1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Gida Nijeriya » Kunsan Sayyidina Umar Ya Taba Aiko Sako Daular Borno?

Kunsan Sayyidina Umar Ya Taba Aiko Sako Daular Borno?

By 1Arewa Tv
Add Comment
Saturday, 24 February 2018

Daular Borno tsohuwar Daula ce a Afirka da aka kafa tun kafin karni na 10 wacce ta hada da yankunan da yanzu ke cikin Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru da Sudan har Libya.

Daular Kanem ta El Kanemi ta samo asali ne daga daular Saifuwa.

Masana tarihi sun ce mutanen Saifuwa daga Yemen ne suka fara kafa daular musulunci a Borno, tsawon shekaru 1000 da suka gabata.

Muhammad al-Amin ElKanemi ya kafa Daular Kanem ne a karni karni na 18, bayan kawar da daular Saifuwa wadanda sarakunanta suka yi mulki shekaru da dama.

BBC Hausa ta duba tarihin Daular Borno ta hanyar tattaunawa da Masana tarihi Alhaji Zanna Hassan Boguma daraktan da ke kula da al'amuran masarautu a Borno, da Farfesa Adam Muhammad Ajiri na sashen nazarin addinin Islama a Jami'ar Maiduguri, wadanda kuma suka yi kokarin amsa wasu tambayoyi da masu saurare suka aiko.

Asalin kalmar Borno - Tambaya ce da muka samu daga Umar Abubakar da Sani Garba da Ishaq Abubakar Kazaure.

Rubuce-rubucen masana tarihi sun nuna cewa Kalmar Borno ta samo asali ne daga kalmomin Larabci, "Bahar Nur" wato ma'ana kogin haske.

Kuma saboda kasancewar Borno gidan Al Qur'ani gidan Musulunci ne dalilin ke nan da ya sa sarakunan farko suke kiranta "Bahar Nur", ma'ana kogin haske na musulunci.

Amsar tambayoyinku kan masarautar Sarkin Musulmin Nigeria
Mata 100: Kun san macen da ta yi zarra tsakanin mazan Nigeria?
Masanin tarihi Alhaji Zanna Hassan Boguma ya ce Ibn khaldun ya ambaci "Bahar Nur" a rubuce-rubucensa na tarihin musulunci a Afirka.

Daular Borno ta kafu sama da shekaru 1000
Tushen Borno - Wannan Tambaya ce da muka samu daga Umar Musa Dambam daga Bauchi a Najeriya da Buhari Yusuf da Abdulmumin Adamu da Ahmad Adamu Tamadina da Shu'aibu Idris Kofar fada Balangu a jihar Jigawa da Garba Saleh.

Tarihi ya nuna cewa Kanuri da suka kafa Borno daga Yemen suka fito, wato tsatson wani sarki da aka yi a Yemen Said Ibn Dhi Yazan da ake kira Malik al-Himyari tun kafin zamanin Annabi SAW, wanda ya kafa dauloli a India da Fasha.

Tarihi ya nuna mutanen Ibn Dhi Yazan suna cikin wadanda suka amince su ba sahabban Annabi SAW mafaka bayan hijirarsa daga Makkah zuwa Madinah.

Yemen ne asalin Kanurin da suka kafa mulki a Borno daga daular Saifuwa' a cewar Zanna Hassan Boguma.

Shehu Umar Kura Ibn Shehu Muhammad Al-Amin Elkanemi sarki na biyu a Daular Elkanemi
Borno a zamanin Sahabbai - Tambaya ce da muka samu daga Jamilu Bagaraje da Magaji Rabiu da Abubakar Umar Usman da Nasir Abubakar Jaja.

Daular Borno ta yi zamani da Sahabbai, kuma masanin tarihi Alhaji Zanna Hassan Boguma ya ce daular ta kafu ne tun kafin zuwan Annabi SAW.

A cewarsa tarihi ya nuna sarakunan Borno sun aika da wasika suna neman malamai da za su koyar da addini zuwa ga Amr al-As gwamnan Misra, wanda shi kuma ya tura Uqba Ibn Nafi.

"Sarakunan Borno sun karbi malamai daga wajen Ibn Nafi a zamanin Sayyadina Umar RA".

Amma Zanna Hassan Boguma ya ce wasu litattafan tarihi sun nuna cewa a zamanin Sayyadina Usman RA ne.

Sai dai Farfesa Adam Muhammad Ajiri ya ce Gwamnan daular Maghribi a arewacin Afirka Uqba Ibn Nafi yakinsa har ya kawo Borno a shekarar 666, kuma zamanin Khulafa'ur Rashidun ya fara ne daga 632 har zuwa 660.

Ya ce ba za a iya cewa sun yi zamani da sahabbai ba, amma ana ganin watakila a lokacin akwai daular musulunci a Borno, ko da yake an fi tabbatarwa a zamanin Umayyad daga 661 zuwa 750.

"A lokacin akwai binciken da ya nuna daga shekarar 661 zuwa 670 akwai malamai daga daular Umayyad da suka shigo yankin Maghrib har suka iso Borno," in ji Farfesa Ajiri.

Taswirar yankunan Tsohuwar Daular Borno
Saifuwa a Borno da kafuwar ElKanemi - Tambaya ce da muka samu daga Abdurahman Salisu Zaria da Abubakar Goni Kolo da Hassan Yarima K/Huguma da Baba Ali Kabir

Saifawa su ne asalin sarautar Borno, kuma Zanna Boguma ya ce dalilin da ya sa ake kiransu Saifuwa saboda sun fito ne daga Said Ibn Dhi Yazan.

Tarihi ya nuna Saifuwa sun yi sarauta sama da shekara 1000 inda suka yi sarakuna kimanin 113, tun kafin karni na bakwai.

Farfesa Ajiri ya ce bayan Saifuwa sun ci Zaghawa da yaki ne suka kafa daular musulunci a Borno, kuma sun kafa daula ne daga wajajen karni na shida.

Sarakunan farko a daular Saifuwa sun hada da Mai Dugu a shekarar 785 da Mai Fune a shekarar 835 da Mai Aritso a 893, da Mai Katuri a 942 da Mai Ayoma a 961 da Mai Bulu a 1019 da Mai Arki a 1035 da Mai Shu a 1077.

Fadar Shehu Umar Sanda Kyarimi da Majalisarsa a Dikwa
"Tun zamanin Sarkin Saifuwa Mai Hume Djilme a wajajen 1080 aka fara daula ta musulunci har zuwa sauran sarakunan da aka yi", a cewar Zanna Boguma.

Ya ce, a zamanin daular musulunci ta Saifuwa an yi Sarakuna da suka hada da Mai Dunama Humemi da ya yi mulki daga shekarar 1098 zuwa 1150 da Mai Biri Ibn Dunoma da ya yi mulki daga shekarar 1150 zuwa 1176 da Mai Bikoru Ibn Biri Dunomami da ya yi zamani daga 1176 zuwa 1193.

Mai Ahmad ne Sarkin Saifuwa na karshe, kafin zamanin daular ElKanemi.

Farfesa Ajiri ya ce karshen mulkin Saifuwa ya zo karshe ne a lokacin da Fulani suka kawo hari suka ci garin Gazargamu da yaki tsohon babban birnin Daular Borno.

Goni Mukhtar ne ya yaki Gazargamu, inda ya kori Mai na Saifuwa tare da taimakon Shehu El Kanemi.

ElKanemi ne ya taimaka aka kori Fulani daga Borno.

Farfesa Ajiri ya ce bayan an kashe Goni Muktar a Damaturu ne kuma Mai Ahmad na Saifuwa ya rasu, daga nan El Kanemi ya zama Sarki a wajajen 1810 zuwa 1814.

ElKanemi ya ci gaba da mulki a daular Saifuwa duk da cewa shi ba daga zuriyar Saifuwa ba ne.

Farfesa ya ce ElKanemi ya kafa daular ElKanemi 1814 a birnin Kukawa, wato shekaru sama da 200 a yanzu.

1809- Kasuwar Kukawa a tsohuwar Borno
"Idan an hada shekaru kusan 800 na Daular Saifuwa da shekaru sama da 200 zai kasance shekarun daular Borno sama da 1000".

Shehu Mohammed el Amin Elkanemi ya fara kafa daula ne a Ngurno tare da ba Mai Dunoma na Tara Lefami matsayin sarki a Kanem daga daular Saifuwa daga 1814 zuwa 1817.

Mai Ibrahim na hudu Ibn Dunoma Lefami ne ya gaji Dunoma a matsayin Sarkin Saifuwa a Kanem.

Bayan El Kanemi ya karbi mulki ne sarautar Borno ta sauya daga Saifuwa zuwa Shehu ElKanemi.

Masanin tarihi Zanna Boguma ya ce lakabin sarautar Borno ya sauya daga "Mai" ma'ana "Sarki" zuwa "Shehu" bayan kafuwar ElKanemi, sabanin sarakunan farko.

"Bayan ElKanemi ya samu mulkin Borno, daga nan ne ya ce shi ba zai amince a kira shi da "Mai" ba saboda shi malami ne".

"Don haka ya ce zai kira kansa a matsayin Shehu, wato Malami, inda ya hada mulki da malamanta", a cewar Zanna Boguma.

Ya kuma ce: "Wannan ne dalilin da ya sa duk wadanda suka zama sarakuna a Borno ake kiransu Shehu daga gidan El Kanemi."

Shehu Umar Kura ne ya gaji mahaifinsa Shehu Muhammad El Amin ElKanemi a matsayin Sarkin Borno daga 1835 zuwa 1853.

Shehu Abubakar Garbai Ibn Shehu Ibrahim Elkanemi Kakan Shehun Borno na yanzu Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi
Sarakunan El Kanemi - Tambaya ce da muka samu daga Naziri Aliyu Abubakar da Hussaini Aminu da Mohammed Mala Ngarannam da Abdullahi Bala da Shafi'u Idris Umar da muhammad Ali.

Kamar yadda bayanai suka gabata an yi shekaru da dama da kafuwar Daular Borno kafin zuwan ElKanemi. Sarakunan Borno zamanin daular Elkanemi kafin Rabeh ya ci Borno da yaki sun hada da:

Shehu Mohammed Al-Amin Elkanemi 1814- 1846
Shehu Umar Kura Umar (1835 - 1853) Dan Shehu Mohammed Elkanemi
Shehu Abdul Rahman Ibn Muhammad Elkanemi - 1853 - 1854
Shehu Umar Kura Ibn Muhammad Elkanemi- 1854 - 1880
Shehu Bukar Zarami Kura Ibn Umar - 1880 - 1884
Shehu Ibrahim Ibn Umar - 1884 - 1885
Shehu Hashimi Ibn Umar - 1885 - 1893
Shehu Kyari Ibn Bukar Zarami - 1893-1894
Shehu Sanda Limananbe Wuduroma Ibn Bukar Zarami - 1894
Shehu Umar Kura na cikin Sarakunan Borno da suka fi dadewa a mulki.

Sai Shehu Sanda Kyari wanda ya shafe shekara kusan 40 yana mulki.

Shehu Mustapha Umar El Kanemi shi ma sarki ne da ya dade inda ya yi shekara 34 yana mulki.

Shehu Garbai kakan Shehu na yanzu ma ya dade inda ya yi shekara 24 yana mulki.

Daular Borno ta yi zama a karkashin turawan Birtaniya da Jamus
Wanene Rabeh? Tambaya ce da muka samu daga Sani Ali da Nura Bala da ahmad Adam Bagas Minna da Adam Musa Ladan Fulata.

Rabeh Zubair Ibn Fadlallah mutum ne da ya taso daga Sudan, wanda ke sana'ar fataucin bayi, inda yake saye ya kuma sayar da bayi.

Masanin tarihi Zanna Boguma ya ce fataucin bayi ne dalilin da ya sa Rabeh ya yaki Borno .

A 1893 ne Rabeh ya kawo wa Borno hari.

"Rabeh Zubair Ibn Fadlallah ne ya rushe tsohuwar daular Borno bayan ya kaddamar da yaki kuma ya samu galabar kwace iko ya mayar da Dikwa a matsayin babban birnin daularsa".

Rabeh ya kashe sarakunan Borno guda biyu, Shehu Kyarimi da Shehu Sanda Wudoroma.

A 1900 sojojin Faransa na mulkin mallaka suka kashe Rabeh bayan ya yi mulki a shekaru bakwai da watanni bakwai da kwanaki bakwai a Borno.

Bayan sun kashe Rabeh ne suka aza Shehu Sanda Kura daga zuriyar Elkanemi a matsayin Shehun Borno a Dikwa a 1900.

A 1901 suka tube shi suka kuma daura dan uwansa Umar Abubakar Garbai, kakan Shehun Borno na yanzu.

Sarakunan Borno bayan kashe Rabeh
Lokacin Turawan mulkin Mallaka, tsohuwar Masarautar Borno ta rabu gida biyu inda Dikwa ta koma karkashin ikon turawan mulkin mallaka na Jamus, bisa wata yarjejeniya tsakanin turawan Faransa da Birtaniya da kuma Jamus na mulkin mallaka.

Daga baya Abubakar Garbai ya koma Sarkin Borno a yankin da turawan Birtaniya ke iko.

A shekarar 1902 ya fara yin hijira zuwa Monguno kafin daga baya ya koma Maiduguri.

Lokacin da Dikwa ta koma karkashin ikon Birtaniya, an samu Shehu guda biyu, Shehun Borno a Maiduguri da kuma Shehun Dikwa.

Shehu Umar Ibn Abubakar Garbai Elkanemi mahaifin Shehun Borno na yanzu.
Tsarin sarautar Borno. Wannan tambaya ce da muka samu daga Aminudden Ali Dan Hassan.

An kafa masarautar Borno da al'adunta ne a kan tsari na musulunci.

Masanin tarihi Zanna Boguma ya ce a zamanin farko na El Kanemi an bi tsari ne irin na khalifancin Manzo SAW.

Ya ce El Kanemi yana da mashawarta guda hudu wadanda kuma suka kasance kamar majalisar Koli.

"Mutanen sun hada da Malam Muhammed Terab da Malam Ahmad Gonimi da Ibrahim Wadaima da Aji Sudani wadanda suka taimaka masa wajen shinfida tsari na shari'a da adalci a Borno".

Amma ya ce bisa tsari na al'ada Borno tana da tsarin sarautu 3,333, wadanda suka kunshi na 'ya'yan gidan sarki da fadawa da bayi da na Malamai.

Sannan akwai sarautu na sana'o'i kamar na wanzanci da kira da rini.

Amma sarautun da suke da girma da kima sun kai 313.

Source :bbc hausa

Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by 1Arewa Tv at 13:43
In Gida Nijeriya
Kunsan Sayyidina Umar Ya Taba Aiko Sako Daular Borno? Title : Kunsan Sayyidina Umar Ya Taba Aiko Sako Daular Borno?
Description : Daular Borno tsohuwar Daula ce a Afirka da aka kafa tun kafin karni na 10 wacce ta hada da yankunan da yanzu ke cikin Najeriya da Nijar da C...
Rating : 5
Related Posts: Gida Nijeriya

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Kunsan Sayyidina Umar Ya Taba Aiko Sako Daular Borno? "

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ▼  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ▼  February (127)
      • BBC Takori Ma aikatan Ta Sabida Kallon Batsa
      • Zakanya Ta Hallaka Wata Mata A South Africa
      • Anrufe Coci Sama Da 700 A Rwanda
      • Sirrin Namun Dajin Dake Nijeriya
      • Na aikata Kura Kurai Da Dama A Rayuwata-Adam A Zango
      • Dalilin Dayasa Nayi Ma Umma Shehu Tambaya Akan Add...
      • Jarumar Fina Finan Hausa Na Busa Sigari
      • APC Sun Kunyata Yan Nijeriya - Dino Melaye
      • Dalilin Dayasa Ban Sa Hanu Akan Takardar peace Cor...
      • CBN Na Kokarin Cika Kasuwanni Da Kananan Kudi
      • NNPC Ta Amince A Gina Sabuwar Matata A Arewa
      • Abubuwan Da Baku Saniba Game Da Dakta Mamman Shata
      • Antura Jiragen Yaki 100 Neman Yan Dapchi
      • Wani Jami'in Kwastam Ya Harbe Wani A Jigawa
      • Sabon film din hafsat Idris da maryam gidado
      • Sojoji Sun Kashe Mayakan Boko Haram 35
      • Saudiyya Ta Kori Manyan Hafsoshin Sojan Ta
      • Gawar Sridevi Kapoor Yashiga Hanun Yan Uwanta
      • Yazamo Dole Wa Buhari Ya Tafi Dapchi - PDP
      • Yadda Akeyi Wa Yara Bilicin Tun Suna Ciki
      • Yan Sanda Da Kyakkyawan Mace - hausa comedy
      • Akwai Babban Kalubale Akan Kungiyar Kwadago-Dogara
      • Jaruman Da suka Kafa Tarihi A Kannywood
      • Abunda ya sa addinin musulunci ya fi na Kiristanc...
      • Abubuwan Da Baku Sani Ba Game Da Sace Yan Matan Da...
      • Gwanda Islamiyya Da Makarantar Dapchi
      • An Kwantar Tarzoman Data Taso A Kaduna
      • Sojoji Basu Kula Da Dapchi Inda Yakamata Ba-Yan Sanda
      • Bam Ya Hallaka Jama'a Da Dama A Leicester
      • Hatsaniyar Addini Ta Barke A Kaduna
      • Zakunan Syria Da Iraki Sun Gudu
      • Kun San Meyayi Ajalin Sridevi Kapoor?
      • Yanzu Mata Zasu Iya Shiga Aikin Soja-Gwamnatin Sau...
      • Sabon Wakan Umar m sharif da nafeesa Abdullahi
      • Abinda Da Yasa Bansake Aure ba-Sameera Ahmad
      • Damu za'ayi Zabe Mai Zuwa-Makiyaya
      • An gano inda rabin 'yan matan makarantar Dapchi suke
      • Hakkine Ke Bin Gwamnatin APC-Inji PDP
      • Kwankwaso ya tofa albarkacin bakin sa kan mulkin B...
      • Kalli Sabon Wakan Abdul D one
      • Xi Jinping 'zai zama shugaban mutu-ka-raba' a China
      • Arsenal Tasa Kashi A Hanun Man city
      • Kalli Trailer Film Din Daya Dauki Hankali a 2018
      • Man united Tabawa Chelsea kashi
      • Kalli Sabon wakan Da Akayi Wa Ali Nuhu
      • Sabbin Wakokin Maryam yahaya guda 10 masu fitowa
      • Kyautar Aure Ta Hallaka Ango Da Kakarsa A India
      • Illar yin Tsarki Da Sabulu Ga Mata
      • Sridevi, Jarumar Fina Finan Indiya Ta Rasu
      • Yawan Wasannin Da Conte Yaci Mourinho
      • Yadda Akeyi Nasamu Jikoki da Maniyyin Dana Daya Mutu
      • Shin Wa Zai Lashe Kofin Caraboa Tsakanin Mancity d...
      • An fidda sunayen dalibai 105 da akayi awun Gaba Da...
      • Mene ne yake hana matan karkara zuwa awon ciki?
      • Shin Za ku iya sayen wasika a kan N18m?
      • Ankai Hari Kusa Da Fadar Shugaban Kasan Somalia
      • Sabon Wakan Umar m sharif Da Bangis
      • Yar Buhari Nayi wa 'yan Nigeria romon baka - Dr Ju...
      • Kunsan Sayyidina Umar Ya Taba Aiko Sako Daular Borno?
      • Bala'in Daya Shafi Kasane Sace Yan Matan Dapchi-Bu...
      • Shin Kunsan Yaren Da Mutum Uku Ne Keji A Duniya?
      • Ina jiran El-Rufai a Kotu – Shehu Sani
      • Fitattun Wakokin Hausa Masu Fitowa na 2018
      • Yara Na Kallon Yadda Akeyi Wa Iyayensu Fyade a Sud...
      • Laifin Buhari ne Sace Yan Matan Dapchi-PDP
      • Wani Biri Ya Cinye Naira Miliyan 70
      • Idan Mun Samu Miji Zamu Ajiye Film Muyi Aure-Hassa...
      • Kalli Teaser Sabon Wakan Umar M Sharif Tareda sabu...
      • Saudiyya zata hanun jarin $64bn a bangaren nishada...
      • Yakamata Akoyi Darasi Daga Chibok-Dapchi
      • Nan Bada Dadewa Ba Buhari Zai Sanar Da Yan Nijeriy...
      • Wasu Manyan Nijeriya Naso Tambuwal Ya Kalubalanci ...
      • Wani Kurtun Soja Ya Harbi Mai Gidansa Da Bindiga
      • Matan Ghana Sun Fara Kwallon Rugby
      • Gwamnatin Yobe ta yi amai ta lashe Abinta
      • Wani Malami Ya Kashe Dalibinsa Da Bulala A Zamfara
      • Video: Kalli Bidio Zuwan Shugaba Buhari Adamawa
      • Kalli Yanda Ake Shirya Wakar Kannywood
      • Ansake Kai Shugaban Ansaru Kotu
      • Gwamnan Jihar Yobe Yanemi Afuwa Agun Mutanen Dapchi
      • Video; Kalli Yanda Adam A Zango Ke Rera Waka Hamis...
      • Kalli Rawan isheh baba Akan Stage
      • Video: Rabuwa Ba Mutuwa Ba - Sabuwar Waka Hausa
      • Rike Bindiga Agun Malamai Zai Magance Matsalar Har...
      • Wata Ma'aikaciyan Gidan Rediyo Ta Haihu A Bakin Aiki
      • Ya Akayi Sevilla Ta Shake Wa Manchester wuya?
      • Ba Sauyi Haryanzu Akan Rashawa A Nijeriya-Kungiya...
      • Anceto Yanmatan Da Aka Sace A Yobe
      • Mata Adon Gari-short comedy drama
      • Sabuwar rayuwa e10
      • Haduwar Ganduje Da Sule Lamido
      • Hussainin danko performance
      • Anrasa Yan Mata 51 A Harin Da Boko Haram Suka Kai ...
      • Yusuf Na Nan Da Ransa-Fadar Shugaban Kasa
      • Ankama Wani Da Zinaren Dayakai Miliyan 360
      • Shin Manchester Zata Iya Doke Sevilla?
      • Jirgin Dana Yafadi A Dajin Fatakwal
      • Dagaske Ne Dan Shugaban Kasa Buhari Ya Rasu?
      • Wani Matashi Ya Auri Kanwarsa Bayan Ya Mata Ciki
      • Satar Abinci Yakai Yan Boko Haram Makaranta A Yobe
    • ►  January (7)
  • ►  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ►  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ►  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Suspect - Episode 1 ( Dj Giggs ft J Prince ft Nabs Kid) Hausa HipHop Ser...
  • Innalillahi wainna illaihin rajiun - Allah Yayi Wa Mawaki Aliyu Sharba R...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • (New Music) Reason By Peevibes
      PeeVibes - Reason Williams Akinsola Precious Popularly known as peevibes has returned again with this mind blowing song tagged “Reason”. T...
  • Barrister Aysha Ahmad - Kira Da Babban Muryan ( Akan Fyade Da Cin Zarafi...
  • Yadda Kotu Ta Daure Bobrisky Watanni Shida Ba Tare Da Zabin Biyan Tara Ba
    Kotu ta daure Bobrisky watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba Babbar kotu a jihar Lagos ta yanke hukunci ga Idris Okuneye da a...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger