1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Hausa Novels » NI DA PRINCE ( FINAL )

NI DA PRINCE ( FINAL )

By Abdul Mk
1 Comment
Wednesday, 12 July 2017
By *AYUSHER MOHD*📚
     © *NWA*
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄☄

*NA AYUSHER MOHD*

No: 5⃣9⃣

Salman ya kalli Ishaq yace " ahhh so matar kaninka kake so shine kaje d'akinsa?" Ishaq yace " nifa ba haka nake nufi ba."
  Fulani tace " wai Salman meye hakan? Kasa yaro a gaba kanata bugar cikinsa, to bazan yarda ba, nasani sarai Ishaq d'ina bazaije gun wata matar ka ba mai kama da aljanna."
     Salman yad'anyi dariya yace "Umma I feel hurt, wato ni ba naki bane bako?" Fulani takalli sarki tai kasa dakai tace "nifa ba haka nake nufi ba."

    "Ohhhh nagane me kike nufi, amma umma bakya ganin bai kamata kice nasa yaro agaba ba? Yanzu kamar Ishaq a kira shi yaro? Yafa girmeni?"
Salman ya fad'a yana mata wani kallo.

   Fulani kam ta tsani Salman yasata agaba duk ya rikitata haka, bare yau agaban Sarki tama rasa me zata ce.

    Ishaq yace" niba yaro bane, nasan kuma duk abunda nakeyi, yama za'ayi kid'inga kirana yaro agaban Salman?"
     Sarki yai gyaran murya hakan yasa kowa ya nutsu,cikin b'acin rai ya kalli Ishaq yace "kenan dagaske ka shiga d'akin Salman kaje neman matarsa?"
    Ishaq yace " Abba ba haka bane.."
"To ya ya ne? Ko inkira matar tawa ne? Ko kuma kanaso in kara maka dukan dana ma d'azu ne?" Jiyai Salman ya katseshi da wad'an nan kalmomin.
   Ishaq ya kalli Salman a rikice yakuma kalli Fulani datake makama Salman harara ta gefe, yai kasa dakai tare da runtse ido.
   Salman yad'an tab'e baki ya kalli Sarki, sannan ya kalli Ishaq  yace "  nikam yaya waye ya kaimu asibiti ranan da mukai karamin accidents d'inan?"
Ishaq cikin zumud'i ya d'auka wani abu ne yace " nine mana, nina kaiku."
Fulani zatai magana Sarki yace " kar inkuskura inkara jin bakinki anan tunda badake suke ba."

   Salman yai murmushi yace " Ayya yaya nagode, dabadan Allah yakawo ka ba bansan mezai faru da Salma ba."

    Ishaq ya sosa keya cikin farin ciki yace " ai duk lefinka ne, mezaisa ka bari Salma ta tarema, nifa kai........"
Kara Fulani ta saki, hakan yasa Ishaq yin shiru, Salman ya kalleta yace " aya Umma ta shiga wani hali, yazakiyi Umma gashidai Ishaq  yafad'i komai da bakinsa."

    Ishaq ya kalleta yace "Umma inafa da wayau hauka nake zan fad'amai, karyar Salman ne kawai yana za'ayi yasan nina je bigeshi bayan bai kula ba? Sai dai in yau yake nufi, wannan kuwa ai shiyakamani....."

Fulani mik'e wa tai cikin b'acin rai ta zo kusa dashi ta haska mai mari, tace wlh Ishaq nikam banyi sa'ar d'aba.

     Sarki ya fusata yace ke Sakina! Ai duk fadar sai da kowa ya juyo, cikin sanyin jiki Fulani ta zauna Ishaq kam ido yai wuri wuri, Sarki cikin b'acin rai yace "banataraku anan bane kowa yai abinda yaga dama ba, kuma duk abinda kukama Salman dake da d'anki karkuyi tunanin zan kyaleku, ada na d'auka kina kula da Salman, a'a koma bakya kula dashi banyi tunanin zakuma ku had'u keda d'anki ku muzguna ma Salman ba, yanzu da sanda ya bige Salman ya mutu fa? Sannan ko kunya harya samu damar shiga d'akinsa neman matarsa? Gidana yakoma gidan dabobi kenan ko me? To wlh daga shi har ke dakike biyemai sai kun fuskanci hukunci mai tsanani."

    Ishaq yasa kuka yace " Abba d'an Allah kayi hakuri nasan nayi laifi, wlh ni tun ina karami da k'in Salman na taso, kullum umma zancenta d'aya ne kar in kuskura in bari Salman ya wuceni akomai."

    Sarki ya kalli Fulani datai kasa da ido, da alama itama kwalla ke zubo mata.

    Sarki ya kalli Salman sannan ya kalli Ishaq yace " na cireka a matsayinka na yarima mai jiran gado, sannan nakuma bama Salman wannan mukamin."

    Fulani ta d'ago ta kalleshi cikin tsananin b'acin rai tace me kake nufi mai martaba? Ishaq shine babban d'anka a tunanina duk abinda yai zaka yafemai tunda shine magajinka kuma ni danake uwar gida, Fulani nice ya kamata d'ana yazama Sarki."

   Jitai Sarki yace " ahh namanta, gwara da kika tunamin kema ina sanar dake matsayinki na Fulani na cireshi daga yau......."
    Salman yace " Abba!!!"

  Sarki yace " kamanta na sanarma bazan yafema duk wanda ya nemi kad'eka ba? Sannan ko kunya Ishaq ya nemi matarka? Kuma duk nasan lefin mahaifiyarshi ce."

    Fulani cikin kuka tace" Alhaji ni zakawa haka? In ka cireni daga mukami na nida Ishaq alama ce ta mu mutu kawai, dama nasan ba sona kake ba, amma duk da haka bai kamata kamin haka ba."

     Sarki yace " kin d'auka shi kad'ai ne? Nasani sarai in na kauda Ishaq zakiyi tunanin saka Mannir ko wani daga cikin d'anki, bazaki tab'ajin kunyar abinda d'anki ya aikata ba, dan haka na yanke hukuncin dolene kibar nan gidan ki koma can karshen gida( inda ake kai iyayen sarki insun tsufa sosai ) anan zaki zauna."

Salman yace " Abba? Hukuncin kamar yayi tsauri." Sarki bai bashi amsa ba ya kalli Fulani dake kuka sosai tana bada hakuri, sannan ya kalli Ishaq yace kaikuma kashirya kaida iyalanka kubar nan ku koma kasar Egypt dazama kada kuma kadawo har sai in nina bada izinin hakan."
Abba yana gama fad'ar haka ya mike yai cikin gida, Fulani tasa kuka, Ishaq ma kuka yake sosai yana cewa "Salman d'an Allah kataimakemu, ni wlh duk Umma ce,  laifina d'aya danafara san Salma wannan kuma Salman kasan ba laifina bane laifin zuciya ne. "

    Salman ya kalleshi shikanshi tausayin hukuncin da Abba ya yankr yakeyi.

By *Ayusher Mohd*📚

© *NWA*
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄☄




*NA AYUSHER MOHD*



No: 6⃣0⃣


Salman ya kalli Ishaq duk sai kuma yaji Ishaq d'in na bashi tausayi, Waziri ne ya shigo ya kalli Salman yace " Yarima mai martaba yace ka ciga ciki."
    Salman ya kalli Waziri yace " Toh" mik'ewa yai ya d'an bugi kafad'ar Ishaq sannan ya kalli Fulani dake kuka yai ciki, Fulani tabishi da harara tare dacewa" niza'a wulakanta akan wani banza Salman? Wlh Sarki yayi kuskure."
   Ishaq ya matso kus da ita ya riko hannunta yace "Umma kitaimakeni kisa abarni akasar nan, ni wlh na tsani wata kasar."
     Fulani ta wafce hannunta tace " wato kanka ka sani kad'ai ko? Ni baka tausayin inda za'a kaini? A k'alla in na zauna acan kila sai nayi wajen sati 3 zuwa wata kafin 'ya'yana suzo su ganni."

    Jisukai Waziri yace " ku fito daga fad'a ba gurin hira bane, sannan kai yarima Ishaq katabbatar ka shirya d'an gobe zaka wuce, sannan Fulani au hajiya kema ki had'a kayanki yau dan gobe da safe zaki koma."
    Yana kainan yai waje, Fulani ta zuciya tace "me? Au hajiya? Sai na ci*********, "
    Ishaq ya kalleta yace " nidai Umma yanzu ba lokacin wani zagi bane ya kike so nayi?"
 Fulani ta watsamai wani kallo tace " duk ba kaikaja ba d'an rainin hankali, dalla matsamin." Ta fad'a tare da wucewa.
   Ishaq ya dunkule hannu ya naushi bango, yace " ni dai rayuwa ta gama b'aci, bansamu Salma ba, bansami mulki ba, garin muma yanzu ya fi karfina."
Shima waje yai jiki a sanyaye.
   Abinda zai baka mamaki kafin si fita zancen har ya yad'u agidan Sarki, suna tafiya bayi na kallansu suna d'an gulma.



     Salman zaune a gaban Sarki, Sarki yace" hukuncin baiyi ba kome?" Salman ya kara kasa dakai yace "a'a ba haka nake nufi ba sai dai ina ganin kamar hukuncin ya musu tsauri. "
    Sarki yai murmushi yace " mutanen da sukaso yin kisa? Da kuma hukuncin neman matar wani? Shine kake cewa d'an wannan hukuncin yai musu yawa? To ko kotu zan kaisu? Sai a banbance wanne yafi tsauri."
    Dasauri Salman yace " a'a Abba masan can sai yafi tsauri."
  Sarki yace " karka wani damu da wannan, ka maida hankalinka akan karatunka, inka gama kazo ka amshi mahaifinka."
Salman yai shiru.....
Hakan yasa Sarki yace " yaushe zaku fara jarabawa?"
 Salman yace " saura sati d'aya."
Sarki yace " good gwara ku gama kafin lokacin da likitan nan zai iso."

  Salman yai murmushi tare da cewa " amma Abba taron nad'in daza'amin a bari sai nagama ganin likitan." Sarki ya d'aga kai yace " hakan ma is a good idea."
Sunyi shiru kafin Salman yace "bari inkoma Abba, sai da safe."
Sarki ya amsa mai, nan ya mike yai waje.



    Mutane sai tayashi murna suke, shidai tafiyarsa kawai yake ba wanda ya amsawa, b'angarensa ya nufa, Salma na zaune a falo duk da ba kallo takeyi ba amma ta kurama tv ido, hankalinta nakan abinda hanne tace mata wai anba Salman yarima mai jiran gado, batama san sanda Salman ya shigo ba ya tura kofar tare da matsowa saitin wuyanta ta baya yace " me Beauty take tunani?"
Da sauru ta juya d'an tad'an tsorata, tace "haba Prince nafa tsorata. " tai maganar cikin shagwab'a,  shima kwaikwayar tata maganar yai yace " nima na tsorata" yasa mata d'ariya tad'an d'akeshi kad'an ya rike hannun tare da d'agota tayo jikinshi, hannunsa yasa a k'ugunta yace " bari mu gani ko Beauty tayi missing d'in mijinta sosai?" Yafad'a yana duba fuskarta, saurin rufe idanta tai, tace " ta ina ake gane wa?" Yace in nuna miki? Ta d'aga kai.
   Batai auni ba taji bakinshi anata, sosai yau take maidamai sun shagala sosai, kafin su saki juna, ahankali suka bud'e ido tare dayima juna murmushi,  Salman ya kamo hannunta yai d'aki da ita,  suna shiga ya rufe kofar ya tsaya ajikin kofar, ta matso kusa dashi tace " Prince baka fad'amin. ......jawota yai yakara kai bakinsa nata, nan suka kara tsundumawa cikin shauki, nikam har yanzu ban manta da korar da Salman yamin ba hakan yasa nai sumsum sum nai waje, tare da kara rufo musu kofar.


Bayan sun gama Salman yad'au Salma ya kaita toilet tace " au toilet d'inma bazan iya zuwa ba ko me?" Salman yace "banaso a wahalar min da baby na." Tace uhmmm.....harzai fita ta riko hannunsa, ya kalleta tare da mata alamar tambaya, itama dakai ta nunamai, ya kara mata alama dakai na bai gane ba, murmushi tai tace " muyi tare, " shima murmushin yai yace "ahhhh yau naji dad'i na.

Sunyi wanka sun fito, Salma ta wuce falo tad'an zubo ma Salman abinci kad'an a plate,  ita da kanta tabashi, sai daya gama yasha ruwa sannan ta maida tare da hawa kan gadon, Salman ya jawota jikinsa yace " Beauty akwai matsala fa? " ta kalleshi tace name? Nan ya sanar da ita abinda ke faruwa.

   Tai shiru, kafin can tace"Allah yasa hakan ne mafi alkairi." Salman yace "Amin, amma Beauty nifa banasan harkar mulkin nan, duk abi a hana mutum sakewa, ni dake fa sai lokaci_ lokaci ni kuma banasan hakan." Gabanta ne ya fad'i tace "lokaci_ lokaci? Muna gida d'ayan?" Yace" hmm yanzu in akaban me jiran gado, nasan halin mai martaba abubuwa zai d'inga sani, kinga zama na dake dole zai rago."
Salma ta kalleshi jitake kamar tai kuka, sai dai tana tunanin ko bazata ji dad'i ba dolene ta karfafama mijinta, tace " to menene baga waya ba? " tafad'a tare da nuna wayarta, yace uhmmm,  ta shige jikinshi tace " bacci nake ji.
Ta dade batai barci ba,  har Salman yai bacci, tai shiru tare da kura mai ido itakad'ai tasan meke ranta.


     Ishaq kam da Fulani da matan Ishaq bana tunani sunyi barci dan dukansu ba wanda yake farinciki.





By *Ayusher Mohd*📚
  © *NWA*
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄☄




*NA AYUSHER MOHD*



No: 6⃣1⃣



Da safe Salman yace Salma ta shirya yakaita gida, bayan ya kaita ya gaisa dasu Abba sannan yajuya ya koma gida, sam bayasan Salma takasance a gida arana irinta yau da gidan zai kasance a hargitse.

   Waziri da wasu fadawan ne sukazo suka tsaya a b'angaren Ishaq har sai da matanshi suka gama had'a kaya, kana kallan fuskokinsu kasan tabbas suna cikin bakin ciki.

  Fulani kam kuka sosai tai cikin dare sai dai da safe tana zaune tana kallan bayinta na had'a mata kayanta, ita kad'ai tasan bakin cikin dake damunta ga rabuwa da d'anta, matsayinta sannan korarta da akai, kana kallanta kasan bakin ciki ne fal zuciyarta.


   Salman yafito yai b'angaren Ishaq, ganin su waziri a tsatsaye yasa shi mamaki, karasawa yai suka gaisa ya tambayesu meke faruwa yagansu haka? Waziri yace" mai martaba ne ya umarcemu da mu tabbatar mun tsaya harsai Ishaq ya bar gidan nan ya shiga jirgi."
Salman ya kalli Waziri yace " haba a tunanina ko ba'a tsareshi haka ba zai tafi dakansa tunda yasan umarni ne ba shawara ba."
   Jiyai Ishaq yace " Salman inasan magana dakai." Salman ya juya ya kalleshi duk ya canza a kwana d'aya, binsa yai suka d'an keb'e, Ishaq ya kalli Salman yace " Salman nasani tunda kadawo kasarnan nake muzguna ma, bana kunyar yimaka sharri ko agaban mai martaba ne, ko ba'a fad'aba nasan bai kamata inma d'an uwana haka ba, amma azahiri kai kasan duk inda gidan sarauta yake to tabbas akwai hassada, kyashi da kuma san kai a ciki, sai dai bazan nemi yafiyar ka akan sharrin dana maka ba, dan nasan ko kaine ba shakka hakan zakayi, sai dai zan nemi yafiyarka akan abu biyu, na d'aya bigeka danaso yi, sannan neman matarka danai." Yana kai nan yai ajiyar zuciya idanunsa suka cika taf da kwalla.
   Salman ya kalleshi cikin tsananin tausayi, ya runtse ido sannan ya bude tare da cewa" Mubar zancen nan, dana yanzu dana da banasan adinga tunowa, abu d'aya nakeso kasa aranka, a duk inda kake kazama mai so wa d'an uwanka abinda kake sowa kanka, karka manta wannan kalmar hadisi ne sahihi, duk wani abu daya shiga tsakanina dakai nayafe ma."
 
   Ishaq ya kalleshi cikin hawaye ya riko hannunsa cikin kuka yace "Salman please take care of my mother,  nasani she is so greedy, amma tunda nake da ita bata tab'a bani shawarar neman Salma ko kad'eka ba, duk da batasanka."
 Salman ya dafashi yace " karka damu I will take care of her,  amma inkaje can me zakayi?"
   Ishaq yace " ban mayi wannan tunanin ba."
Murmushi Salman yai yace " u have to make plan, dan karkaje kawai kace zama zakai kaga dai zama ne bama shekara ba, mayb inka tafi ba dawowa zakai ba."
    Ishaq yace " nagode Salman."
Salman dakanshi yakaisu airport da azahar suka tashi, baiji dad'in yanda Sarki ya had'ema Ishaq rai ba dayaje masa sallama.


    Yana dawowa gida yatadda Fulani har ta tattara ta koma, yai ajiyar zuciya yace " why am I feeling so empty? "

   Salma kam taji dad'in zuwa gidan nan tayi mamakin yanda aka gyara gidan, sam bazakace gidansu ne na da ba, goggo sai janta a jiki take, sun sha hira da Abbanta, nan ya fad'a mata ai kamal ya kusa komawa kasar waje d'an yin masters d'inshi, takalli Abba tace " Abba zanma Salman magana, akwai naga mutanen da ake  d'eba na scholarship a gidan Sarki, duk da dai naga 'yan uwane yawanci amma nasan in namai magana zaisa sunanshi"
Abba yace kina ganin ba matsala?
Tai dariya tace " yasan komai Abba ba wata matsala. "

  Salma duk yanda taso suyi hira da umma amma abin ya gaggara hakan yasa ta hakura ta koma gun Abbanta.


     Sai bayan magrib Salman yazo, sun gaisa da Abba sai daya shigo yaga gyaram gidan da akai lalai komai yayi kyau, Abba ya kara mai godiya sosai sannan yagaudasu umma da goggo, sannan suka fito.

  A hanya ne Salma ta sanar dashi zancen kamal, Salman ya mata wani kallo yace " tsohuwar zuma ce ta motsa?" Dariya tai tace " ai kafi kowa sanin ba wata tsohuwar zuma araina, daga sabuwae har tsohuwar mutum d'aya kawai nasani."

    Kallanta yai yad'an d'age gira yace "mutum d'ayan dai ko ba'a fad'a ba nasa nine."
   Tad'an murgud'a baki tace "irin wannan confidence haka?"

  Yace "kinsan nayarda dakaina, no doubt. "

Tace "ahhhh namanta ne, but what can we do? Sai kuma yakasance bakai bane Mr self-assurance?"

Salman ya kalleta yace "ban gane ba?"

Tad'an langwab'ar da kanta batace komai ba.

Salman cikin b'acin rai yai gefe da motar yai parking,  ta guntse dariyata tare da maida kanta tana kallan window, Salman yasa hannu ya juyo da fuskarta, yace " Beauty  magana nake." Juyowa tai ta had'e rai tace " inaji Mr self-assurance."
    Yace " me kike nufi da kalamanki?"
Tace " me nake nufi kuwa?"
Yace " karkisa naje na fasama kamal baki wlh, dama inajin haushi banine first love d'inki ba kar ki kara b'atan rai."
 Dariya ta kwashe dashi tace " Prince kanada abin dariya wlh, ni fa matarka ce banasan mud'inga zancen wani kamal inbadai aharkar 'yan uwan taka ba."
   Yace " to ai kece kika zo min da magana abaibai."
  Salma tace "uhmm  nad'auka Mr Prince duk abaibai d'in danai magana zai gane, tunda dai shi ya koyamin."


    Salman yace " ohhh dama saboda ni kikai? Band'auka kema kin koyaba ai."
Tace "ina zaune dakai ai dole ne."
Kunnenta yad'an ja tace ahhh, yace " ramawa nai......dariya sukai atare, nan suka wuce gida.




      Yau Salman sun gama jarabawa kuma a yau akesa ran za'a kwantar dashi a asibiti danyin treatment,  dan yau da yamma akesa ran zuwan Dr Bilal da matarsa Dr Ilham.

Salma ta had'a musu kayansu a akwati, duk yanda akaso a hanata zama acan saboda larurarta amma taki, hakan yasa sarki yace akyaleta, Fulani kusan kullum sai tayi abun marmari ta aikoma Matar Munnir dake da ciki da kuma Salma, Salma kam tsoron ci takeyi sai dai ganin mai kawowar bata take ta zab'a kafin takaima matar munnir yasa ta fara rage kokuntan ko magani ne a ciki.



     Farha kam mahaifiyarya taji bakin cikin korota da akai, sai dai yazasuyi? Da Mumyn ta kira Sarki dan tai fad'a sai ya gwaleta yace " yama za'ayi ace yarinya takai shekara 25 amma ba zaku mata aure ba? Sai dai tai ta yawo a gari, wannan dalilim yasa tama daina kiran Sarkin.




By *Ayusher Mohd*📚


© *NWA*
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄☄




*NA AYUSHER MOHD*



No: 6⃣2⃣

    Bayan Shekara 3...........

Salman zaune akan dinning shida d'ansa Salim, Salma tazo kusa dashi ta zaune tace " Prince dagaske kake wai?"
   Salman ya kalleta sannan ya shafa kan Salim yace " Beauty wai dole ne sai naje wani matriculation?  Ni yaro ne?"
  Salma tad'an had'e rai tace " yara ne ke zuwa?" Salman ya kalleta zaiyi magana wayarshi tai kara yad'aga tare da cewa " Najib ya akai?" Najib yace " malam Yarima mai jiran Gadon Sarki bawai dan anaso Sarki ya mutu ba sai dan hakan Al'ada ta tsara."
   Saki yai yace " kafara ko? In roko ka fara to zan iya taimaka maka da kalangu."

    Najib ya kwashe da dariya yace " kaii mutumin akwai iya fad'ar bakar magana, yah zaka shigo kuwa? Su dad zasuzo fa."

     Salman yace " kai fa banza ne, meyasa baka sanar dani da wuri ba? Gashi nikuma banda niyar hallatar taron."
    Najib yace " haba yarima kafasan yanda Director yabada umarnin kaje saboda akwai kyauta dasuke san baka."
   Yai wani murmushi yace" kyalesu so suke suyi neman suna gun mai martaba, ko an fad'a musu ban sani bane."
 
   Najib yace " to yanzu ya za'ayi?"
Salman yace" zanzo bayan an gama sai mu gaisa dasu Dad d'in."
  Nan sukai sallama ya kashe wayar.

   Salma ta kalli Salim tace" Ma boy jeka akaika gun Fulani tun jiya take aiken nemanka."
Cikin murna yace to.
  Yana fita Salma ta harari Salman tai d'aki, murmushi yai tare da mik'ewa yai d'akin, tana zaune akan gado, yana zuwa ya kwanta akan cinyarta, tare da sai ta fuskarshi kan nata, yace " Beauty muje yawo?"

  Salma tace " indai bazaka ba shikenan, dama bansan mai martaba yaga baka hallarci taron bane. "

 Salman ya shafa cikinta yace " Baby na kinga Mumynki na neman tilastama mahaifinki abinda baya so ko?"
   Salma ta shafa kan Salman tace "kaima kasan ba haka bane Abba nasan Umma bazata ma haka." Tai magana amatsayin wai babyn

   Ajiyar zuciya yai yace " Babyna I wish mace ce mai kama da Beauty na kinga sai in mata rival, ni dama ban tab'a ganin magajin Sarki da mata d'aya ba sai ni."

    Salma tai dariya tare da manna mai kiss a kumatu tace " na daina tambayar tunda an fara zancen rival."

 Shigewa jikinta yai tad'an mai shakulkuli ta ciki tace " kar ka matse mana babyn mu."
Yace 3mnt ko? Tace yeah

 Turata yai kan gadon tare da jawota jikinsa, yace " Beauty wai sai naje?" Ta girgiza kai alamar a'a tace " Ur choice. "
 Ahankali ya kai bakinshi nata............

Ya shirya tsaf ya kalli Salma yace " Zan wuce." Tace sai ka dawo, Allah ya bada sa'a." Yace amin "amma taso muje tare indai kinaso naje."
 Murmushi tai ita kanta tanason zuwa, gyara fuskarta tai, Salman yakalleta yace " ni fa banasan zuwa dake gun taro, maza suyi ta wani kallanki, narasa meyasa Abba kwanakin nan yai ta sakamu hallarta taro tare, haushi duk ya isheni."

 Dariya tai tace" to ko inzauna?" Yace " yau ni nakeso muje tare saboda nasan kinasan zuwa, koba yau zee zata gama ba itama? Sannan inaso kiga matar da Najib zai aura."

  Nan suka gama kintsawa suka fito.

Wata had'ad'iyar Motarsa mai masifar kyau suka shiga, sam yanzu anhanashi fita shi kad'ai, hakan yasa dole akwai mota d'aya da akesa fadawa suke rakashi inda zashi.


   Yafara tuki tare da kallan bayanshi ya kalli motar haushi ya isheshi,  yai kwafa yace " Who am I?" Salma tace" The Prince!!!!!" Yai wani mugun murmushi yace " Sa belts dear." Tasa tare da cewa me za'ai? Ya kalleta yai murmushi tare kara gudun motar, nan yadinga shiga cikin d'an lungun hanya daya gani, sun rikece suna binshi, sai dai ina, salon da Salman yake musu yasa sun rasa inda yai.


   Sai dayaga ya b'acemusu b'at sannan yai wani murmushi, Salma ta tafa mai tace " irin wannan salo?"
Yace "inama ni ba d'qn sarauta bane, da mota zan koya miki mud'inga fita bayan gari muna tsere."

Dariya tai tace " stop Imagine, nikam kuna waya da Dr Bilal?"

 Salman yai murmushi yace " guy d'in nan da matarsa sunyi, ba sa'idan kowa akansu, rayuwarsu free."

  Salma tai shiru, can tace" amma fa ance aunga rayuwa, sai dai naji dad'in yadda yawarkarmun da My Prince."

Murmushi sukai Salman ya wuce skul d'in dadinshi d'aya bai fad'a ma fadawar  inda zasu ba, kuma a iya saninsu bazai je makaranta yau ba.




Anyi taro lafiya Salman an kirashi ya amshi kyauta amma yanajinsu ya sharesu, sai Mannir ne ya amsar mai a matsayin sa.


   Salma tayi farin cikin ganin zee, sunsha hira nan Zee take tambayar Salma labarin Kamal, Salma tace yana can naji Abba yace ya samu aiki acan, zee tace lalai.


Ishaq kam yanzu rayuwa tazama saisa saisa, duk da ana tura musu kud'i kuma yana karatu, amma yanzu ya koma shiru shiru, sam bayasan garin, amma ya zai yi?



   Fulani kam an shiryu kusam kullum sai ta nemi akai Salim da kuma 'yar gidan Mannir( Zulfa) sun tayata hira.



   Farha kam anata shirin bikinta, Salman yace zasuje shida Salma....
...........





After 6years...........

  Salman zaune akan kujerar mulki, yana karanta korafe korafen mutane, wazirinsa na yanzu shine ya kalleshi yace "Ranka ya dad'e  bai kamata ace har yanzu matarka d'aya ba."
   Salman ya bugamai wani kallo yace" in na kara auren kai zaka rik'emin matar? Ko kuwa mutanen dakesan in aure 'ya'yansu suke turoka su zasu zaunamin da ita? ."

   Waziri ya had'iyi yawo yace" ya hakuri ranka ya dade ba haka nake nufi ba."
   Salman yace " ko ma me kake nufi, sannan ban fahimci wannan takardar ba."

   Waziri ya kalli takardar, yace " eh wani babban d'an kasuwa ne yakeso kad'an taimaka mai da sa hannu."
   Salman yai tsaki tare da wurgo takardar yace " ina sa mai hannu sai yaje yai ta shigo da kayan da basu dace ba yace nine na bada izini ko?"
Waziri yace "ba haka bane, zai d'inga aiko da kud'aden da kadarori masu yawa ai."



   Salman yai murmushin sa yace" bama bukatar kud'insa in bazai abu dan Allah ba ya barshi, sannan kar in kara ganin takardu shigen wannan anan gurin."

  Waziri yad'an tab'e baki a zuciyarsa yace " wannan wani irin mutum ne? Yaza'ayi mu tara arziki in baya.....

Salman ne ya katseshi yace jeka na sallameka, waziri ya mike yana fita yai ajiyar zuciya yace" kaiii!!!!!! Haka zan d'inga fama kullum?"



    Salman kam yana ganin waziri ya fita ya kira Salma, tad'aga da sauri tare da cewa "My Prince gaskiya I miss u."
 Yace "mee too dear, ina Swty na?" Tace gani nan.
  Yace " not u new nake nufi, murmushi tai tace gatannan tana barci."

  Yace shafamin kanta....tace yaushe zan ganka? Yace yau da aiki amma zan tsagaita inshigo, tace sai na ganka.....

Nan sukai sallama tabi wayar da kallo, ga shi dai yanzu arziki itada 'yan uwanta ba'a magana, ga matsayi na Fulani an batan ga yaransu guda Uku, 1 namiji, 2 mata, sai dai tarage zama da mijinta sosai, yazatai haka rayuwa take ba'asamun komai dole in an samu d'aya a rasa d'aya.





*ALHAMDULILA NAN NAKAWO KARSHEN LITTAFINA MAI TAKEN 'NI DA PRINCE' BANSAN IYA YAWON GODIYA DA ZAN NUNAMA D'UNBIN MASOYANA BA, NAGODE KWARAI DASO DA KAUNAR DA KUKA NUNA MA LITTAFINAN, ALLAH YABARMU TARE........*



*THANKS ALOT ALL MY FANS.....LOVE YOU SOOOOO MUCH*💋





*Godiya ta musamman ga duk 'yan group d'ina, dakuma 'yan uwana writers nagode sosai Allah yasaka da alkairi da zumunci da san da kuka nunamin.*


_*Jinjina Gareku ' yan Nagarta Writer's Association nagode kwarai Allah ya kara d'aukaka*_



My fans sai kunjini a sabon novel d'ina nan gaba........




By *AYUSHER MOHD*📚
© *NWA*

Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Abdul Mk at 11:56
In Hausa Novels
NI DA PRINCE ( FINAL ) Title : NI DA PRINCE ( FINAL )
Description : By *AYUSHER MOHD*📚      © *NWA* [11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄☄ 💥 *NI DA PRINCE*💥 ☄☄☄☄☄☄☄☄ *NA AYUSHER MOHD* No: 5⃣9⃣ ...
Rating : 5
Related Posts: Hausa Novels

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

1 Response to "NI DA PRINCE ( FINAL )"

Mimi said...

Macha Allah

12 July 2017 at 20:30

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ▼  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ▼  July (223)
      • Photos; Daya Daga Cikin Hanyoyin Makircin Shedan D...
      • 'Yan Sanda Sun Kama Masu Luwadi 42 A Wani Hotel A...
      • Wasu 'Yan Mata 3 Sun Yi Wa Fasto Fyade
      • Ba za a rufe Jami’ar Maiduguri ba – Ministan Ilmi
      • Graphic Photos: Wani Bafullace Ya Sare Wa Wani Mat...
      • Duniyar Fina Finan Hausa Ta Samu Magajin Ibiro.
      • Gamayyar Mata Nason A Halasta Sana'ar Karuwanci A ...
      • Ubangiji Ya Karbi Addu'o'in Talakawa Kan Buhari- G...
      • REGRETS -(KA CUCE NI) Episode 13
      • Video: Ciki Da Raino Official Trailer Starring Fal...
      • Ramuwar Gayya: Ya Yiwa Yar Shekara 12 Fyade, Shima...
      • AN KADDAMAR DA DAN TAKARAR DAN MAJALISAR WAKILAI N...
      • Photos:Gwamnonin da suka Ziyarci Buhari sun Dauko ...
      • PHOTOS: An Kaddamar Da Ofishin Sojojin Sama A Jiha...
      • Fasto Ya Illata Ta Saboda Ta Daina Zuwa Ibada Cocinsa
      • REGRETS -(KA CUCE NI) Episode 12
      • Manchester City ta Lallasa Real Madrid daci 4-1
      • Photos: Sanata Kwankwaso ya tapi ziyar tar dalibai...
      • Photos: Yar Asalin Jihar Bauchi Ta Yi Zarra A Birn...
      • Sojoji sun kubutar da masu hako danyen mai da aka ...
      • REGRETS -(KA CUCENI) Episode 11
      • Real Madrid Da Barcelona Zasu Kara Sau Uku A Kwana...
      • Graphic Photos: Sojoji Sun Bindige Dan A Daidaita ...
      • Photos: Wani Magidanci Ya Koka Da Dawainiyar Shaya...
      • REGRETS -(KA CUCE NI) Episode 10
      • Photos: Wasu 'Yan Uwan Gwamna Ganduje Sun Koma Aki...
      • Gwamnonin Jam'iyyar PDP Zasu Ziyarci Buhari Yau
      • Yadda Muka Gana Da Buhari A Landan, Cewar Gwamna R...
      • REGRETS -(KA CUCE NI) Episode 9
      • An Fafata Tsakanin Yan Boko Haram da yan sanda saf...
      • Wasu Matasan 'Yan Boko Haram Sun Mika Wuya Ga Sojoji
      • REGRETS -(KA CUCE NI) Episode 8
      • An Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomi A Legas
      • Neymar Na Shirin Barin Barcelona Zuwa PSG
      • Photos: Wani Magidanci A Jihar Kebbi YaYi Wa Matar...
      • Buratai Ya Ba Da Wa'adin Kwana 40 A Kamo Shekau A ...
      • REGRETS -(KA CUCE NI) Episode 7
      • CHELSEA TA dauki Morata daga Real Madrid
      • Na Yi Shekara Uku Ina Soyayya Da Nafisa Abdullahi ...
      • Graphics Photos: Wasu 'Yan Ta'adda Sun Yi Wa Wani ...
      • SUBHANALLAH: Wani Sabon Annabi Ya Bayyana A Kasar
      • Mohammed Nadada Umar Ya Zama Sabon Sakataren Gwamn...
      • An Dage Shirya Fim Din Aliko Zuwa Wani Dan Lokaci
      • Gwamnan Bauchi Ya Sauke kwamishinoninsa Da Sakatar...
      • Photos: The Stunning New Look Of Tonto Dikeh
      • An Yanke Masa Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rayata Bisa ...
      • An kama wani likitan bogi dake gogawa mararsa lafi...
      • An Bukaci Karfafa Tsaro Kan Rikicin Kudancin Kaduna
      • REGRETS -(KA CUCE NI) Episode 6
      • An Farfasa Kawunan Wasu Shugabannin APC A Jihar Lagos
      • Kira Da Babban Murya Ga GwamnatinJijar Bauchi
      • Arsenal Tana Neman Dan Wasan Real Madrid – Benzema
      • Adadin Kudaden Paris Club Da Gwamnatin Tarayya Ta ...
      • Tsoho Mai Shekaru 74 Ya Yi Wa Jikar Shi Mai Shekar...
      • KABEER PART 4 (END)
      • REGRETS -(KA CUCE NI) Part 5
      • Yan Sanda Sun Kama Wani Inyamuri Da Kwayoyi Na Kim...
      • Photos: Dubu Wani Barawon Mota Ta Cika A Kano
      • BAM YA KARA TASHI A DAREN JIYA A MAIDUGURI.
      • Photos: Yusutzai Malala Ta Ziyarci Gwamnan Jihar B...
      • KABEER PART 3
      • REGRETS-(KA CUCE NI) Part 4
      • Saeed Nagudu Na Fama Da Rashin Lafiya
      • Yan Nigeria na son jam'iyyar PDP ta dawo mulkin ka...
      • Photos: Wata Mata Ta Biya Dubu Goma An Kashe Mijin...
      • Wasiyyar Da Dan Masanin Kano Ya Yi Min - Hadiza Gabon
      • Hada-Hadan kasuwan Kwallon Kafa a Yau
      • Photos: Adam A Zango Ya Kai Ziyarar Ta'aziyya Gida...
      • Matasa Sun Gargadi Gwamna Fayose Da Ya Iya Bakinsa...
      • Photos: Yau Bikin Ranar Murna Haihuwar Sabuwar Jar...
      • An Hana Saraki Ganin Buhari A Birnin Landan
      • Mutane Goma Sun Mutu A Fashewar Bututun Iskar Gas ...
      • KABEER PART 2
      • Ka cuce Ni Part 3
      • Kabeer Part 1
      • Saraki Ya Gagara Ganin Buhari A Birnin Landan
      • Photos: Wani Matashi Ya Cakawa Kansa Wuka A Potiskum
      • PDP Ta Koma Hannun Barayi - Sanata Ali Modu Shariff
      • REGRETS -(KA CUCE NI) :Episode 2
      • NIGERIAN PROFESSIONAL FOOTBALL LEAGUE FIXTURES #WE...
      • Video: Hotuna Daga Wajen Bikin Sunan Jaririyar Sad...
      • Osibanjo Zai Ziyarci Jihar Zamfara
      • PHOTOS : JADAWALIN WASANNIN GASAR PRIMIER TA NIGER...
      • WASU BARAYI SUN CAKKA MAWANI MUTUM WUKA DAN SU KAR...
      • Photos: Sabin Hutuna Bilkeesu Abdullahi
      • PHOTOS : MAWAKI NAZIRU M. AHMAD YAYI AURE NA BIYU
      • Ambaliyar ruwa ta yi barna a Kaita Jihar Katsina
      • PHOTOS : JAMI'IN CIVIL DEFENCE YA HARBE WANI DIREB...
      • PHOTOS : ANYI SALLAR JANA'IZAN HON. ABDULLAHI MUHA...
      • KAYLE WALKER YA KOMA MANCHESTER CITY
      • PHOTOS : DAN WASAN KANO PILLARS ZAI ANGONCE
      • Photos: Baba Ari Ya Ziyarci Abba Kyari
      • Photos: Yau Bikin Murna Ranar Haihuwa Jaruma Kanny...
      • Fulani Makiyaya Za Su Maka Gwamnatin Taraba Kotun ...
      • Ka Cuce Ni Part 1
      • Photod: Hutuna Sabuwar Jarumar Kannywood Bilkeesu ...
      • Wata Jiha a Malaysia za ta fara aiki da hukuncin b...
      • Photos: Sani Danja Da Mansura Isah Sun Yi Bikin Ci...
      • An Haramta Karuwanci, Shaye-shaye Da Gidajen Sinim...
      • Etisalat Najeriya Ya Sauya Suna Zuwa 9Mobile
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ►  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ►  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Fantyz Guy ft Mr SPYZY - ALKALERI GARINA (Official Hausa HipHop Music Video...
        Bauchi Base Popular HipHop musician FANTYZ GUY release hit track ALKALERI GARIN Featuring Mr SPYZY 
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • Zuwa Da Budurwa Yawon Duniya ( Kalli Kaci Dariya)
  • Rikicin Tsakanin Hadiza Gabon Da Zaharadeen Sani ( Bayanai Da Rahoto) S...
  • The Missing seven-year-old boy found dead in Kano
    Seven-year-old Khalifa Saminu Saleh was tragically found deceased six days after he was reported missing in the Kuruma community...
  • Yadda Kotu Ta Daure Bobrisky Watanni Shida Ba Tare Da Zabin Biyan Tara Ba
    Kotu ta daure Bobrisky watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba Babbar kotu a jihar Lagos ta yanke hukunci ga Idris Okuneye da a...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger