‘Yar takrar Shugabar kasa a karkashin Jam’iyyar KOWA a zaben 2015 watau Remi Sonaiya ta bayyana cewa da ita za a kara fitowa zaben 2019 inda ta ke sa ran kada Shugaba Buhari.
Farfesa Remi Sonaiya ta bayyana cewa za ta jarraba sa’ar ta a zabe mai zuwa. Sonaiya ta bayyana wannan ne a Ranar mata ta Duniya da ya fado a wancan makon inda aka yi wata lacca game da mata a harkar siyasa.
Sai dai Farfesar na iya samun cikas a wajen takarar ganin cewa akwai wasu mutane 4 da ke neman kujerar Shugaban kasar a Jam’iyyar su ta KOWA amma tace ta na sa rai duk za ta buge su a zaben fitar da gwani da za ayi.
Sonaiya mai shekaru 63 ba yau ta fara siyasa ba don kuwa da ita aka buga a 2015 tace babu kasar da za ta cigaba a Duniya idan mata ba su shigo harkar siyasa ba don haka tace a daina barin maza kadai da wannan aiki.
Source :naij hausa
Title :
Ansami Wata Mata Da Zata Nemi Kujerar Buhari
Description : ‘Yar takrar Shugabar kasa a karkashin Jam’iyyar KOWA a zaben 2015 watau Remi Sonaiya ta bayyana cewa da ita za a kara fitowa zaben 2019 inda...
Rating :
5