1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Hausa Article » Kisan Gilla Da Aka Yi A Ile Ife Da Matsaloli Masu Tasowa

Kisan Gilla Da Aka Yi A Ile Ife Da Matsaloli Masu Tasowa

By Abdul Mk
Add Comment
Thursday, 16 March 2017

Daga Mahmud Isa Yola

Mu muna nan ne a Arewa ba a jihar Osun ba. Amma labarin da yazo mana shine: wani dan Arewa matashi ya mari matar wani Taana (kuyi hakuri na kira shi da sunan Taana saboda shine ƙurewa a kasanci) a bakin shagon ta. Daga nan ita kuma ta kira mijin ta Tana ta sanar dashi abunda ke faruwa shi kuma ya gayyato ‘yan uwan shi, suka kashe iya abunda zasu iya kashewa cikin mutane sannan kuma suka wawuri dukiyan jama’a iya son ran su.

A cikin wannan labari akwai abubuwa guda biyu ma banbanta.

Idan da labarin ya kasance cewa wani bahaushe ya mari matar wani  bayarbe ne, sai bayarben ya zo don ramuwa, kuma ya rama mata, ko kuma ya gayyato mutanen shi suka rama wa matar kan Bahaushen da yayi marin, to wannan ba sabon abu bane kuma a matsayin shi na namji yana da hakki yabi kadun matar shi.

Amma abun ya kai ga kisan mutane wadanda basu ji ba basu gani ba har sama da mutum ashirin, wannan wani babban abu ne na daban.

Ina nufin zarcewa da suka yi har suka kashe mutane sama da ashirin, ba yana nuna wa cewa ramuwar gayya suke yi ba. Abun da wannan yake nuna wa shine dama suna cike da wadannan Hausawa dake zaune tare da su. Sun jima suna neman sanadi amma sai yanzu suka samu, wannan yasa rikicin da ya shiga tsakanin Bahaushen nan da bayarbiya nake ganin shi abu na daban. Haka kuma kisan gilla da aka yi wa Hausawa mazauna garin Sabo, cikin Ile Ife shima nake ganin shi a matsayin abu na daban.

Shi rikicin dake tsakanin matashin nan da bayarbiya rikici ne da ko yaushe ana iya samun shi tsakanin mutane biyu ko fiye, wannan yasa zakaga hatta harshe ma da hakori sukan yi sabani. Kuma ita matar idan har ya mare ta, tana da dama cikakke da zata nemi mijin ta don ita ba namji bace da zata fiskance shi.

Amma kisan gillan nan, wannan wani mummunan makarkashiya ce da dama an dade ana shirya shi, an jima ana tsumayin ranan da za’a aikata hakan akan wannan mutane, yanzu kawai an samu sanadi ne abun ya bayyana.

Sun far wa Hausawan  nan ne da niyyan kassara su na har abada, sun kona musu shaguna. sun kwashe musu dimbin dukiyoyin su, sun musu kisan wulakanci tamkar dabbobi, wasu sun sassare su, wasu sun harbe su, wasu sun kona su da ran su!

Yarbawa mazauna garin Ile Ife sun tabbatar mana da cewa duk abunda dabba zai aikata, to mutum zai iya aikata abunda ya fi shi.

Ba rayukan Hausawan nan ne kadai suka hara ba, sun hari dukiyoyin su. Da dama na karanta labaru cewa sun rasa miliyoyi kudi, wannan wadanda suka tsira da rayukan su muke magana.

Alamu sun nuna cewa wadanda suka aikata wannan aika aika sun aikata hakan ne a bisa dalili daya. Wannan dalili kuwa ba zai wuce kyashi da suke dashi akan habakar kasuwancin bakin su Hausawa ba.

Garin na Ile Ife kuma gari ne da yake da Hausawa fiye da kowani yanki a jihar Osun. Hausawa sun dade a wannan wuri, wasu ma na hasashen cewa garin Sabo gari ne da asali yake mallakan Hausawa.

Babu shakka gwamnati ta dauki matakai da suka dace kawo yanzu, to amma wannan matsala ba ta gwamnati kadai bace, matsala ce da nake gani Sarakunan gargajiyan wannan yanki ya kamata su warware.

Kaman yanda na sha fada a rubutu na cewa, mutane sun fi kusa da wadannan shuwagabanni fiye da gwamnati, kuma su din sune shuwagabannin abun da ake fada akai, wato kabilu. Wannan yasa nake gani sune ya kamata su fara kiran al’umman su su gargade su akan illan abunda suke aikatawa.

Akwai ‘yan uwan su a Arewa, yau da gobe ba abun da ya bari. Hakan da suke yi suna jefa rayuwar ‘yan uwan nasu ne cikin hatsari. Haka kuma fa idan sun manta ya kamata su tuna, Hausawan nan da suka yi wa kisan wulakanci fa ‘yan kasuwa ne da suke sayar da kayan masarufi da ba’a noma su a kudu. Idan har suka kashe su, to ina makomar masu bukatan kayakin su?

Naga wani hoton gawar wani an kashe shi a wurin sana’an shi, gawan shi na kwance akan Albasa da yake sayarwa. Abunda na fara tunawa da naga wannan shine tunda sun kashe shi, wa zai kawo musu Albasa kuma?

Yanzu haka da dama Hausawa mazauna garin, wadanda sun riga sun yi jijiya a garin suna dawowa Arewa. Wannan babban koma baya zai jawo wa ‘yan garin saboda zasu dau shekaru masu dimbin yawa suna ji ajikin su ta fannin kasuwanci.

Kisan gilla wa wata kabila ko wace iri ce ba karamin illa bane ga cigaban kasa. Yin hakan da farko zai kara sanya gaba ne cikin zukatan wadanda abun ya shafa, sannan kuma zai kara janyo wata baraka a kasa. Kuma rikicin idan an fara shi zai rika tafiya ne ba iyaka. Wanda aka ci gaplaba akan ta zata koma shirya wa don ramuwa.

Al’umman kasar Nijeriya ya kamata su gane cewa, zaman lafiya shine ginshikin cigaban kasa, idan har babu zaman lafiya to kasa babu yanda zata cigaba. Idan kuma kasa bata cigaba ba, to al’umman cikin kasar suna cikin tashin hankali a koda yaushe.

Za’a iya samun marubuci a:
08106792663 (Text)
isamahmud77@gmail.com 
Facebook: www.facebook.com/mahmud.isa.752

Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Abdul Mk at 13:04
In Hausa Article
Kisan Gilla Da Aka Yi A Ile Ife Da Matsaloli Masu Tasowa Title : Kisan Gilla Da Aka Yi A Ile Ife Da Matsaloli Masu Tasowa
Description : Daga Mahmud Isa Yola Mu muna nan ne a Arewa ba a jihar Osun ba. Amma labarin da yazo mana shine: wani dan Arewa matashi ya mari matar wani ...
Rating : 5
Related Posts: Hausa Article

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Kisan Gilla Da Aka Yi A Ile Ife Da Matsaloli Masu Tasowa"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ▼  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ▼  March (14)
      • Morell Robbed In Abuja Last Night
      • Buhari Ya Nada Sabbin Ministoci Guda Biyu
      • New Music: Personal Lady By Ghoskid
      • Photos: Aliko Dangote Host Ganduje In Lagos
      • Yadda Ake Yawo Da Hankalin 'Yan Nijeriya
      • Allah Yayiwa Mahaifiyar Samira Saje Rasuwa
      • Ban Yi Nadama Kan Wasikar Da Na Rubutawa Buhari Ba...
      • Wasu Dattawan Arewa Sunyi Allah-wadai Da Mulkin APC
      • New Music: Sai Munkai By Dking ft Sanity
      • New Music: Mazaje By Master ft Dexter
      • Photos: El-Rufai Inspects The 150MLD Zaria Water E...
      • Kotu Ta Bada Belin Andrew Yakubu
      • Kisan Gilla Da Aka Yi A Ile Ife Da Matsaloli Masu ...
      • Photos: Nuhu Abdullahi Zai Kashe Naira Milyan Goma...
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ►  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ►  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Suspect - Episode 1 ( Dj Giggs ft J Prince ft Nabs Kid) Hausa HipHop Ser...
  • Innalillahi wainna illaihin rajiun - Allah Yayi Wa Mawaki Aliyu Sharba R...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • (New Music) Reason By Peevibes
      PeeVibes - Reason Williams Akinsola Precious Popularly known as peevibes has returned again with this mind blowing song tagged “Reason”. T...
  • Barrister Aysha Ahmad - Kira Da Babban Muryan ( Akan Fyade Da Cin Zarafi...
  • Yadda Kotu Ta Daure Bobrisky Watanni Shida Ba Tare Da Zabin Biyan Tara Ba
    Kotu ta daure Bobrisky watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba Babbar kotu a jihar Lagos ta yanke hukunci ga Idris Okuneye da a...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger