1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Fadakarwa » HALAYEN MANZON ALLAH (SAWW)

HALAYEN MANZON ALLAH (SAWW)

By Abdul Mk
Add Comment
Tuesday, 24 March 2015

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

Salati da aminci su tabbata bisa fiyayyen halittu, Annabinmu Shugabanmu Muhammadu tare da tsarkakan iyalan gidansa masu albarka, da yardaddun Sahabbansa masu kwazo da dukkan mabiyansa har zuwa ranar Alkiyama.

Har yanzu dai muna magana ne akan hakurinsa (saww).

5. HAKURINSA BISA JINYA KO RASHIN LAFIYA IDAN TA SAMESHI (SAWW).

* Sayyiduna Abdullahi bn Mas'ud (Allah shi yarda dashi) yace:

"Na shiga wajen Annabi (saww) alhali shi yana ciwon ciki. Sai nace masa: "Ya Rasulallahi ashe kana ciwon ciki haka mai tsanani?"

Sai yace "KWARAI KUWA. NI INA YIN CIWON CIKI KAMAR IRIN YADDA MUTUM BIYU DAGA CIKINKU SUKEYI (WATO ANA NINKA MASA CUWON KENAN)".

Sai nace "Hakane, wato kana da ninkin lada biyu kenan?"

Sai yace "EH WANNAN HAKANE. BABU WANI MUSULMIN DA WATA CUTARWA ZATA SAMESHI, GWARGWADON SOKEWAR QAYA, KO SAMA DA HAKA FACHE SAI ALLAH YA KANKARE MASA KURAKURENSA SABODA ITA, KUMA YA SHAFE MASA ZUNUBBANSA KAMAR YADDA BISHIYA TAKE ZUBARWA DA GANYENTA".

Imamul Bukhary ya ruwaito hadisin akan lamba ta 5,667.

Imamu Muslim ma ya ruwaito akan lambar hadisi na 2,571.

* Hadisi na biyu daga Sayyiduna Abu Sa'eed Alkhudry (Allah shi yarda dashi) ya shiga wajen Manzon Allah (saww) sai ya ganshi yana cikin Zazzabi har an sanya tsumma an daure masa kansa dashi.

Sai ya sanya hannunsa asaman tsumman da aka daure kan dashi.. (yaji yanayin zafin zazzabin) sai yace:

"Mamakin zafin zazzabin nan naka Ya Rasulallahi!"

Sai yace "MU (ANNABAWAN ALLAH) HAKA AKE TSANANTA MANA BALA'I, KUMA ANA NINNINKA MANA LADA".

- Aduba Sunanu Ibni Maajah, hadisi na 4,024.

- MUSTADRAK na Imamul Hakim, juzu'i na hudu shafi na 307.

* Hadisi na uku daga Sayyiduna Huzaifah ibnul Yamaan shi kuma ya karbo daga Goggonsa ('yar uwar mahaifinsa) Fatima (Allah shi yarda dasu) tace:

"Munje wajen Manzon Allah (saww) tare da wasu mata domin mu duboshi alhali yana cikin zazzabi, sai yasa aka dauko wata jakar ruwa (kamar gora, amma ta fata).

Yasa aka lankaya ajikin wata bishiya, shi kuma ya kwanta karkashin bishiyar. Ruwan yana digowa ajikinsa saboda tsananin zazzabin da yake ji.

Sai nace "Ya Rasulallahi, da ka roki Allah ya yaye maka"

Sai yace "MAFIYA SHAN TSANANIN BALA'I DAGA CIKIN MUTANE SUNE ANNABAWA. SANNAN WADANDA SUKE BIYE DASU, SANNAN WADANDA SUKE BIYE DASU, SANNAN WADANDA SUKE BIYE DASU".

– Aduba MAJMA'UZ ZAWA'IDI juzu'i na biyu shafi na 392.

6. HAKURINSA BISA MUTUWAR 'YA'YANSA DA JIKOKINSA (Amincin Allah ya tabbata gareshi dasu baki daya).

Annabi (saww) ya shiga wajen 'dansa Ibraheemul Mu'azzam alhali alokacin nan yana jin jiki.. (ransa ya kusan fita).

Sai aka ga idanunsa (saww) suna zub da hawaye.

Sai Abdurrahman bn 'Auf (ra) yace : "Kai din ma kana kuka Ya Rasulallahi?!"

Sai Manzon Allah (saww) yace masa "YA KAI IBNU AWFIN, WANNAN (HAWAYEN) AI RAHAMA CE".

Sannan ya ci gaba da cewa : "HAKIKA IDANUWA SUNA ZUBDA HAWAYE, KUMA ZUCIYA TANA BAKIN CIKI. AMMA BA ZAMU FADI KOMAI BA, SAI DAI ABINDA ZAI YARDAR DA UBANGIJINMU.

HAKIKA MU MUNA BAKIN CIKIN RABUWA DAKAI YA IBRAHEEMU!!".

- Sahihul Bukhary hadisi na 1,303.
– Sahihu Muslim hadisi na 2,315.

* Hadisi na biyu awannan babin daga Sayyiduna Usamah bn Zaid (Allah shi yarda dashi tare da mahaifinsa) yace:

'Yar Manzon Allah (saww) ta aiko masa (shi Annabin) cewa : "Yarona Mutuwarsa tazo. Ina so kazo nan wajenmu.

Sai ya aika mata da gaisuwa tare da cewa:

"DUK ABINDA ALLAH YA KARBA, DAMA NASA NE. KUMA ABINDA YA BAYAR MA DUK NASA NE. KUMA KOWANNE ABU YANA DA WANI AJALI SANANNE AWAJENSA. KIYI HAKURI, KUMA KI NEMI LADANSA AWAJEN ALLAH".

Sai ta sake aiko masa tana magiya cewa DON ALLAH yaje. Don haka ya tashi ya tafi tare Sa'adu bn Ubaadah, da Mu'az bn Jabal, da Ubayyu bn Ka'ab, da Zaidu bn Thabit, da sauran mazaje (Allah shi yarda dasu baki daya).

(bayan ya isa gidan) Sai aka dauko masa yaron. Ya dorashi bisa cinyoyinsa (saww). Alhali shi yaron yana numfashi sama-sama. Sai idanun Manzon Allah (saww) ya fara zub da hawaye...

Sai Sa'adu bn Ubaadah (ra) yace : "Wannan menene haka Ya Ma'aikin Allah?".

Sai Manzon Allah (saww) yace masa "WANNAN (HAWAYEN) RAHAMA CE WACCE ALLAH YAKE SANYAWA ACIKIN ZUKATAN BAYINSA".

Awata ruwayar kuma cewa yayi "WANNAN RAHAMA CE WACCE ALLAH YAKE SANYAWA ACIKIN ZUKATAN WANDA YASO DAGA CIKIN BAYINSA.

KUMA MASU TAUSAYI NE KADAI WADANDA ALLAH YAKE TAUSAYA MUSU DAGA CIKIN BAYINSA".

- Sahihul Bukhary hadisi na 1,284.
– Sahihu Muslim hadisi na 923.

7. HAKURINSA BISA CHUTARWAR DA WASU DAGA CIKIN SAHABBANSA SUKAYI MASA (SAWW) :

* Yayin da aka kammala yakin HUNAINU, (An samo ganima mai yawan gaske ) Sai Manzon Allah (saww) ya fifita wasu daga cikin manyan sarakuna da shuwagabannin larabawa wajen rabon ganimar yakin.

Misali : Ya bama Al-Aqra'u bn Haabisin RAKUMA 100, ya bama 'Uyainah bn Hisnin shima haka.

Sai wani mutum (ana ce masa Dhul Khuwaisara At-Tamimiy) yace:

"WALLAHI wannan rabon ba'ayi adalci cikinsa ba!! Kuma ba'a nufi Allah cikin rabon nan ba!!".

Abdullah bin Amru bn Al-aas (ra) yana wajen. Sai yace "Wallahi sai na gaya ma Manzon Allah (saww).

Don haka naje na gaya masa duk abinda mutumin nan ya fada. Nan take sai naga launin fuskar Manzon Allah (saww) ya chanza. Yayi ja-jawur.

Sai yace : "SHIN WANENE ZAI IYA YIN ADALCI IN DAI ALLAH DA MANZONSA BAI IYA ADALCI BA?!

ALLAH YA JI-QAN ANNABI MUSA. AN CUCESHI FIYE DA HAKA AMMA YAYI HAKURI".

Aduba:
- Sahihul Bukhary hadisi na 3,150.
- Sahihu Muslim hadisi na 1,062.

ABIN LURA:
************
'yan uwa na tabbata duk wanda ya karanta darasin nan namu da kyau, kuma yayi tunani sosai, sai ya zubda hawaye.. Koda bakayi kuka afili ba, zuciyarka zatayi kuka saboda tausayinka ko soyayyarka ga Manzon Allah (saww).

Sannan ku dubi yadda ya rika hakuri yana nan ladansa awajen Allah (SWT). Tun daga kan jinyarsa har zuwa rasuwar 'Dansa da jikansa.

Ku dubi dadadan kalmomin da yake furtawa alokacin da idan mune zamu zama mun dimauci mun gigice, muna tunane-tunane kala-kala.

Manzon Allah (saww) ba ya rabuwa da jinya. Musamman ma ciwon kai da ciwon ciki. Kuma baya rabuwa da jarrabobi kala kala da kuma damuwa. Amma duk wannan ba ya hanashi Qiyamullaili, zuwa wajen yaki, fita domin gudanar da ayyukan alkhairi da jagorancin jama'a.

Sannan dukkan 'ya'yansa guda shida sun rasu ne agabansa.. Wasu ma akan hannunsa.. In banda Sayyidah Fatima (ra)..

Duk da yana da makiya masu yawa adoron Qasa, kamar Yahudawa da kuma Munafukan da suke cikin al'ummarsa, amma Manzon Allah (saww) bai ce ASIRI bane, ko MAKARU, Ko kuma wani abun makiyansa sukayi masa.

Muma ya kamata mu zam masu daukan darasi daga rayuwar nan tasa mai tsarki. Domin kuwa cikakken mabiyin sunnah shine mai koyi da halayen Manzon Allah (saww).

Amma aiki komai yawansa idan babu ikhlasi ba zai zama karbabbe ba. Hakanan kamanninka ko suturarka batta da wani tasiri awajen Allah sai dai abinda zuciyarka ta Qulle na alkhairi ko sharri.

Anan zamu tsaya sai karatu na gaba idan Allah ya kaimu.

Sallu alan Nabiyyi wa aalihi

Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Abdul Mk at 06:13
In Fadakarwa
Title : HALAYEN MANZON ALLAH (SAWW)
Description : BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM Salati da aminci su tabbata bisa fiyayyen halittu, Annabinmu Shugabanmu Muhammadu tare da tsarkakan iyalan gida...
Rating : 5
Related Posts: Fadakarwa

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "HALAYEN MANZON ALLAH (SAWW) "

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ►  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ►  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ▼  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ▼  March (116)
      • President Jonathan Congratulates Buhari
      • Okorocha Catches Alleged PDP Loyalists With Ballot...
      • Okorocha rejects poll result, accuse soldiers of c...
      • Eight suspected Boko Haram gunmen killed in Gombe,...
      • Buhari Wins Kano With Landslide Victory-daily Inde...
      • Soldiers Already Opening fire in Bauchi
      • Gunmen storm INEC collation centre
      • Abuja Presidential Election Result: APC Defeats PDP
      • APC won in Osun State
      • INEC Postpones Election Indefinitely In 18 Polling...
      • Breaking: Buhari leads Jonathan in Ogun state
      • Photo: Inec Staff That Were Killed Today In Dukku ...
      • Policeman Kills Youth For Insisting On Sighting El...
      • Umana Calls For Cancellation Of Election In Akwa Ibom
      • Obanikoro, Mimiko, Adams Fail To Deliver Wards To ...
      • Buhari Seems To Be Leading. Results So Far
      • Soldiers Surround Ex Gombe State Governor, Senator...
      • APC condemns election violence in Gombe, Rivers
      • Presidential Villa: APC defeats PDP
      • Elections Must Be Cancelled In Rivers State, Says ...
      • APC members shot dead in Rivers state, many arrested
      • I will not accept polls cancellation – Buhari
      • Boko Haram Beheads 23 People And Sets Homes On Fir...
      • Boko Haram attacks polling units in Yobe and Borno...
      • BREAKING: INEC Announces That Elections Will
      • Boko Haram Attacks Gombe Polling Stations
      • Card Reader reject Jonathan’s PVC
      • Buhari accredited in Daura
      • Police plan arrest of El-Rufai, others, APC alleges
      • Dress Code Of Muslim Women and Men
      • Kaduna Governor, Yero, others honoured at Kannywoo...
      • HUKUNCIN WANDA YA KARBI CIN HANCI ABISA TILAS :
      • HUKUNCIN WANDA YAKE SHAN NONON MATARSA, DA KUMA MA...
      • Thugs open fire on Gov Amaechi’s convoy
      • AMMA Awards 2014 – List of Nominees
      • Buhari’s Last Message To Nigerians Before Election...
      • HUKUNCIN WANDA YA ZAGI ANNABI (SAWW
      • President Jonathan Plans Trouble In Six States, AP...
      • Shin kudi yana sa mutum rashin tausayi
      • Legal suit filed to disqualify Buhari postponed ti...
      • KU DUBA WANNAN GIRMA
      • MA'AIKATA MASU HULDA DA BANKI
      • MIJINTA YA RASU A KURKUKU
      • SHIN MAI HAILA ZATA IYA YIN ZIKIRI?
      • Boko haram Kidnapped 400 Women & Children In Borno...
      • PDP share Garri, Groundnut and sugar in Bauchi
      • Thugs loyal to PDP allegedly attack APC chieftain ...
      • KADAN DAGA CIKIN MUNANAN HALAYEN DASUKE CUTAR DA A...
      • LABARIN WANI MUTUM DA MUTUWA TA RISKESHI.
      • LADUBBAN DAREN FARKO DOMIN SABABBIN MA'AURATA
      • HARAMCIN KALLON BLUE FILM (BF)
      • DARAJOJIN MATA GUDA 16 DA SUKA ZARCE MAZA
      • HALAYEN MANZON ALLAH (SAWW)
      • NUNA LADABI GA MANZON ALLAH (SAWW)
      • FA'IDODIN ALBASA
      • MA'AIKATA MASU HULDA DA BANKI
      • Mourinho ya yi korafi kan fenariti
      • Magoya bayan AC Milan sun kaurace wa wasa
      • Man United ta doke Liverpool a Anfield
      • LABARIN WANI BARAWO
      • MAZA SUNA IYA YIN KITSO?
      • DAURIN KWALIN ACUCI MAZA *
      • HUKUNCIN YIN SADAQAH DOMIN MAMACI
      • MAGANIN RASHIN GAMSAR DA IYALI
      • Rescue Nigeria, save us from another civil war, Ig...
      • YIN SHURU BAYAN KARATUN FATIHA
      • HUKUNCIN AURE TSAKANIN MUTANEN DA SUKE KUSANTAR ZINA
      • NASIHA GA 'YAN MATAN ZAMANI
      • MATSALAR ZUBAR JINI BAYAN SADUWA
      • 5,000 PDP Members Join APC In 5 Months
      • IMANI
      • MANIYYI YANA FITO MASA BA TARE DA DALILI BA
      • MASU CIN AMANAR MATANSU
      • MUTANEN DA ALLAH YAKE KAUNA
      • Fati Muhammad released hot new Picture
      • ILOLIN SHAFE-SHAFEN BLICING GA MATA
      • Mob Lynch Suspected Suicide Bomber
      • Ali Nuhu Accept Adam A Zango Apologies
      • Adam A Zango Apologies to Rahma Sadau
      • Ali Nuhu celebrate Birthday with wife and kids
      • Finally Adam A Zango Apologies to Ali Nuhu
      • Farewell to Kannywood- Fati Ladan
      • Prof. Ango Abdullahi shot in Bauchi
      • APC House Of Assembly Candidate Killed
      • MAGANIN KOWACCE IRIN CUTA DA IZININ ALLAH
      • Graphic Photos: Another Young Man (allegedly) Kill...
      • I am a former military ruler, now a converted demo...
      • YAYA NASABAR ANNABI (S.A.W) TAKE ???
      • "QANANAN ZUNUBAI SUKE KAI MUTUM IZUWA GA TABEWA"
      • HUKUNCIN MAZA MASU SANYA ZOBE DA SARKA:
      • MATSALOLI YAYIN SADUWA
      • SHIN MUMINAI ZASU GA ALLAH? KO KUWA BA ZASU GANSHI...
      • MAGANIN HAWAN JINI DA ULCER (OLSA) DAGA ZAUREN FIQHU
      • HUKUNCIN RUNGUMAR JUNA KO YIN KISS (SUMBA) ABAKI
      • BA'A SHIGA TSAKANIN ALLAH DA BAWANSA
      • Nigerian Army Liberates Bauchi Forest From Insurgents
      • Unknown Gunmen Kidnapped APC Reps’ Candidate in Ba...
      • Kaduna denies Buhari access to rally venue – APC
      • CAF shifts Pillars, Tetouane match
      • Presidency Doubts Mu’azu’s Loyalty
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Suspect - Episode 1 ( Dj Giggs ft J Prince ft Nabs Kid) Hausa HipHop Ser...
  • Innalillahi wainna illaihin rajiun - Allah Yayi Wa Mawaki Aliyu Sharba R...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • (New Music) Reason By Peevibes
      PeeVibes - Reason Williams Akinsola Precious Popularly known as peevibes has returned again with this mind blowing song tagged “Reason”. T...
  • Barrister Aysha Ahmad - Kira Da Babban Muryan ( Akan Fyade Da Cin Zarafi...
  • Yadda Kotu Ta Daure Bobrisky Watanni Shida Ba Tare Da Zabin Biyan Tara Ba
    Kotu ta daure Bobrisky watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba Babbar kotu a jihar Lagos ta yanke hukunci ga Idris Okuneye da a...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger