1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Rayuwar Duniya » Abinda Ke Kawar Da Shaawan Jima'i Ga Mata

Abinda Ke Kawar Da Shaawan Jima'i Ga Mata

By Unknown
Add Comment
Sunday, 27 August 2017

Barbara Gattuso lokacin tana da shekara 30 da wani abu ta fara ganin ta fara juya wa mijinta baya game da harkar jima'i. "Na daina yi masa magana kan lamarin, domin ban damu da jima'i ba," a cewarta.

Tsawon shekaru Gattuso, wadda yanzu ta kai shekara 66 ta yi wayon boye wa mijinta don ka da ya zo mata ta ki tara wa da shi kai tsaye; sai ta rika kwanciyar barci da wuri, sannan ta farka kafin ya tashi.

"Bayan wani lokaci hakan al'amarin ya kasance, ko me ke faruwa a nan? Ina son mijina, mun yi auren jin dadi, tare da samun kyawawan 'ya'ya; ko me ke faruwa?"

Matsalar ta sha'awa ce. Duk da cewa mafi yawan mutanen da suka dade da aure za su tabbatar da cewa karsashin sha'awa kan dusashe tsawon lokaci, Gattuso ba ta ma da sha'awar tarawar jima'i ko kadan. Ba ma ga mijinta kadai ba; ba ta ma sha'awar kowa.

Masana tantance tasirin kwakwalwa kan dabi'ar jima'a sun yi ikirarin cewa irin wannan sauyin bijirowar sha'awar jima'i al'amari ne da aka saba gani, musamman ga mata in sun fara tsufa.

Wasu kuwa na ganin raguwar karsashin sha'awa ciwo ne; sakamakon rashin daidaiton sinadarai a kwakwalwa. Ta yiwu yanzu a samu maganin cutar.

A ranakun 3 da 4 ga Yuni, Hukumar kula da ingancin abinci da Magunguna ta Amurka (FDA) za ta tattauna da kwararru su bayar da shawar ko amincewa kwayar Flibanserin a matsayin maganin zaburar da son jima'i na mata "female Viagra" don masu larura su yi amfani da shi ko a jefar da shi a kwandon shara.

Matsalar ta raba kan masana gida biyu, inda wadanda suka amince da masu adawa suka jajirce.

Matsalar kewayar sakonni

Ko mene ne ke kawar da sha'awar jima'i, kuma yaya maganin Flibanserin zai taimaka? Ba mata kadai ne ke kyarar jima'i da sun fara tsufa ba; shaharar gagai samfurin 'Viagra' wani tabbaci ne kan hakan.

A cewar mai barkwanci George Buirns: "Jima'in mai shekara 90 kamar jikqa igiya a ruwa ne." Sai dai yanayin matsalar ya bambanta a tsakanin jinsi (maza ko mata).

Akwai dalilai uku da ke haifar wa mata rashin son jima'i: sha'awa, sha'awa da sha'awa

"Akwai maganar da ake fada a likitanci cewa matsaloli uku ne ke kashe sha'awar jima'i karfin mazakuta, karfin mazakuta da karfin mazakuta," a cewar Stephen Stahl, masanin tasirin kwakwalwa kan dabi'u da ke Jami'ar California a San Diego. "Sannan akwai dalilai uku da ke haifar wa mata rashin son jima'i: sha'awa, sha'awa da sha'awa"

Hakikanin abin da ke kashe sha'awa al'amari ne da ya boyu ga masana kimiyya, ko da yake sun fahimci cewa yana da alaka da zagayen sinadarai.

Daya daga mahangar ita ake kira mutuwar gaba ko mazakuta (HSDD) - a mata kuwa ana yi wa lamarin lakabi da dusashewar sha'awar jima'i sakamakon kin kullewar goshin kwakwalwa da ke yin tarin ayyuka a kullum, kamar tunawa da tura sakon ranar haihuwa ko warware matsalolin aiki.

Sakamakon zagayen sinadarai, wadanda ke tarairayar zaburarwa da annashuwa ya kasance a tauye.

Tun da gaigai din Viagra ya samu nasarar warkar da matsalar jima'in maza (ba tare da ambaton garabasar kamfanin da suka sarrafa shi ba), wasu sun yunkura wajen samar da irin wannan kwayar maganin ga mata, amma wadda za ta shawo kan matsalar kwakwalwa fiye da kafar al'aura.

Flibanserin na daya daga jerin wadanda ke kan gaba.

Da farko an samar da maganin da ke shawo kan dugunzumar damuwa, wanda aka gano tasirinsa kadan ne a kan yanayin mutane. Sai dai matan da aka yi gwajin kwayar magnain a kansu sun bayar da rahoton illar da ba a zata ba; zakuwar son jima'i.

Alamun aikin Flibanserin na nuni da daidaiton sinadaran da ke kewaya kwakwalwa, wato dp[amine da noradrenaline da serotonin.

"Muna jin cewa ko ana daidaita musu zama ko a maye gurbin abin da bai daidaitu ba, ta yadda za su ci gaba da kewayawa," in ji Stahl.

"Tabbas akwai yiwuwar yana taimaka wa mata wajen kauce wa cibiyar zagayen goshin kwaklwalwa da ke tauye sha'awar jima'i."

Bijiro da sha'awa

Duk da cewa kwayar maganin an ajiyeta a gefe a matsayinta na mai kawar da dugunzumar damuwa, saboda takaituwar tasirinta, an sake bunkasata don bijiro da sha'awa ga mata da ke fama da mutuwar kafar al'aura (HSDD).

Sai dai an ci gaba da bibiyar gwaje-gwajen, inda mata suka ruwaito cewa ana samun karuwar "gamsuwar jima'i," sun dai kasa tabbatar muhimmin tasirinta wajen bijiro da sha'awar jima'i.

Sakamakon hakan Hukumar FDA ta ki amincewa da maganin a shekarar 2010.

Ku san a iya cewa Ba'amurkiya kan yi jima'i a kalla sau uku a wata; idan mai fama da larura ba ta yi jima'i sau uku ba, shin ko wannan na nufin kwayar maganin ta gaza?

Nazarin da aka kara yi ya tabbbatar da cewa tana kara zaburar da sha'awar jima'i daga bisani, ko da yake tasirinta ya yi bazata.

"Matsalar dai ita ce, yaya za a kimanta ci gaban da aka samu? Tambayar da Susan Scanlan ta yi, wato Shugabar kun giyar fafutikar kare lafiyar jima'in mata ta Even The Score campaign, wadda ta ciri tuta wajen samar da maganin mutuwar al'aura (HSDD).

(Abin da ya kamata a lura shi ne ta yiwu kamfanoin sarrafa magunguna ya biya Scanlan wani kudi ta ja zugar fafutikarta). Ta yi nuni da cewa tarairayar sauyi ta yi karanci. Kusan a iya cewa Ba-Amurkiya kan yi jima'i akalla sau uku a wata; idan mai fama da larura ba ta yi jima'i sau uku ba, shin ko wannan na nufin kwayar maganin ta gaza?.

A gaskiya matan da ke amfani da kwayar maganin Flibanserin sun bayar da rahoton mu'amalar jima'i sau biyu da rabi cikin kwanaki 28, in an kwatanta da daya da rabi (1.5) na matan da ke fama da mutuwar al'aura (HSDD), wadanda ba sa shan maganin.

Tabbas, wasu daga cikin masu matsalar da aka yi gwajin a kansu sun samu tabbacin gyaruwar lamuran. Gattuso ta shiga jerin wadanda aka yi wa gwajin a shekarar 2011.

Da farko an ba ta makwafin maganin sarrafa tunani (placebo), abin da ta ce bai yi aiki ba, duk da cewa ta yi kokarin zaburar da sha'awar jima'inta.

Sai dai bayan gwaji an ba ta damar yin amfani da maganin gaske. "Cikin makonni kadan na yi matukar samun sauyi," in ji ta.

"Na kan tashi cikin dare in rungume maigidana. Kasancewar kusancin kud-da-kud da sha'awar makalkale wa juna ya zama 100 bisa 100."

Sai dai daya daga cikin abin damuwar shi illolin da ke tattare da nasarorin sun hada da juwa da layi da tashin zuciya. Ko da yake Scanlan ta yi nuni da cewa matsalolin ba su taka-kara sun karya ba, in an kwatanta da na 'Viagra' da sauran magungunan shawo kan mutuwar gaba.

"Bari mu bibiyi wasu daga cikin illolin da ke tattare da magunguna 26, wadanda aka amince maza su yi amfani da su don maganin matsalar mutuwar mazakuta," in ji Scanlan. "Mun ji akwai bugun zuciya da makanta da mutuwar fuju'a da kuma wanda ya fi jan hankalina shi ne, raunin mazakuta."

Wasu kuwa na fargabar in an amince da Flibanserin za a ingiza mata su rika neman maganin matsalar da kamata ya yi a ce sun warwareta ta hanyar tuntubar mai bayar da shawarar zamantakewar ma'aurata maimakon likita, ko shawo kan matsalolin da suka danganci jibga wa kai dimbin aiki ko dugunzumar damuwar.

"Idan aka yi batun sha'awa, dangantakar ma'aurata na da muhimmanci, yanayi muhimmi ne, daukacin halin da aka samu kai, wanda ya hada da fasalin bayyane da na boye duk suna da muhimmanci," a cewar Cynthia graham, babbar malama a fannin kula da lafiyar kwakwalwa ta Jami'ar Southampton da ke Birtaniya.

Akwai wadanda ke jin cewa watsi da Flibanserin zai haifar da rudanin neman magani mafi nagarta.

Ko da a hakan ma ta yarda cewa magani zai yi matukar taimakawa a nau'ukan yanayin. "Ina jin cewa wasu mata na fama da matsalar sha'awa, karshe dai sai an samo kwayar maganin matsalar matan.

Sai dai akwai bukatar a tabbatar kwayar maganin na da amfani a likitance, kuma akwai bukatar sanin illolin da ke tattare da ita," in ji graham.

Wasu na fargabar cewa watsi da Flibanserin zai haifar da rudanin neman makwafin maganin mafi nagarta.

Source: BBC Hausa

Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Unknown at 10:42
In Rayuwar Duniya
Abinda Ke Kawar Da Shaawan Jima'i Ga Mata Title : Abinda Ke Kawar Da Shaawan Jima'i Ga Mata
Description : Barbara Gattuso lokacin tana da shekara 30 da wani abu ta fara ganin ta fara juya wa mijinta baya game da harkar jima'i. "Na daina ...
Rating : 5
Related Posts: Rayuwar Duniya

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Abinda Ke Kawar Da Shaawan Jima'i Ga Mata"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ▼  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ▼  August (338)
      • Gwamnonin Kudu Maso Gabas Na Ganawa Da Nnamdi Kanu
      • Babban Mai Garkuwa Da Mutane Ya Amsa Laifinsa A Kotu
      • Hanyoyi 5 Da Mahajjaci Zai Kare Lapiyansa Yayin Yi...
      • Yadda Ciwon Kai Kejawo Mantuwa Da Rudin Kwakwalwa
      • Rabon Buhari Da Taron Ministoci
      • Aikin Shekara Nawa Zakayi Kafin Kasami Albashin Da...
      • Dattawan United Zasu Gwabza Dana Barcelona
      • EFCC Na Shirin Taso Keyar Diezani
      • Yan Siyasa Ne Kawai Ke Jin Dadin Nigeria
      • Buhari Ya Tafi Bikin Sallah Daura
      • Tir:Mutumin Da Yayi Wa 'Yarsa Sau Uku A Kano
      • Chelsea Na Daf Da Daukan Dan Wasan Gefe Na Arsenal
      • Koriya Ta Harba Makami Mai Linzami Ta Saman Japan
      • An Gayyaci Yan Madrid Sha Bakwai Tawagan Kasashensu
      • Dalilan Dayasa Dangote zai Sayi Arsenal
      • Gobara Ya Lashe Dakunan Daliban Jamiar Filato
      • Yawancin Alhazan Nigeria Manoma Ne-Abdullahi Mukhtar
      • Buhari Ne Ya Jefa Nigeria A Yunwa Da Talauci
      • Shin Buhari Ya Tambaya Aiki Nawa Aka Samawa Samari?
      • Kotu Ta Mallakawa Gwamnati N7.6bn Na Diezani
      • Kashi 70 Zuwa 80 Bisa 100 Na Mutan Dake Dauke Da C...
      • Nakwashe Duk Iyalai Na A Sansanin Yan Gudun Hijra ...
      • Ranar Juma'a Da Litinin Hutun Sallah Ne-Gwamnatin ...
      • Falalar Layya Da Sharudansu
      • Naji Dadin Farfadowar Tattalin Arzikin Nigeria-Buhari
      • Paris Saint-Germain ta amince ta biya kungiyar Mon...
      • Barcelona Ta Kammala Sayan Dembele
      • Isa Ali Ya Lashe Muhimmiyar Kyauta A Landan
      • Ban Maida Obasanjo Saniyar Ware ba-Buhari
      • Dalilin Dayasa Na Boye Wasu Abubuwan Dasuka Shafen...
      • Ku Fada Wa Buhari Inanan A Aba Kuma Ba wanda Ya Is...
      • Bacin Raine Ya Tilasta Mini Komawa Saliyo
      • Ambaliyar Ruwa Yayi Barna A Niger
      • Kenya Ta Haramta Amfani Da Leda
      • Dangantakar Dangote Da Dantata
      • Hamma Misau Yasa Zare Da Yan Sandan Nigeria
      • Amfani 7 Da Asuwaki Keyi Ga Lafiyar Mutum
      • Yadda Jami'an Alhazan Jihar Nasarawa Suka Yanke Ma...
      • Liverpool Ta Sha Arsenal Ci 4 Da Babu
      • Ansako Ma'aikatan Hako Ma'adanai Da Aka kama A Jih...
      • Abinda Ke Kawar Da Shaawan Jima'i Ga Mata
      • Venezuela Ta Daura Damarar Kare Iyakokinta
      • Liverpool Tabawa Barca Wa'adi Kan Coutinho
      • Barcelona Tabaiwa Dembele Rigan Neymar
      • Everton Zata Ziyarci Chelsea
      • Tamowa Ta Fara Kama Yan Gudun Hijira-ICRC
      • Meyasa Mutuwar Aure Ta Yawaita A Kasar Hausa?
      • Mutanen Gaza Sunyi Kallo A Cinema Bayan Shekara 30
      • Alamu Ya Nuna Cewa Raguna Zasuyi Kwantai
      • IPOB Bata Amince Dan Janye Koran Yan Kabilar Igbo ...
      • Gwamnatin Tarayya Zata Gina Gidaje 2,736 A Kowani ...
      • Duk Film Din Da Nafisa Tayi Kuka A Ciki Haka Kawai...
      • Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Kotu Data Soke Belin Nna...
      • Sarkin Dayafi Kowani Sarki Dukiya A Nigeria
      • Guguwa Mai Hatsari Ta Afkawa Wa Texas
      • Wani Dan Boko Haram Yayi Nadama
      • Angano Wani Zoben Zinaren Da ya Bata Ajikin Wani K...
      • Korea Ta Arewa Tayi Gwajin Makamai Masu Linzami
      • Nafi Buhari Bawa Yan Nigeria Yanci-Jonathan
      • Buhari Ya Amince Da Gina Sabbin Layin Dogo
      • Yan PDP Sunje Duba Shugaba Buhari
      • Amfani 5 Da Kwan Salwa Keyi A Jikin Mutum
      • Munanan Kan Bakanmu,Beraye Ne Sukayi Barna A Ofish...
      • Jawabin Buhari Bai Isa Ya Yaudare Muba-Uchenna Madu
      • Mun Fasa Korar Yan Kabilar Igbo Daga Arewa
      • Dalilin Dayasa Na Fito A Barauniya-Hafsat Idris
      • Film Ne Yahana Ni Zama Farfesa-Bosho
      • Nigeria Zata Taso Keyar Masu Laifin Dasuka Gudu UAE
      • Jirgin Sojojin Saman Nigeria Yayi Hatsari A Kaduna
      • Ronaldo Ya Lashe Kyautan Gwarzon Dan Kwallon Turai
      • Dangote Zaikashe Naira Biliyan 200 Wurin Gina Jami...
      • Gwamnatin Jihar Legas Ta yi Odan Tireloli 70 Na Bu...
      • Wasu Maniyata Biyu Yan Jihar Sokoto Sun Tsinci Mak...
      • Ban Isa Aureba,Kwata Kwata Shekaruna 23 Ne A Duniy...
      • Yawan Haihuwa Ne Silar Talauci A Niger
      • Kasar Saudiyya na bukatar Dabbobi 120,000 Duk Sati...
      • Hafsat Idris Ta Tashi Hankalin Kannywood
      • Yadda Yayana 14 Suka Mutu
      • An Gurfanar Da Wani Malamin Islamiyya Kan Zargin Y...
      • Dalilin Dayasa Nakafa Sojojin Sirri Na Biafara-Nna...
      • JAMB Ta Takaita Makinta Zuwa 120
      • An Haifi Wani Jariri Da Juna Biyu
      • Beraye Da Kwari Sun Hana Buhari Shiga Ofishinsa
      • Wata Kotu Ta Raba Auren Wata Dake Auren Maza Biyu ...
      • Ranar Daya Ga Watan Satumba Zaayi sallah Inji Sark...
      • Shuwagabanin Katolika Sun Nemi Gwamnatin Tarayya D...
      • PDP Ta Soki Buhari Kan Babachir
      • Shugaba Buhari Ya Soke Taron Ministoci Na Wannan S...
      • Wani Magidanci Ya Yi Ido Hudu Da Matarsa Tare Da W...
      • Messi Bayaso Coutinho Ya Dawo Barcelona
      • Gwamnatin Saudiyya Ta Ziyarci Yan Nigeria Da Akaci...
      • Tsananin Zafi Ya Hana Mahajjata Fita A Saudiyya
      • Wani Alkali Ya Harharbi Wani Dan Bindiga
      • Mahajjata Tara Sun Isa Madina A Keke
      • Mutanen Dasukaji Kunya Bayan Dawowan Buhari
      • Gobara Ya Tashi A Wani Otal A Saudiyya
      • Neymar ya Caccaki Darektocin Barcelona
      • Buhari Ya Turawa Majalisa Da Wasika
      • Dawowan Buhari Yasa Yan Nigeria Samun Sa'ida
      • Nafisat Abdullahi Tayi Kaca Kaca Da Rahma Sadau
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ►  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ►  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Suspect - Episode 1 ( Dj Giggs ft J Prince ft Nabs Kid) Hausa HipHop Ser...
  • Innalillahi wainna illaihin rajiun - Allah Yayi Wa Mawaki Aliyu Sharba R...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • (New Music) Reason By Peevibes
      PeeVibes - Reason Williams Akinsola Precious Popularly known as peevibes has returned again with this mind blowing song tagged “Reason”. T...
  • Barrister Aysha Ahmad - Kira Da Babban Muryan ( Akan Fyade Da Cin Zarafi...
  • Yadda Kotu Ta Daure Bobrisky Watanni Shida Ba Tare Da Zabin Biyan Tara Ba
    Kotu ta daure Bobrisky watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba Babbar kotu a jihar Lagos ta yanke hukunci ga Idris Okuneye da a...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger