1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Daga Jama'a » Yadda Waya Ta Ruguza Tarbiyan 'Yata

Yadda Waya Ta Ruguza Tarbiyan 'Yata

By Unknown
Add Comment
Friday, 1 September 2017

Da zarar an ambaci wayar salula abin da ke fara zuwa zukatan mutane shi ne, wata na'urar zamani mai saukaka isar da sako.

Ko dai ta hanyar sakon kar ta kwana, ko kiran gaggawa a fadi wani abu da a baya sai an dauki tsawon kwanaki kafin sakon ya isa inda ake bukata.

Wasu kuma za su iya kallon wayar salula a matsayin jakadiyar sada zumunci, ko ma 'yar aiken da isarta da wuri ka iya ceto rayuwar wani ko wasu mutane daga fadawa wani ibtila'i. Misali gobara, hadarin mota, rashin lafiya, kwantar da tarzoma, isar da sakon farin ciki ko akasin haka.

A takaice wayar salula na taka muhimmiyar rawa a rayuwarmu ta yau da kullum.

To amma kun taba zama kun baje kolin irin rawar da ta kan taka wajen haddasa fitina ko gurbata tarbiyya, da haddasa rashin jituwa tsakanin miji da mata ko abokan juna ko kawaye har ma da gurbata tarbiyyar 'ya'yanmu?

Badriyya Tijjani Kalarawi ta yi ma na nazari kan wannan batu

Lamarin ya samo asali ne da yammacin ranar 13 ga watan Agustan 2017, da misalin karfe 8 na dare, a lokacin ina zaune bayan gama cin abincin dare.

Ga al'adata na kan kalli labarai na tashoshinmu na gida da kuma waje, kana sai na kalli wasannin kwaikwayo na kasar Indiya da ake fassarawa da harshen Turanci.

Wayata na ji tana kira, da na duba sai na ga ashe wata abokiyar wasata ce da ba zan ambaci sunanta ba, bayan gaisawa ta bukaci don Allah na zo gidanta akwai abin da take son mu tattauna akai.

Ban yi kasa a gwiwa ba na tafi, abin da ya daga min hankali yadda na gan su cirko-cirko kamar an yi mutuwa, tambayar farko da na yi mata ba ta amsa min ba ta dai miko min wayar salular 'yarta samfurinIphone 7+.

Manhajar WhatsApp ce a bude, inda na ga wani suna 'Stranger' wato bako, na ci gaba da duba sakonnin da yake turowa 'yarta mai shekara 16 wadda a bana ta kammala karatun sakandare.

Sakonnin ba masu dadi ba ne, a takaice sakwannin badala ne hadi da hotunan tsiraicin maza da mata wanda mai wannan lambar yake aikowa matashiyar yarinya.

Bayanin da mahaifiyarta ta yi min shi ne kusan shekara uku da mahaifin yarinyar ya siya mata wayar salula, ta nuna kin amincewa da hakan amma ya yi biris da ita.

Kuma duk shekara sai ya sauya mata waya.

Wannan mutumin da aka sakaya sunansa da Stranger, sun hadu ne a irin kungiyar nan ta abokai da ake haduwa don sada zumunta da raha wato WhatsApp Group.

Ya dade yana mata dadin baki tun ba ta tura masa hotunan tsiraicinta har ta fara.

A takaice dai sai da muka lalubo lambarsa muka dangana da zuwa wajen hukuma, aka kira shi don a yi musu tsakani.

Abin takaicin garjejen kato ne da ya girmeta da a kalla shekara 10, dole mahaifiyarta ta karbe wayar salular da ta zama jakadiyar batawa 'yarta tarbiyya.

Ko kun san?

Wannan ke nan da aka san abin da ya faru, akwai iyaye da dama da ba su san abin da 'ya'yansu ke yi da wayoyin salula ba, kawayen da a baya kan zo gida don sada zumunta zamani ya kawo lokacin da ba sai sun zo gida ba.

Ta wayar salula ake tattauna ko wacce irin magana, don haka ba ko wacce uwa ce ta san adadin kawayen 'ya'yanta ko 'yarta ba.

Iyaye ba su damu da bibiyar halin da 'ya'yansu ke ciki ba, ko da kuwa a cikin gida ne bare kuma idan suka fita.

Iyaye kan dauka 'ya'ya sun yi bacci da dare, alhalin a wasu lokutan suna can yin wayar dare da ba a cajin kudi wato Free Call ko dai da kawaye ko kuma da samari.

Kuma a yawancin lokutan wayar da ake yi da tsakar dare, ta sha bamban da wadda ake yi da rana ido na ganin ido, daidaikun samari da 'yan mata ne ke tattaunawa kan wani muhimmin batu a irin wannan lokacin.

Yawancin iyaye mata da na tattauna da su kan batun rawar da wayar salula ke takawa a rayuwar 'ya'yansu musamman mata, labarin ba mai dadi ba ne, kamar dai yadda wata uwa da ta bukaci na sakaya sunanta ta shaida min.

''Zan iya fada miki daya daga cikin abin da nake yin da-na-sanin yi a rayuwata, shi ne bai wa Zainab (ba sunanta na asali ba) wayar salula a lokacin da ta fara makarantar sakandare.

"Abin da Babanta ya shaida min ya kuma ba ni kwarin gwiwa akai shi ne yana da muhimmanci a san duk lokacin da ta fita ko dai makaranta ko gidan biki da sauransu.

"Ban dai saki jiki ba gaskiya, amma daga baya na bar damuwar, wallahi in takaice miki batu wayar salula ita ta koyawa 'yata abubuwa guda uku;"

Ta lissafa su kamar haka:

Na farko Zainab ta daina karatu da dare sai dai waya da chatting da kawaye a cewarta.

Ta ci gaba da cewa yarinyar ta daina ayyukan gida da 'ya'ya mata ke yi wa iyayensu, sam ba ta son zama cikin 'yan uwanta don yin hira ko taya su aikin gida da ake ba su daga makaranta.

"Abu mafi ciwo shi ne, ta dalilin wayar salula Zainab ta rasa 'yancinta na diya mace, don kuwa ta hadu da wani shaidanin saurayi da ya yaudare ta da abubuwan kyale-kyale da take boyewa ba mu san da su ba da dadin baki."

"Ya gayyace ta liyafar na abokinsa, ta min karya da walimar murnar zagayowar ranar haihuwar kawarta za a yi ta shirya da kawar suka je a can aka sanya mata abin gusar da hankali a lemo.

"Daga nan sai mai aikuwar ta auku, wannan shi ne abin da ba zan taba mantawa da shi da wayar salula ta haddasa min ba.

"Na kuma san har na mutu ba zan manta da wannan abin takaici ba,'' in ji wannan baiwar Allah.

Wata uwar ta daban ta shaida min cewa, ''Ta wayar salula ita ma 'yarta ta hadu da kawaye bata gari da suka rinjaye ta, suka koya mata yawo.

"Ta kai ma ba ta zuwa makarantar Islamiyya, idan ta fita daga gida sai ta hadu da kawayen su tafi yawo.

"A can ta koyo shaye-shayen nan na zamani da ake ta fama da su, ba mu farga da rashin zuwanta Islamiyya ba sai da malaminsu ya aiko cewa ba ta cika zuwa makaranta ba, don haka yana son ganin mahaifinta.

"A lokacin da ya je ne muka san halin da ake ciki, amma sai ta yi mirsisi wai tana zuwa hadda ce da ba ta bayarwa shi ne dalilin da ya sa malamin ba ya ganinta.

"To a hankali kuma sai na lura tana yawan bacci, alhalin a baya ba ta cika baccin rana ba, sannan ba ta son kannenta su shigar mata daki.

"Sannan tana yawan shan lemon kwalba, kuma ba ta taba bari kannen su sha.

"Abin ya ishe ni na dage da sanya ido a kanta, ba a je ko ina ba na kama kwalaben Benilin da Emzoline a durowar gefen gadon dakinta.

"A halin da ake ciki baban ya hanata zuwa makaranta daga boko har islamiyyar, kuma ya sha alwashin aure zai mata kowa ya huta daman dan kanina yana mutuwar sonta, amma ta ki maida hankali.

"Kin ji yadda wayar salula ta janyo min salalar tsiya.''

Ire-iren wadannan labarai suna da tarin yawa, sai dai kuma ba duka aka zama daya ba.

Akwai yara 'yan mata da samari da yawa da suke amfani da wayar salula kuma babu abin da ya faru sai alheri, yana da kyau dai iyaye su mayar da hankali da sanya ido kan tarbiyyar 'ya'yansu.

Ina mafita?

Na tattauna da Muhammad Salihu Abubakar, wanda aka fi sani da Baban Sadik, wanda masani ne kan harkokin intanet, inda ya ce, yana da matukar muhimmanci iyaye musamman mata, su dauki matakin janyo 'ya'yansu a jiki, ba su kulawa da cikakken 'yancin shaida musu duk abin da ke damunsu.

"Bin kwakkwafin son sanin kawayen 'ya'yanmu ba lallai sai mata ba har da mazan, sanin daga gidan da wadannan yara suka fito.

"Kokarin nusar da 'ya'yanmu illar da ke cikin badala, da zantukan batsa da kallon hotunan tsiraici, ko kallon bidiyon da ake yin badala.

"Nusar da su muhimmancin amfani da lokaci wajen cimma wani buri na rayuwa, da zai amfane su da al'uma baki daya, misali neman ilimi.

"Lokaci zuwa lokaci karbi wayar salular daga hannunsu, ajiye ta a kunne ba ma tare da binciken komai a ciki ba.

"Da yin kokarin amsa duk kiran da ya shigo wayar don sanin wadanda ke yawan kira ko ake kiran.

Source: BBC Hausa

Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Unknown at 23:18
In Daga Jama'a
Yadda Waya Ta Ruguza Tarbiyan 'Yata Title : Yadda Waya Ta Ruguza Tarbiyan 'Yata
Description : Da zarar an ambaci wayar salula abin da ke fara zuwa zukatan mutane shi ne, wata na'urar zamani mai saukaka isar da sako. Ko dai ta han...
Rating : 5
Related Posts: Daga Jama'a

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Yadda Waya Ta Ruguza Tarbiyan 'Yata"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ▼  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ▼  September (167)
      • Za'a Cire Shingayen Binciken 'Yan Sanda
      • Ba'a Hada Aure Da Sana'ar Film-Maryam Yahya
      • Yakin Koriya Da Amurka Zai Iya Kawo Karshen Duniya
      • Ma'aikaciyar British Airways Taci Zarafin 'Yan Nig...
      • Buhari Nason Musuluntar Da Nigeria-CAN
      • Zamu Kammala Kwaso Alhazai Nan Da Kwana Goma-Hukum...
      • Zaa Rantsar Da Sabon Shugaban Kasar Angola
      • Arsenal Ta Dago Sama Bayan Tasha West Brom 2-0
      • Kishin Kasana Yasa Na Rike Minista Har Sau Biyu-Ok...
      • Da Amincewar Iyayena Nashiga Film-Maryam Yahya
      • Ana Binciken Yan Sandan Dasuka Lakadawa Dalibai Duka
      • 'Yan Bindiga-Dadi Sunkai Hari Fadar Sarkin Oyo
      • Buhari Yadawo Gida Nigeria
      • Majalisan Adaamawa Ta Tsige Shuwagabanninta Guda Hudu
      • Alkali Ya Tura Tsagerun Biafara 60 Kurkuku
      • Za'a Fara Shari'ar 'Yan Boko Haram 1,600
      • 'Yar Nigeria Tashiga Jerin Mawaka Masu Tashe A Lo...
      • Angano Wani Kamfanin Kera Makamai A Abuja
      • Nigeria Tarasa Mutum 423 A Watan Yuli-Hukumar Kiya...
      • Magoya Bayan Jam'iyar APC Dubu Ashirin Sun Koma PD...
      • Ronaldo Ya Gagara Zura Kwallo Ko Daya A La Liga
      • Kunsan Nawane Albashin Neymar A PSG?
      • Ozil Na shirin Komawa Man United
      • Buhari Zai Dawo Gida Nigeria Daga London
      • Korea Da Amurka Zasu Bawa Hammata Iska
      • 2019: Jarumi Lawal Ahmad Zai Nemi Kujerar Dan Maja...
      • Al'ummar Garin Bama Na Jihar Borno Na Gangamin Kom...
      • Lukaku Ya Bukaci Magoya Baya Su Daina Kyamar Sa
      • 'Yan Nigeria Miliyan 75 Basu Iya Karatu Da Rubutu ...
      • Kai-Kawon Masana Kan Tsarin Tunanin Al'umma
      • Aikin Hako Mai Yayi Nisa A Jihar Sokoto-NNPC
      • Man United Taci Ribar Fam Miliyan 581
      • Trump Nada Tabin Hankali-Kim Jong Un
      • Sunan Muhammad Ya Sami Matsayi A Burtaniya
      • Tir:Kotu Ta Daure Wani Magidanci Da Laifin Yin Lal...
      • Boko Haram Sunkashe Limami Da Mutane 16 A Borno
      • Ranakun Kiranyen Dino Melaye
      • Masana Sun Kirkiro Hanun Dayafi Na Mutum Karfi Sau 15
      • Wata Mata Takashe Kanta A Jigawa Don Mijinta Yamat...
      • Antura Jirgin Yaki Yankin Igbo
      • Menene Sirrin Mallakar Miji?
      • Mummunan Girgizan Kasa Ya Hallaka Mutane Sama Da 1...
      • Bamucewa IPOB 'Yan Ta'adda Ba-Sojin Nigeria
      • Buhari Ya Bukaci A Sulhunta Da Shugaban Korea Ta A...
      • Gwamnonin Arewacin Nigeria Na Rangadi A Jahohin Kudu
      • Kwale Kwale Ya Nitse Da Mutum 56 A Kogi
      • 'Yan Biafara Nason Ganin Bayan Gwamnatin Buhari-La...
      • Dybala Yaci Kwallo Uku A Wasansa Ta Dari
      • An kirkiro Manhajar Komputar Hausa Daba Irinta A D...
      • Guguwa Mai Tsanani Ta Hallaka Mutane A Romania
      • Luwadi Da Madigo:Fira Ministar Romania Ta Kafa Tarihi
      • Dalilin Dayasa Naki Amincewa Nafito A 'Yar Madigo-...
      • Mu Ba 'Yan Ta'adda Bane-'Yan Biafara
      • Chelsea Da Arsenal Zasu Kece Raini
      • Zanga Zanga Ta Barke Kan Shugaban Kasan Da Baa Zab...
      • Kabilar Igbo Mazauna Kano Da Adamawa Sun La'ananci...
      • Buhari Yazauna Da Nnamdi Kanu A Teburin Sulhu-Obas...
      • Gwamnonin Igbo Sun Haramta IPOB
      • Matan Datafi Tsufa Ta Fadi Sirrin Tsawon Rai
      • Yadda Kalamanka Ke Cutar Da Dabi'unka A boye
      • Wata Halittan Da Ba'a Taba Ganiba Ta Bullo A Amurka
      • Uwar Gida Tajefa 'Ya'yan Kishiya Biyu A Rijiya
      • 'Yan Siyasan Kudu Maso Gabas Neke Tunzura Mutane
      • Ankafa Dokar Hana Walwala A Garin Jos
      • An Amince Matan Tunisia Su Auri Mazan Daba Musulmi Ba
      • Sojoji Sunkai Sumame Gidan Nnamdi Kanu
      • Nataka Rawar Gani A Arsenal-Wenger
      • Wasu Abubuwa Sun Fashe A Tashan Jirgin London
      • Allah Yayi Rasuwa Wa Dan Autan Mawakan Hip Hop Na ...
      • Arsenal Da Cologne Zasu Fuskanci Hukunci
      • Sha'awar Jima'in Mata Na Raguwa In Aka Kwatanta Da...
      • Wani Mai Magani Yace A Tsigo Masa Gashin Clinton
      • Gobara Takashe Dalibai Da Dama A Makarantar Islami...
      • Yadda 'Yan Arewa Suka Tafka Asara A Rikicin IPOB
      • Nigeria Zata Fara Sayarda Takardun Sukuk
      • Giwayen Afrika Sun Bullo Da Dabarar Kariya Daga Ma...
      • Angargadi Mata Game Da Kunzugu
      • Ansa Dokan Hana Fitar Dare a Abia
      • Sojin Nigeriya Sunyi Wa Boko Haram Ruwan Wuta
      • Kasan Dasuke Cin Kyankyaso A Afrika
      • Liverpool Zata Daukaka Kara Kan Mane
      • Gwamnatin APC Munafukace-Jonathan
      • Gwamnatocin Sokoto Da Zamfara Sun Kammala Gyaran T...
      • Wani Mutum Yayi Lalata Da Yarinya Yar Shekara 4 A ...
      • Atiku Ya Kalubalanci Masu Cewa Yayi Sata Basuda Hujja
      • Matasan Nigeria Na Cike Da Fushi-Obasanjo
      • Yadda Kwakwalwan Bera Take Aiki
      • Ankama Bindigogi Sama Da dubu Daya A Lagos
      • Gwamnatin Tarayya Zata Samar Da Buhun Taki Miliyan...
      • Yar Sanda Tayi Alkalancin Wasan Maza
      • Kwalara Ta Sauka A Jihar Borno
      • Littafin Magana Jarice Tafito Da Martabar Bahaushe...
      • Sojojin Nigeria Sun Karyata Farmaki Kan 'Yan Biafara
      • Dalilin Dayasa Mukayi Harbi A Sama a Garin Umuahia...
      • Mutane 19 Sun Rasu A Hadarin Mota A Kano
      • 'Yan Sanda Sunkama Barayin Shanu 22 a Jihar Neja
      • Ronaldo Zaiyi Wasa Wa Madrid Ranan Laraba
      • Yadda Ake Musguna Wa Musulmi A Myanmar
      • Rikice Ya Barke Tsakanin Ali Nuhu Da Rahma Sadau
      • Ankama Babban Kwamandan IS a Kano
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ►  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ►  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Suspect - Episode 1 ( Dj Giggs ft J Prince ft Nabs Kid) Hausa HipHop Ser...
  • Innalillahi wainna illaihin rajiun - Allah Yayi Wa Mawaki Aliyu Sharba R...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • (New Music) Reason By Peevibes
      PeeVibes - Reason Williams Akinsola Precious Popularly known as peevibes has returned again with this mind blowing song tagged “Reason”. T...
  • Barrister Aysha Ahmad - Kira Da Babban Muryan ( Akan Fyade Da Cin Zarafi...
  • Yadda Kotu Ta Daure Bobrisky Watanni Shida Ba Tare Da Zabin Biyan Tara Ba
    Kotu ta daure Bobrisky watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba Babbar kotu a jihar Lagos ta yanke hukunci ga Idris Okuneye da a...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger