yanayin aiki ya kai shi Bebeji dake jihar Kano yadda a nan aka haifi Marigayiya Zulaiha. Ta yi karatun firamare a garin na Bebeji bayan kammala karatun firamare sai kuma ta shiga makarantar sakandiren ‘yan mata dake Garin Tudun wada a karamar hukumar Tudun wada da ke jihar Kano.

“Bayan kammala karatun sakandiren ne marigayiya ta kuma ci gaba da karatu a Kwalejin shari’a da ke Ringim a Jihar Jigawa yadda ta kammala ta kuma fita da shaidar Difiloma.

Ta kasance Amaryar Alhaji Munkaila Abdullahi kuma sun haifi ‘ya’ya uku tare da shi yadda daya ya rasu kafin daga bisani wannan gobara ta faru, su ma ragowar biyun suka rasu tare da mahaifan nasu baki daya.

‘Ya’yan marigayiyar guda biyu duk sun kasance mata Asma’u Munkaila mai shekaru uku da rabi da kuma A’isha Munkaila mai shekaru biyu da haihuwa kafin rasuwarsu,” in ji shi.

Malam Auwal ya bayyana marigayiya Zulaiha a matsayin mace mai addini tausayin ‘yan’uwa gami da son zumunci duk da ksancewarta tana nesa da gida.

“Babu ko shakka mutuwarta ta girgiza mu, kuma ba ma tsammanin za a samu wanda zai maye gurbinta a danginmu baki daya. Kuma muna yi mata addu’ar Allah ya gafarta musu ya kyale laifinsu, ya kuma kai rahama kabarurrukansu baki daya.”

Tuni dai aka gabatar da Jana’izarsu kamar yadda addinin musulunci ya tanada a babban masallacin Juma’a dake birinin Dutsen jihar Jigawa.

Wasu daga cikin mayan mutanen da suka halarci Jana’izar tasu sun hada da Gwamna Sule Lamido, Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) Farfesa Attihu Muhammad Jega, Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Mai Martaba Sarkin Dutse, wakilan Mai Martaba Sarkin Kano da kuma sauran dumbin al’ummar Musulmi. Abubuwansa Na Karshe
Ana saura kiris ya bar duniya, Marigayi Alhaji Munkaila ya aikata wadannan abubuwa:

Sakon kar-ta-kwana (TES) ya turawa abokinsa (Haruna Gantsa).
Taro na karshe da jami’an Hukumar Zabe, a nan aka ji shi yana cewa: ‘Kowa ya kula da aikin kowa, wannan aikin daga bana sai badi.’
Ado Sale Kankiya ya kira shi ranar Alhamis yana sanar da shi cewar shi ne babban bakonsu ashirin gidan Radion Freedom na Barka da hantsi na ranar Juma’a, ya kuma amsa da cewa: ‘Allah nuna mana goben lafiya.’
Cikin abubuwa da jama’a ke ta tunawa har da jawabin da ya gabatar kwana biyu kafin rasuwarsa, inda ya bayyana cewar shirye-shirye sun kammala na zaben gwamna mai zuwa ranar Asabar, ya ce sun tanadi wurin da dukkan ma’aikatan zaben za su kwana tare da samar da dukkan abubuwan bukata domin da zarar asuba tayi ga motocin nan mun tanada kai tsaye za a dauke su zuwa wuraren aikinsu. Haka kuma Ranar Juma’ar da Allah Ya karbe ran Abdullahi Munkaila an shirya gudanar da tattaunawa kai tsaye akafafen yada labarai kan batun zaben Gwamna da na ‘yan majalisar jihar Kano.

Hausa Leadership hausa

Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Abdul Mk at 14:30
Title : Rasuwar Kwamishinan Zaben Kano Da Iyalinsa: Boyayyun Bayanan Da Ba A Sani Ba
Description : A karshen makon jiya ne al’ummar Kano ta wayi gari cikin jimami da alhinin rasuwar Kwamishinan Zaben Jihar, Alhaji Abdullahi Munkaila da iya...
Rating : 5
Related Posts:

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Rasuwar Kwamishinan Zaben Kano Da Iyalinsa: Boyayyun Bayanan Da Ba A Sani Ba"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ►  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ►  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ▼  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ▼  April (187)
      • AWOYIN DA YAKAMATA ANA SAMU NAYIN BACCI
      • **Tunatarwa Guda 5 Ga Musulmi* *
      • Remain In PDP, We Don’t Need You-APC to WIKE
      • 64 Senators Endorse Bukola Saraki For Senate Presi...
      • Change Buhari promised will not happen overnight –...
      • MAI KIWON SHANU DA KARENSA
      • ME ZA'AYI YAU MAI GIDA? ''YACE KUNU''
      • DOMIN KE DA MIJINKI Part 6
      • DOMIN KE DA MIJINKI Part 5
      • DOMIN KE DA MIJINKI Part 4
      • DOMIN KE DA MIJINKI Part 3
      • DOMIN KE DA MIJINKI Part 2
      • DOMIN KEDA MIJINKI Part 1
      • KO KASAN KAKAN MUTU A RANA SAU (5) WANI LOKACIN?
      • INA MASU SAURIN KAWOWA A LOKACIN JIMA'I ???
      • Why Our Prayers Are Not Accepted
      • *** WAYYO NI NURUL AYN 003 ***
      • *** WAYYO NI NURUL AYN 002***
      • *** WAYYO NI NURUL AYN 001 ***
      • Fitsaranci Alokacin Bikin Aure
      • Jinnul Ashiq - Aljanin Soyayya
      • Daga Cikin Abubuwan Mamaki Wadanda Na Gani Akan Sh...
      • Mafi Qazantar Sihiri
      • I’m ready for probe, says FCT minister
      • I did not ask anyone to bar AIT from covering my a...
      • Chibok girls found? Nigerian troops find 200 girls...
      • DAUKEWAR RUWAN NONO
      • HANYOYIN RABUWA DA MASTURBATION
      • MATSALAR DA YA SHIGA SAKAMAKON SA'BA MA ALLAH TA H...
      • MAGANIN SHAFAR ALJANU DAGA ZAUREN FIQHU
      • GA WANI ALBISHIR
      • WANI LABARI MAI GIRGIZA ZUCIYA!
      • HALACCIN ZIYARTAR QABARI
      • MAGANIN QARIN KUZARIN NAMIJI.
      • MATSALAR KANKANCEWAR ALKALAMI
      • ABINCIN ZUCIYA
      • MATSALAR KANKANCEWAR ALKALAMI
      • QARIN BAYANI AKAN ALJANUN GADO
      • GORON JUMA'AH
      • FALALAR ALQUR'ANI
      • KU SAURARA KUJI
      • HUKUNCIN ALWALAR WANDA YA KALLI TSARAICI
      • YANA CIKIN BABBAR MATSALA
      • BA WAI MUTUWA CE ABIN TSORO BA.
      • YAWUN BAKIN MA'AIKINA (SAWW)
      • ALAMOMIN MASU TSORON ALLAH
      • HAMZA THE LION OF ALLAH
      • HALIMATUS SA'ADIYYAH (RA)
      • ALIYYU BN ABI TALIB (RTA)
      • Buhari bars AIT from covering his activities
      • 21 killed by Boko Haram in Yobe today
      • 21 killed by Boko Haram in Yobe today
      • FIQHU ASAUKAKE - DAGA ZAUREN FIQHU (DARASI NA 9).
      • This is daylight robbery.. Aisha Alhassan
      • Gen Buhari signifies interest to probe alleged mis...
      • Fulani Gunmen Kill 30 In Benue, Nasarawa
      • Okorocha, Ikpeazu win •PDP leads in Taraba
      • Bomb blast reported in Plateau
      • Marte Town Capture by 2000 Boko Haram Members
      • Boko Haram chase Nigerian troops from Sambisa
      • EFCC set to declare Ali Modu Sherrif a Wanted Man
      • GMB and GEJ Meet in Abuja today
      • GORON JUMA'AH
      • FALALAR ALQUR'ANI
      • Jonathan orders removal of campaign posters nation...
      • HUKUNCIN ALWALAR WANDA YA KALLI TSARAICI
      • WACECE MACE TAGARI? WAYE MIJI NAGARI?
      • Dalilin Da Yasa Matasa Suke Aure Yanzu
      • MATANSA SUN GALLABESHI
      • YADDA AKE TUBA DAGA LAIFIN ZUWA WAJEN BOKA
      • Rahma Sadau and Friend released new Pictures
      • Photos: Emir of Kano pays Gen. Buhari congratulato...
      • Gunmen kill El-Rufai’s campaign coordinator
      • Fire guts popular ​Kano shop
      • HUKUNCIN WANDA YA FIDDA MANIYYI DA AZUMI
      • MAGANIN SANYI NA YARA
      • DUNIYA TA RIGA TA AUREKA :
      • DAGA CIKIN ILLOLIN ZINA
      • IDAN AJALIN MUMINI YAYI
      • LABARIN ANNABI ISA (AS) DA WANI MUTUM MAI KWADAYIN...
      • KU DUBA WANNAN GIRMA
      • ALIYYU BN ABI TALIB (RTA)
      • Eight injured in failed suicide bomb attack in Pot...
      • LUQMAN AL-HAKEEM
      • LABARIN ANNABI ISA (AS) DA WANI MUTUM MAI KWADAYIN...
      • PDP’s sins will soon start coming out,’ President-...
      • Soldier, lawyer die in Bauchi roach crash
      • Jonathan demands N2tn Election funds return
      • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
      • MAZINACIYA MAI MUMMUNAN TARIHI
      • Boko Haram Slits The Throats Of 12 People In Gwoza...
      • SOYAYYA TA SANYATA SAUYA ADDINI Part 2
      • MATA 10 WAINDA ALLAH YATSINE MUSU
      • Kuskure Guda 50 Alokacin Bawa Yaro Tarbiyya
      • Makircin Iblees
      • APC rejects May 28 handover date
      • DUTSE YA SACE KAYAN ANNABI MUSA
      • YANA TAMBAYA AKAN ZAITUL LAWZ
      • MAI TSARKIN ASALI (SAWW).
      • Rahma Sadau released hot new Pictures
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • The Missing seven-year-old boy found dead in Kano
    Seven-year-old Khalifa Saminu Saleh was tragically found deceased six days after he was reported missing in the Kuruma community...
  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Rikicin Tsakanin Hadiza Gabon Da Zaharadeen Sani ( Bayanai Da Rahoto) S...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...
  • (New Music) Reason By Peevibes
      PeeVibes - Reason Williams Akinsola Precious Popularly known as peevibes has returned again with this mind blowing song tagged “Reason”. T...
  • Innalillahi wainna illaihin rajiun - Allah Yayi Wa Mawaki Aliyu Sharba R...
  • Suspect - Episode 1 ( Dj Giggs ft J Prince ft Nabs Kid) Hausa HipHop Ser...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger