1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Hausa Article » Labarai » Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Kwamishinan Yan Sanda Na Jihar Kano

Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Kwamishinan Yan Sanda Na Jihar Kano

By Abdul Mk
Add Comment
Thursday, 17 November 2016

Daga Khadija Garba Sansui

DANGANE DA RIKICIN KWANKWASIYYA DA GANDUJIYYA

Bayan daruruwan gaisuwa a gare ka da fatan kana cikin Koshin lafiya, ya aka ji da ayyukan ofis?

Maigirma Kwamishina na zabi hanyar rubuta maka budaddiyar wasika ne domin tunatar da kai wasu muhimman abubuwa da m al'ummar jihar Kano suke ganin laifin rundunar ka akai. Dangane da rikicin tagwayen Kungiyoyin siyasar nan na Kano Kungiyar da ba sa ga maciji da juna, wato Kungiyar Kwankwasiyya ta magoya bayan tsohon Gwamnan Kano Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso da kuma Kungiyar Gandujiyya ta magoya bayan gwamnan Kano mai ci Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Saboda ba ni da wata hanya da ta wuce wannan.

Ranka ya dade rikicin wadannan kungiyoyi na siyasa a jihar Kano wato Kwankwasiyya da Gandujiyya ba sabon labari bane a kunnuwan rundunar 'yan sanda ta jihar Kano domin sau da dama mukan jiyo sanarwar haramta wasu tarurruka na wancan Kungiyoyi daga rundunarku saboda kare lafiya da dokiyar al'ummar Kano.

Saidai abunda ya daurewa ire-ire na kai shine yadda wancan haramcin yake aiki akan Kungiya daya tal wato kungiyar Kwankwasiyya. Ba mu taba jin kun haramta taron Gandujiyya ba duk da cewar kuna sane da irin tashin hankali da taron wancan kungiya yake haifarwa a Kano.

Ranar 20 ga Watan Agusta da ya gabata kungiyar Kwankwasiyya ta shirya taron aurar da Zawarawa 100 amma kwatsam sai muka ji rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta hana wannan taro, saboda wai ya yi daidai da ranar da Gandujiyya za ta gudanar wani taron tallafawa matasa 1000 da kayan sana'oi kuma duk da cewar yan Kwankwasiyya sune suka fara neman iznin gudanar da nasu taron kafin yan Gandujiyya su nema daga rundunar ku kuma kuka lamuncewa Kwankwasiyya ta je ta yi taronta, amma daga baya kuka ce kada Kwankwasiyya ta yi taron saboda dalilin da na fada a sama,

Hakan ya sa 'yan Kwankwasiyyar suka ce to ku ba su dama su gundar da nasu taron ranar 21 ga wata amma shi ma fafur rundunar 'yan Sanda ta ki yarda, karshe ma kuka ce gaba daya taron kun hana shi har illama sha Allahu. Haka nan 'yan Kwankwasiyya suka hakura aka daura auren a Msallatai daban-daban na cikin birnin Kano ba tare da da gudanar da taro ba.

Abunda ya kara bawa Kanawa mamaki shine yadda rundunarka ta Yan Sanda ta rufe gidan tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso wanda a ciki ne aka ajiye kayan dakin wadancan Zawarawa, bugu da kari har kwanan gobe ba mu ji inda Gandujiyya suka gudanar da wani taro na taimakawa matasa da kayan sana'oi ba. Dalili kenan da ya sa mutanen Kano suke fadin cewar dama hada baki aka yi da rundunarka ta Yan sanda domin hana wancan bikin Aure na Zawarawa.

Ranka ya dade Kwamishina ba wai iya wancan taron Kwankwasiyya na bikin Zawarawa kawai Rundunarka ta hana Kwankwasiyya ba, akwai tarurruka masu dumbin yawa da kuka hana kungiyar kwankwasiyya amma na dauki iya wancan ne domin na kafa Hujja dashi.

Yallabai na san kana sane da da wasu tarurruka a Kungiyar Gandujiyya take yi a ofishin jam'iyyar APC na Kano dake kan Titin Maiduguri kuma ka san yadda tarurrukan suka zamo barazanar zaman lafiyar mutanen wannan yanki, saboda babu wata rana da za'ayi wannan taro baka ga nau'i-nau'i na muggan makamai ba suna walankeluwa a wannan wuri kuma a gaban Jami'an rundunar 'yan sanda ta Jihar Kano ake daga wadannan makamai amma ba mu taba jin muryar rundunar tana Allah wadai da wancan taro ba ballantana har takai ga an dakatar dashi ko kuma rufe ofishin gaba daya ba, duk da cewar wata ranar ma riga a hannu takalmi a hannu mahalarta wannan taro suke barin wurin.

Wata ranar kuwa ma sai an yi wa wasu jina-jina saidai kaga motocin asibtin suna zaryar diban wadanda aka raunata, amma duk rundunarku ta yi shuru ta ki cewa uffan akai. To yau dai an yita ta kare domin a wajen wannan taro da aka gudanar yau Laraba 16/11/2016 an samu mummunar tashin hankali wanda rahotanni suke cewa ya yi sanadiyar rasa rai bayan jikkata al'umma da dama sakamon sakacin rundunar ku ta 'yan sanda.

Gaskiyar Lamari yanzu al'ummar jihar Kano da makota sun zuba idanu su ga wanne hukunci za ku dauka. Shin za ku dakatar da gudanar wancan tarurruka ne ko kuwa za ku ci gaba da zuba idanu ana wasan kura da zaman lafiyar al'ummar wannan yanki?

Allah dai masani ne akan komai kuma ya yi alkawarin yi wa kowa sakayya akan abunda ya shuka a wannan duniyar walau mai kyau ko akasin haka ranar da dukkan halittu za su taru a kotunsa.

Khadija Garba Sanusi Bauchi ita ce
Mataimakiyar Shugabar Mata ta kasa a Kungiyar Kwankwasiyya.

Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Abdul Mk at 09:02
In Hausa Article, Labarai
Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Kwamishinan Yan Sanda Na Jihar Kano Title : Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Kwamishinan Yan Sanda Na Jihar Kano
Description : Daga Khadija Garba Sansui DANGANE DA RIKICIN KWANKWASIYYA DA GANDUJIYYA Bayan daruruwan gaisuwa a gare ka da fatan kana cikin Koshin lafiy...
Rating : 5
Related Posts: Hausa Article, Labarai

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Kwamishinan Yan Sanda Na Jihar Kano"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ►  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ▼  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ▼  November (108)
      • Buhari Na Shirin Soke Auren Yar Sa Zahra Da Ahmad ...
      • Za A Yi Gwajin Sabon Maganin Kanjamau A Afirka Ta ...
      • Photos: Wani Dalibi Yayi Barazanar Kashe Mallamin Sa
      • An Dakatar Da Karin Kudin Data
      • Tinubu Gagarabadan APC Ne - Buhari
      • Hanyoyi 7 Da Zaka Kare Kanka Da Facebook Dinka Dag...
      • Dalilin Da Ya Sa NCC Ta Umarci Kamfaninnikan Wayoy...
      • An Alakanta Wutar Dajin da ta Mamaye Kasar Isra’il...
      • Photos: Chika Ike Sanye Da Rigar Naira Miliyan Biyu
      • Buhari Ya Bada Umarnin A Fara Shigo Da Danyen Mai ...
      • Photos: Kayan Lefen Zahra Buhari
      • Sojoji Sun Kashe Mayakan Boko Haram 30 A Gwoza
      • Takaddama Kan Gina Masallatai A Jihar Jigawa
      • APC ta lashe zaben gwamnan jihar Ondo
      • Shekarar 2017 Za Ta Kasance Abin Farin Ciki Ga 'Ya...
      • Photos: Mummunar Yanayin Wajen Kwana 'Yan Bautar K...
      • Tsohon Shugaban Cuba Castro Mai Shekaru 90 Ya Rasu
      • Ni Musulmi Ne Amma Ina Son Zuwa Coci - Bobrisky
      • Rundunar 'Yan sanda Ta Girke Manyan Makamai A Jiha...
      • Mikel Obi Zai Bar Chelsea
      • Gidaje Miliyan Biyu Za Su Samu Takardun Mallaka A ...
      • An Bukaci A Daure Eto'o Na Shekara 10
      • Za A Iya Fuskantar Karancin Abinci Sakamakon Fita ...
      • Wani Farfesa Dan Shi'a Ya Kalubalanci Masu Kyamar ...
      • Obasonjo Ne Ya Fi Kowa Laifin Cin Hanci A Nijeriya...
      • Buhari Ya Taya Atiku Murnar Cika Shekaru 70
      • Iyalan Tshon Ministan Da Aka Sace Sun Yi Waya Da W...
      • Ya Rasu Yayin Aikin Hajjin Da Ta Gabata Amma Gawar...
      • Gwamnatin Zamfara Kafa Dokar Hana Amfani Da Budadd...
      • Sunlight Laraba’s World TV Drama: Rivalry Between ...
      • Photos: Ganduje Ya Kaddamar Da Kasafin 2017
      • Najeriya Ta Daukewa Dangote Biyan Haraji
      • Buhari Zai Tsaya Takara Shugaban Kasa A Zaben 2019
      • Za A Fara Karbar Haraji Daga Masu Buga Wayar Salul...
      • Ba Ma Zargin Atiku Da Aikata Wani Laifi - Gwamnati...
      • Photos: Daga Wajen Bikin 'Yar Atiku Abubakar...Ruk...
      • Zahra Buhari Za Ta Auri Ahmad Indimi
      • Photos: Aliko Dangote Ya Ziyarci Sabon Gidan Su Ps...
      • Sojojin Nijeriya Sun Kashe 'Yan Boko Haram Da Dama...
      • Photos: Kashim Shettima Ya Ziyarci Iyalan Kanal Ab...
      • Jihar Zamfara Na Bukatar Agajin Gaggawa Akan Matsa...
      • Photos: Buhari Da Gwamnonin APC,Sun Dira Jihar Ondo
      • Za A Kafa Hukumar Rage Radadin Talauci A Nijeriya
      • Direbobin Manyan Motoci Za Su Shiga Yajin Aiki Sab...
      • Graphic Photos: Dan Sanda Ya Bindike Wani Majinyac...
      • Photos : Jami'an Tsaro Sun Rushe Sabuwar Husainiyy...
      • Photos: An Rusa Makarantar 'Yan Shi'a Dake Zariya
      • Tsohon Gwamnan Jihar Abia, Orji Kalu Ya Sauya Shek...
      • Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Kwamishinan Yan Sanda Na...
      • Yawancin 'Yan Boko Haram Ba 'Yan Nijeriya Ba Ne, I...
      • Photos: Inyamura Guda Uku 'Yan Gida Daya Sun Musul...
      • Mayakan Boko Haram 1000 Sun Mika Wuya
      • An Kara Wa'adin Amfani Da Whatsapp A BlackBerry
      • Son Mulki Ko Ta Halin Kaka Ya Sa Atiku Bai Mutunta...
      • Dalilin Da Ya Sa 'Yan sanda Suka Kashe 'Yan Shi'a ...
      • Graphic Photos : Ga Yanda Aka Yi Ma Barawo A Legas
      • Video: Sadiq Zazzabi Ya Yi Waka Wa Kwankwaso
      • Yan Shi'a Guda Sha Biyu Da Dan Sanda Daya Sun Rasa...
      • El-rufai Ya Ba Ni Kyautar Hannun Jari Amma Naki Ka...
      • Donald Trump Ya Share Furucin Da Ya yi Akan Musulu...
      • Najeriya Zata Fara Fitar Da Shinkafa Kasar Waje - ...
      • Photos: Tyson Fury Ya Musulunta
      • Trump Da Clinton Duk Abu Daya Ne - Shekau
      • Photos: Jami'an Tsaro Sun Tarwatsa Mabiya Shi'a Da...
      • Photos: Aikin Binciken Man Fetur Ya Fara Kankama Y...
      • Ba A Baiwa Kanal Abu Ali Isasshen Hutu Ba, Cewar '...
      • Trump Ya Sake Karyata Kansa-Da-Kansa
      • Adam Zango Ya Kafa Gidauniya Domin Taimakawa Marayu
      • Photos: An Gudanar Da Zikirin Shekara A Fadar Mai ...
      • Niman Shawara: Wata Bakwai Mijin Ta Ya Hanata Haki...
      • LABARIN ABU HANIFAH DA WANI KAFIRI
      • An Kashe  'Yan Kunar-Bakin-Wake A Maiduguri
      • Tinubu Na Shirin Kafa Wata Sabuwar Jam'iyya
      • Kungiyar Izala Ta Tanadi Bilyan 1.3 Don Gina Makar...
      • Photos: El-Rufai Ya Ziyarci Iyalan Marigayi Abu-Al...
      • Photos: Ana Zanga-zanga A Kasar Amurka Kan Nuna Ad...
      • Don Allah Ku Mana Rai, Tsagerun Neja-Delta Sun Rok...
      • Allah Ne Kadai Zai Hade Kan 'Yan Nijeriya - Buhari
      • Photos: Mahaifiyar Adam A Zango Ta Ziyarci Sabon S...
      • Fasa Bututun Mai Ya Janyo Tashin Farashin Siminti ...
      • Donald Trump Ya Zama Sabon Shugaban Kasar Amurka
      • Ina So Nayi Aure Amma Lokaci Ne Bai Yi Ba - Hadi...
      • An Kashe Mutane 40 A Wata Mahakar Zinari A Jihar Z...
      • Sojoji Sun Kashe 'Yan Boko Haram Guda 13 A Garin K...
      • Majalisa Ta Yi barazanar Bada Umarnin Cafke Shugab...
      • Sarkin Musulmi Bai Gayyace Ni Bikin Cikarsa Shekar...
      • Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mutane 5 A Jihar Ekiti
      • Allah Yayiwa Mahaifiyar Abdul Amart Rasuwa
      • Yan Fashi Sun Yi Wa Tawagar Amarya Fyade A Jihar ...
      • Photos: Ali Nuhu Tare Da Yan Wasan Leicester
      • Photos: An Karrama Hadiza Gabon A Birnin Landan
      • Photos: Ali Nuhu Ya Ziyarci Ahmed Musa A Ingila
      • Photos: An Sake Gano Daya Daga Cikin 'Yan Matan Ch...
      • Photos: Yan Boko Haram Sun Kaiwa Sojoji Farmaki
      • Abdullahi Dikko Inde ya dawo da Naira Biliyan 1
      • Kimanin Mutum Dubu 700 Na Neman Guraben Aiki 500 A...
      • Me Ya Jawo Hargitsi A Masallacin Sultan Bello Kaduna?
      • Har Idan Trump Ya Lashe Zabe Lallai Duniya Zata Sh...
      • Yan Sanda Sun Kashe Yan Fashi Biyu A Musayar Wuta
      • Sojoji Sun Ceto Wani Matashi Daga Hannun Masu Sata...
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ►  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Suspect - Episode 1 ( Dj Giggs ft J Prince ft Nabs Kid) Hausa HipHop Ser...
  • Innalillahi wainna illaihin rajiun - Allah Yayi Wa Mawaki Aliyu Sharba R...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • (New Music) Reason By Peevibes
      PeeVibes - Reason Williams Akinsola Precious Popularly known as peevibes has returned again with this mind blowing song tagged “Reason”. T...
  • Barrister Aysha Ahmad - Kira Da Babban Muryan ( Akan Fyade Da Cin Zarafi...
  • Yadda Kotu Ta Daure Bobrisky Watanni Shida Ba Tare Da Zabin Biyan Tara Ba
    Kotu ta daure Bobrisky watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba Babbar kotu a jihar Lagos ta yanke hukunci ga Idris Okuneye da a...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger