1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Uncategories » Video: KIWON LAFIYA - Bayani Kan Cutar Kyanda Tare Da Hajiya Khadijah Faruq

Video: KIWON LAFIYA - Bayani Kan Cutar Kyanda Tare Da Hajiya Khadijah Faruq

By Abdul Mk
Add Comment
Wednesday, 24 May 2017


A cigaba da shirye shiryen mu na kiwon lafiya 1AREWA TV ofishin Red Cross ta jihar Bauchi a yanda tayi hira da Hajiya Khadijah Faruq, akan cutar Shartuwa ( Kyanda )


Ga Yanda Hira takaya




Hanyoyi Kariya Daga Cutar Kyanda
Ko me ke kawo ciwon kyanda kuma ko ya ake daukarsa? A kuma fada mana alamun ciwon da hanyoyin kariya. Na gode. Daga Musa Dudunni, Kusada
Amsa: Ciwon kyanda ko bakon dauro wani ciwo ne da a yanzu haka a wannan lokaci yara da yawa ke fama da shi saboda busasshiyar iska ta hunturu da rani da ke kadawa a Arewa. Wato su kwayoyin cutar iska suke bi sai a shake su idan an yi tari ko atishawa. Wasu kwayoyin cuta na ‘birus’ ne ke kawo ciwon. kwayoyin cutar sun fi kama yara ’yan kasa da shekaru biyar wadanda garkuwar jikinsu ba ta yi kwari ba. An kiyasta cewa a dan tsakanin wata biyu baya, yara fiye da 2,000 tuni sun riga mu gidan gaskiya a garuruwan Arewa da dama, sakamakon bullar ciwon.
Alamun ciwon su ne da farko yaro zai fara ciwo kamar mura, har idanu su rika yin ruwa suna ja, daga nan sai zazzabi, yaro ya kasa cin abinci. Daga nan sai a ga wasu kananan kuraje sun feso masa duk jikin, har baki. Wadannan kuraje sukan yi kaikayi sosai. Daga nan kuma ko dai jiki ya yaki kwayoyin cutar, ko kuma su ci gaba da jawo lahani. Misali, daga makogwaro har cikin kunne sukan iya shiga su kawo ciwon kunne. A ido ma sukan iya huda farin ido, idan suka shiga kirji kuma su kawo numoniya. Sai an dauki matakin karawa yaro kaifin garkuwar jiki kafin ya iya shawo kansu. Duk wannan yakan dauki misalin sati biyu yaro na fama. Yara masu karyayyar garkuwar jiki kamar masu ciwon kanjamau da ciwon suga ke nan sun fi shan wahala, tun da jikinsu yakan dau lokaci mai dan tsawo yana yakarsu.
Amma idan yaro yana da kwarin garkuwar jiki ba za a ma gane kyanda ba ce, domin ’yar mura kawai zai yi ta kwana uku zuwa hudu ya warke. Wasunsu ma ko murar ba sa yi, amma za su iya sa wa wani.
Hanyoyin kariya daga wannan cuta kan fara tun daga lokacin da aka haifi yaro. Idan aka ba jariri nonon uwa zalla har wata shida ba ko ruwa, to garkuwar jikinsa za ta fi ta sauran yara karfi, ta yadda ba zai rika cutuka sosai ba. Sai kuma allurar riga-kafin ita kwayar cutar da ake yi a wata tara. Yawanci wadanda suke yin ciwon ba a yi musu allurar riga-kafin ba.
Sauran hanyoyin kariya sun hada da saurin kai mai ciwon asibiti da ware masa wurin kwanciya daban da na sauran yaran gida don kada ya yada musu da samar masa soson wanka nasa na daban don kada ruwan majina ko na kurajen jikinsa su sa kwayoyin cutar a jikin soson. Sai kuma yawan wanke hannayen yaran gidan da sabulu. Ko makaranta mai ciwon bai kamata ya je ba tsawon ’yan wadannan kwanakin da yake ciwon, don kada ya yada ta.
Shin mene ne ciwon gonorrhea kuma wane magani ne ko allura mai ciwon sanyi na gonorrhea zai yi amfani da shi kafin ya kai ga zuwa asibiti?
Daga danmaryam, Kebbi
Amsa: To bari a ba dalibin likita, Umar Musa Gwadabawa fagen ya amsa maka tambayar taka, inda ya ce: Ciwon sanyi na ‘gonorrhoea’ cuta ce da ake samu daga mace zuwa namiji ko namiji zuwa mace. kwayar cutar bacteria mai suna Neisseria Gonorrhoea ke kawo ciwon. kwayar tana rayuwa a wuri mai danshi da ruwa a jiki kamar a mahaifa, ko mafitsara, haka kuma a baki da ido.
daukar cutar a ido kan faru ne a jarirai, idan jariri ya kwashi kwayoyin cutar yayin haihuwa a kwararon hanyar fitowa duniya. A wannan lokaci ne za a ga idanun sabon jariri na kwantsa, yana ja. Idan a gida aka haihu, dole a kai jariri asibiti a ba shi magani, saboda kwayar cutar kan jawo makanta.
Ba a daukar cutar sanyin ta hanyar musabaha ko zama a bayan gida inda mai cutar ya zauna.
Wadanda suka fi zama cikin hadari ke nan su ne masu mu’amala da mata masu zaman kansu, domin mata su ke da kwayar cutar amma ba wasu alamun cuta a jikinsu da za a gane sai an yi gwaji.
Alamomin cutar ke nan sun bambanta daga mace zuwa namiji. Mafi yawan mata masu cutar ba su cika nuna wata alama ba. Amma a maza wadanda ke nuna alama takan bayyana bayan kwana goma da kamuwa. Ga alamomin kamar haka:
1-Ciwo ko jin zogi lokacin fitsari. 2-Ganin farin ruwa karshen fitsari. 3-Kumburi ko ciwo ga ’yan maraina. Da zarar an ga wadannan alamu sai a gaggauta ganin likita.
Gwajin da ake yi domin gano cutar, kuma wanda ya kaamata a yi wa duk wanda ake tunanin yana fama da ciwon, sun hada da: 1-daukar farin ruwan a kai dakin gwaji domin a gwada. 2-Sai kuma gwajin fitsari. Za ka iya zuwa asibiti a yi maka wannan gwaji idan kana tsammanin kana dauke da kwayar cutar.
Maganin cutar ya danganta da irin karfinta a jikin mutum, domin akwai har allurai ma, kuma sai ma’aikacin asibiti ya rubuta. Don haka ba kai za je ka sawo magani ka sha ba. Idan aka ba da maganinta ga mutum, to ya tabbata ya sha na tsawon lokacin ko da ya ji sauki kafin su kare.
Matsalar cutar kan yi muni idan aka ki daukar matakin magance ta. Tana kawo matsaloli da yawa ga mata kamar: 1-Jawo mummunar illa ga kwayoyin halitta masu kula da haihuwa, wadanda ke haddasa rashin daukar ciki. 2-Yiyuwar yaduwar cutar zuwa wasu bangarori na jiki. 3-Yiyuwar kamuwa da cutar kanjamau. 4-Lokacin da aka samu juna biyu matar da ke dauke da cutar sanyi kuma ba a yi maganinta ba, takan haifar da barin juna biyun. 5-Haka kuma abin da ke cikin cikinta kan kamu da cutar ta ido, lokacin haihuwarsa.
Hanyoyin da ya kamata ma’aurata su bi wajen kariya daga cutar su ne: 1-Zama masu amana tsakanin juna. 2-Kada a ji kunyar zuwa ganin likita. 3-Masu juna biyu su je awo inda za a yi musu gwajin cutar. 4-A yi kokarin shanye dukkan magungunan da aka bayar a asibiti. 5-Ga mai iyali fiye da daya, yana da kyau idan yana dauke da cutar to ya je da dukkan iyalin domin a yi musu gwaji. Gwaji a mata ita ce kawai hanyar da ake gane ciwon. 6-Sa’annan kuma kada a yi mu’amala da mai cutar har sai ya warke.
Ina tambaya  akan yankan farce da ake yi wa mutane. Na kan ga idan aka gama yankewa wani sai a kunna wuta a kona bakin almakashin kafin a yi wa wani kuma. To hakan ba zai sa a dauki cutar kanjamau ba ke nan? A yi min karin haske.
Daga Matar Soja
Amsa: E, duk lokacin da aka sa wuta a jikin wani karfe na dan lokaci ana iya kashe kwayoyin cutar da ke jikinsa, har kwayar cutar kanjamau kuwa. Don haka ne ake cewa masu yankan farce dole ne su gasa abin yankansu duk bayan yi wa kowane mutum, domin kiyaye yada cututtuka.
Duk lokacin da na yi tukin mota na yi ’yar tafiya mai dan nisa kamar kilomita 90, to da na sauko daga motar sai in ji na gaji, kafafuwana wani lokacin sai su rika mani ciwo har sai na kai ga dangyashi kafin su warware.
Daga Aminu M. Mai’aduwa
Amsa: E, ai dama cewa muka yi dole ka rika fita kana mike kafa idan kana samun irin haka. Muka ce akwai mutanen da ’yar tafiya kadan idan suka jima a zaune dole su ji wannan minjiryar ta rike kafa, musamman ma idan suna da nauyi sosai. Ba ciwo ba ne domin da ka tsaya da motar ka fito ka dan taka abin zai sake ka. Duk lokacin da mutum ya ji hakan ko kilomita ashirin ne, ya fi kyau a fito a mike kafa a koma.
Mene ne gaskiyar da ake cewa idan gashin kyanwa ya shigar wa mutum baki yana kawo tari na fitar hankali?
Daga Ali Fancy, Garko
Amsa: A’a, ba gaskiya a zancen. Akwai dai mutanen da ke samun borin jini idan wani abu kamar kura ko gashin kyanwa ko na wata dabba ko tsinken karmami ya shiga hancinsu ba bakinsu ba, ciwon da ake kira ‘hay feber’ wanda kan sa hanci kaikayi ya kawo mura mai zafi wadda ba ta tafiya cikin sauki. Duk da cewa mu ma mukan samu ciwon amma dai an fi samun borin jini mai tsanani a tsakanin Turawa, ba bakake ba.
Wai shin da gaske ne yawan kwanciya a kan dabe na ‘tiles’ yana kawo ciwon nimoniya?
Daga Baban Kulu, Lafiyan Bare-Bari
Amsa: Numoniya ciwo ne da kwayoyin cuta kan kawo ba sanyi ba. Da sanyi ne ke kawo shi da mutanen kasashen da ake sanyi sosai wanda ya fi namu tuni sun kare da numoniya. A kwayoyin cututtukan da ke sa ciwon numoniya (tunda suna da yawa) akwai wadda dai ta fi son sanyi da danshi.
Daga Aminiya

Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Abdul Mk at 19:56
Video: KIWON LAFIYA - Bayani Kan Cutar Kyanda Tare Da Hajiya Khadijah Faruq Title : Video: KIWON LAFIYA - Bayani Kan Cutar Kyanda Tare Da Hajiya Khadijah Faruq
Description : A cigaba da shirye shiryen mu na kiwon lafiya 1AREWA TV ofishin Red Cross ta jihar Bauchi a yanda tayi hira da Hajiya Khadijah Faruq...
Rating : 5
Related Posts:

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Video: KIWON LAFIYA - Bayani Kan Cutar Kyanda Tare Da Hajiya Khadijah Faruq"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ▼  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ▼  May (54)
      • DSS Ta Sake Kama Jarumar Kannywood Rabi Ismail Bay...
      • An Yi Garkuwa Da Wani Dan Majalisar Tarayya
      • Akwai Kyakkyawar Alaka Tsakanina Da Buhari - Saraki
      • Video: Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum Ramadan...
      • Video: Sheikh Usman Abdullahi Karo Ramadan Tafsir ...
      • Photos: Aisha Buhari Ta Tafi Landan Ganin Mijinta
      • Za A Raba Naira Miliyan Ɗari A Bauchi
      • Photos: Ba Kowace Jaruma Bace Zata Iya Yin Abin Da...
      • Barcelona Ta Nada Sabon Kocin Ta
      • Video: Ramadan Tafsir Day 2 ..Na Sheikh Usman Abdu...
      • Photos: An Jefe Magidanci Har Lahira Saboda Yin Zi...
      • Photos: Karuwai, Makada Da 'Yan Chacha Sun Mamaye ...
      • Sakon Sheikh Dahiru Usman Bauchi A Wajen Bude Kara...
      • Mutuwa Ce Kawai Za Ta Hana Mu Kafa Yankin Biafara,...
      • Ramadan Tafsir Day 1 ..Na Sheikh Usman Abdullahi Karo
      • Video: Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum Ramadan...
      • Video: Paul Pogba A Saudiyya Dan Yi Umrah
      • Graphic Photos: An Zo Har Gida An Sassare Ni Ne Sa...
      • Graphic Photos: Dan Kwallon Kwara United Ya Mutu A...
      • Video: KIWON LAFIYA - Bayani Kan Cutar Kyanda Tare...
      • Photos: Wasu Matasa Biyu Sun Kashe Mutane Uku Akan...
      • New Music: This Life By Daht-Kid.. Hausa HipHop
      • Graphic Photos: An Kashe Barayin Da Suka Je Sata A...
      • Video: Daga Jama'a Episode 1.. Shin Zaka Zabi Buha...
      • Osinbajo Zai Ziyarci Jihar Katsina Don Kaddamar Da...
      • Sarkin Kano Ya Dauki Nauyin Jinyar Mahaddacin Kur'...
      • Rahma Sadau Ta Yi Aman Wuta, Ta Bayyana Munanan Ha...
      • Za A Yi Dokar Gwajin Ƙanjamau Kafin Aure A Jihar Kano
      • Photos: Sabin Hotuna Mansurah Isah
      • Graphic Photos: Wasu Yan Daba Sun Kashe Wani Matas...
      • Photos: Mata Sama Dubu Hudu Ne Suka Canza Sheka Da...
      • Photos: Sabin Hotuna Zahra Buhari Da Mijinta Ahmed...
      • Ana Daf Da Fara Gwabzawa Tsakanin Koriya Ta Arewa ...
      • Shugaba Buhari Ya Shilla Birnin Landan A Daren Jiy...
      • Video: ZAFI BY BOC MADAKI OFFICIAL VIDEO
      • Boko Haran Ta Sake Sakin 82 Daga Cikin 'Yan Matan ...
      • Photos: Mahaddacin Kur'ani Na Bukatar Agajin Gaggawa
      • Photos: An Kama Fasto Da Kokon Kan Mutum
      • Gwamnati Za Ta Dauki Ma'aikata 47,000 Don Gyaran H...
      • Video: First Look Of Adam A Zango Daughter Murjanatu
      • Rashin Lafiyar Buhari Bai Yi Tsanani Yadda Ake Zat...
      • New Video: Fateema By Bala Usher Official Video
      • Photos: Mawaki Banky W Na Shirin Angwancewa
      • Video: Yau Za A Fara Daukar Cigaba Fim Din Dan Kuka
      • Buhari Ya Samu Sauki Zai Kuma Ci Gaba Da Mulkin Ni...
      • (List) Jadawalin Sunayen Malaman Izala Da Jihohi D...
      • New Music: BA RUWAN MU BY DEEZELL FT. MORELL, CLAS...
      • Obasanjo, IBB Da Abdulsalami Sun Yi Ganawar Sirri ...
      • Video: BOC Madaki ZAFI Music Teaser
      • Karnukan Gidajen Gwamnoni Sun Fi Ma'aikatan Jihohi...
      • Photos: Fitaccen Dan Fim Din Hausa, Malam Waragis ...
      • Video: Shagulgulan Auren Mawaki Nura M. Inuwa
      • Dalilin Da Ya Sa Muka Kama Sule Lamido – ‘Yan Sanda
      • Hukumar Kwastam Ta Kama Buhunan Shinkafa 377
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ►  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ►  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Suspect - Episode 1 ( Dj Giggs ft J Prince ft Nabs Kid) Hausa HipHop Ser...
  • Innalillahi wainna illaihin rajiun - Allah Yayi Wa Mawaki Aliyu Sharba R...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • (New Music) Reason By Peevibes
      PeeVibes - Reason Williams Akinsola Precious Popularly known as peevibes has returned again with this mind blowing song tagged “Reason”. T...
  • Barrister Aysha Ahmad - Kira Da Babban Muryan ( Akan Fyade Da Cin Zarafi...
  • Yadda Kotu Ta Daure Bobrisky Watanni Shida Ba Tare Da Zabin Biyan Tara Ba
    Kotu ta daure Bobrisky watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba Babbar kotu a jihar Lagos ta yanke hukunci ga Idris Okuneye da a...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger