Zazzabin Lassa ya yi sanadin mutuwar mutum 110 a Najeriya tun farkon wannan shekara, a daya daga cikin bullar cutar mafi muni tun shekara ta 2016, in ji Cibiyar takaita yaduwar cutuka ta kasar a wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata.
A cikin makon jiya ne Hukumar Lafiya Ta Duniya ta ce cutar ta karu, inda aka tabbatar da kamuwar mutum 317, wasu 72 kuma suka riga mu gidan gaskiya.
A cikin wani rahoto da ta fitar, cibiyar takaita yaduwar cutuka ta ce a farkon bullar cutar Lassa bana, an samu mace-mace har 110.
Haka kuma, an tabbatar da kamuwar mutum 78, takwas kuma na cikin kila-wa-kala, sai mutum 24 wadanda aka gwada su kuma aka tabbatar ba zazzabin ne ke damunsu ba.
Jimilla dai an ba da rahoton mutane su 1,121 sun kamu, a ciki an tabbatar 353 na dauke da cutar, takwas na cikin kila-wa-kala akwai kuma karin mutum 37 da ke jiran su san matsayin gwajin da aka yi musu.
Cibiyar ta ce an samu bullar zazzabin a jihohin Najeriya 18 a cikin 36, kuma jami'an lafiya 16 ne cutar ta shafa a cikin jiha shida.
Kafofin yada labarai a Najeriya sun ambato ministan lafiya na kasar Isaac Adewole na cewa, nan gaba kadan gwamnati za ta karbi alluran riga-kafi don shawo kan yaduwar zazzabin.
Lassa na da kamanceceniya da cutukan Ebola da Marburg inda yake haddasa zazzabi da haraswa da idan kuma ya yi tsanani sai maras lafiya ya fara zubar da jini.
Fiye da mutum 100 ne suka mutu a shekara ta 2016 lokacin da aka samu barkewar zazzabin a 14 daga cikin jihohin kasar 36 ciki har da Lagos da babban birnin tarayya Abuja.
Kwayar cutar na yaduwa ne ta hanyar tu'ammali da abinci da kuma kayayyakin amfanin gida da suka gurbata da fitsari da kashin bera ko kuma ta hanyar shafar duk wani ruwa-ruwa daga jikin mutum da ya kamu.
Source :bbc hausa
Title :
Zazzabin Lassa Ya Hallaka Mutane Sama Da 100 A Nijeriya
Description : Zazzabin Lassa ya yi sanadin mutuwar mutum 110 a Najeriya tun farkon wannan shekara, a daya daga cikin bullar cutar mafi muni tun shekara ta...
Rating :
5