Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a jiya Talata ya bayyana cewa kungiyar ta'addancin Boko Haram kawo yanzu ba ta da wani katabus din da za'a rika maganar ta a kasar duk kuwa da sabbin hare-haren da ta kai a makarantar kwana ta 'yan mata a Dapchi da kuma kauyen Rann a jihar Borno a yan kwanakin nan.
Sai dai da ya ke karin haske, shugaban kasar ya bayyana cewa irin wadannan hare-haren na ta'addancin babu gwamnatin da ke iya hana yin su dun kuwa da irin tsaron da ke gare ta a kasa.
Jaridar NAIJ ta samu cewa shugaba Muhammadu Buhari yayi wannan ikirarin ne a ta bakin mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo wanda ya wakilce sa a taron masana da masu ruwa da tsaki na bitar kan tsaro karo na takwas da a ka gudanar a garin Abuja.
A wani labarin kuma, Gwamnatin jihar Filato dake a yankin Arewa ta tsakiya ta sanar da bayar da hutu ga dukkan ma'aikatan ta a jihar domin samun damar tarbar shugaba Muhammadu Buhari da zai ziyarci jihar a ranar Alhamis 8 ga watan Maris.
Shugaban ma'aikatan jihar Mistam Izam Azi shine ya sanar da wannan matakin da gwamnatin ta dauka a jiya Talata jim kadan bayan gama wani taron tattaunawa na gaggawa da majalisar zartarwas kasar ta gudanar.
Source :naij hausa
Title :
Ba Abinda Boko Haram Zasu Iya Yiwa Kasarmu-Buhari
Description : Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a jiya Talata ya bayyana cewa kungiyar ta'addancin Boko Haram kawo yanzu ba ta da wani katabus ...
Rating :
5