Rahotannin da muke samu daga majiyoyin mu na nuni da cewa 'yan kungiyar nan ta 'yan uwa musulmi watau Islamic Movement of Nigeria, IMN a turance da aka fi sani da 'yan shi'a sun fita sun tattare wasu manyan hanyoyin garin Abuja suna zanga-zangar neman a sakar masu shugaba.
Mun samu haka zalika cewa zanga-zangar ta su da suke cigaba da yi a saman manyan titunan babbar birnin kasar ta jawo cunkoson ababen hawa sosai inda hakan ne ma ya sanya wasu masu motoci canza hanya.
Jaridar Naij dai ta samu cewa a cikin masu zanga-zangar hadda mata, kananan yara da kuma matasa hadi da shugabannin 'yan shi'ar daga sassa daban daban na fadin kasar.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa gwamnatin ta tarayyar Najeriya karkashin shugabancin Muhammadu Buhari ce ke cigaba da tsare shugaban 'yan shi'ar Sheikh Ibrahim Zakzaky biyo bayan wata arangaba da mabiyan sa suka yi da jami'an tsaro a shekarar 2015.
Source :naij hausa
Title :
Yan Shi'a Sun Cika Abuja Suna Neman Asake Musu Zakzaky
Description : Rahotannin da muke samu daga majiyoyin mu na nuni da cewa 'yan kungiyar nan ta 'yan uwa musulmi watau Islamic Movement of Nigeria, I...
Rating :
5