A wani sabon kididdigar bincike da hukumar kula da harkokin kudi ta kasa ta fitar watau FRC (Fiscal Responsibility Commission), ya bayyana cewa kantar bashi ta mafi akasarin jihohin Najeriya ta haura kaso 50 cikin 100 na kasafin kudaden shiga da suke samu.
Rahoton bincike da hukumar ta fitar a ranar Litinin din da ta gabata ya bayyana cewa, kantar bashi dake kan jihohin Legas, Osun da Cross Rivers ta haura kaso 480 cikin 100 na kasafin kudin shiga a jihohin.Hukumar FRC ta bayyana cewa, akwai jerin jihohi 18 da kantar bashin da ke kan su ta haura kaso 200 cikin 100 na kudaden shiga da suke samu.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, cikin tsari da sharuddan da hukumar FRC ta gindaya, bai kamata bashin kowace jiha ya haura kaso 50 cikin 100 na kudaden shigar ta.
Jaridar naij ta fahimci cewa, jerin jihohi mafi kantar bashi a Najeriya kamar yadda hukumar ta fitar sun hadar da; Legas, Osun, Cross River, Filato, Ekiti, Ogun, Kaduna da kuma Imo.
Jaridar ta kuma ruwaito cewa, a karshen makon da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin da ya sanya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fasa fita zuwa kasar Rwanda.
Source :naij hausa
Title :
Jihohi Mafi Karancin Albashi A Nijeriya - FRC
Description : A wani sabon kididdigar bincike da hukumar kula da harkokin kudi ta kasa ta fitar watau FRC (Fiscal Responsibility Commission), ya bayyana c...
Rating :
5