Wani ‘Dan takarar Gwamnan Jihar Oyo a karkashin Jam’iyyar PDP Injiniya Seyi Makinde yayi kaca-kaca da kasafin kudin da Gwamnan Jihar Abiola Ajimobi ya gabatar a gaban Majalisa.
Dan takarar PDP Seyin Makinde ya soki kasafin kudin Jihar Oyo na 2018 wanda yace zai kara jefa matasa da sauran jama'an Jihar ne cikin wani halin ha’ula’i. Makinde yayi wannan jawabi ne ta bakin wani daga cikin ‘yan kwamitin yakin neman zaben sa.
Gwamna Abiola Ajimobi ya ware abin da bai wuce kashi 3% ba kan harkar noma in da ya warewa ofishin sa akalla Naira Biliyan 15 daga kasafin na bana.
Kudin dai da aka warewa ofishin Gwamna ya zarce abin da aka warewa sha’anin lafiya da kuma ilmin zamani.‘Dan siyasar dai yana gani bai dace a warewa harkar noma da kiwo Naira Biliyan 270 ba kacal ganin yadda ake da manoma da dama a Jihar ga kuma rikicin makiyaya da ake ta fama da shi. Yace jama’a su shirya don wahala ba ta kare masu ba a Gwamnatin APC.
Source :naij hausa
Title :
Anyi Kaca Kaca Da Surukin Ganduje
Description : Wani ‘Dan takarar Gwamnan Jihar Oyo a karkashin Jam’iyyar PDP Injiniya Seyi Makinde yayi kaca-kaca da kasafin kudin da Gwamnan Jihar Abiola ...
Rating :
5