1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Hausa Novels » Kazamar Gida Part 12

Kazamar Gida Part 12

By Abdul Mk
Add Comment
Tuesday, 29 December 2015
Duk da kallon da yake binta dashi na tsantsar mamaki,wannan bai hana Ladi k'ara nufoshi ba dauke da murmushinta wanda ya sauya kama zuwa na mai nishin kashi.
"Assalamu alaika yaya j."
Tayi namijin kokari wajen yin furucin sallama gareshi,yayindaJafar yayi mutuwar tsaye ba tare daya iya amsawa ba. Ya d'ago yatsansa ya nunata
"Ladi!! Kada dai ace kece Hadiyya?!"
zuciyarta na fat fat,ta daure ta runtse idonta
"Kayi hakuri yaya j,kwarai kuwa nice Hadiyya."
"No!!! I cnt believe it! Ladi meke faruwa ne?"
Tuni kwallah ta cika idonta,ta waiga taga mutanen wurin harkokin gabansu kawai sukeyi. Ta fiddo wayarta ta bud'o sak'onnin da suka dunga musayarsu ga juna. Ta mik'a masa cikin rawar murya tata mik'a mishi
"Wannan kad'ai ya isheni shaida yaya j. Na rantse da Allah zuciyata bata nufinka da sharri."
Ya kalleta kafin ya sanya hannu ya karb'i wayar,ransa yayi tsananin b'aci. Jikinsa ya hau rawa,ya kauda kansa ya mik'a mata wayarta. Yayi shiru zuciyarsa na k'una,kafin ya d'ago jajayen idanunsa wadanda bacin rai ya rina ya dubeta,tuni Ladi ta soma ruwan hawaye
"Nasan ni hakika mai laifi ce yaya j,nasan nayi abunda addininmu ya haramta. Ina rokon gafararka,kayi uzuri ga zuciyar data riga ta gama tsumuwa da soyayyarka. Wallahi yaya j...."
"Dakata!! Banason jin komai daga gareki. Tsakanina dake akwai Allah! Kin cuceni Ladi,kin cuceni!"
Daga haka ya hau mashin d'insa,da sauri ta dafe kan mashin d'in har tana had'awa da hannuwansa kafin ta kautar da hannuwanta da sauri. Durkusawa tayi gwuiwoyinta a k'asa tana kuka sosai gaba d'aya 'yar kwalliyar tarbar mijin kazamatuya goge
"Kada kayimin haka yaya j,bakasan wahalar dana sha akan kaunarka ba. Yaya j bakasan yanda zuciya da gangar jikina suke azabtuwa a dalilin kaunarka ba. Yaya j rashinka a rayuwata ba k'aramin tashin hankali bane a gareni. Idan da gaske kake kanason Deeya,me zai sanyaka ka guji Ladi? Yaya j me zanyi ka yafemin laifina? Ko menene na shirya yinsa amma domin Allah kada ka barni."
Yayi tsai yana dubanta,har ta soma tunanin ya hakura saidai taji ya tayar da mashin d'insa da saurinta ta mike tsaye tana kokarin tsayar dashi. Ya girgiza kanshi
"Kin yaudareni Ladi! Bazan taba cigaba da mu amala dake ba...!"
Daga haka ya ja mashin d'insa inda yabar Ladi cikin tsananin nadama. Ta yarda SO BABBAR CUTA ne!!tom mudai du Abdool allah yaymana maganin namu chutan..!
Da gudu gudu ta shige gidansu ta fad'a jikin mamanta tana kuka. Cikin tsananin gigitaMama ta d'ago fuskarta tana salati
"Yau ni Binta na shiga uku! Ke menene? Meya faru?"
Sai kuma ta mike da saurinta ta fito waje tana lek'e amma idonta bai gane mata kowa tsaye a kofar gidan nasu ba. Ta dawo da sauri tana jijjiga kafadar Ladi
"Ki tashi ki gayamin me yayi maki? Wanene?"
Ladi ganin yanda Mama ta rud'e ya sanya ta sassauta kukanta
"Mama ki zauna zan fad'amaki komai."
Mama ta zauna jiki sanyaye
"Ina sauraronki,kiyiazamar sanar dani kada jinina ya hau."
Ta dubi mamanta
"Yaya jafar ne yazo."
Mama ta zaro idocike da mamaki
"Jafar dai na kasuwa? Menene ya kawoshi?"
Ta tambaya cike da zargi,Ladi ta daure ta zayyane mata dukkan abunda ke faruwa. Bata kai k'arshe ba taji Mama ta wanke mata fuska da kyakkyawan mariwanda ya sanya Ladi zaro ido rike da fuska tana kallon mahaifiyarta. Tunda ta taso Mama bata tab'a kai hannu kan fuskarta ba,bata tab'a yunkurin marinta ba sai yau.
"Kin bani mamaki Hadiyya! Lamarin nan ya sanyamin tsoronki! Ina maki kallon mai hankali ashe har yanzu kuruciya yana yawo a kanki?! Waye Jafar! Waye shi? Me yake dashi da har yafi sauran maza?!! Akanshi kika sab'awa Ubangijinki! Kikayi k'arya!!!! Ashe zaki iya aikata abu har haka ba tare da sanina ba? Ina tarbiyyar dana kwashi shekaru ina baki? Akan soyayya kinyi fatali da ita?!! Wace riba kika tsinta da hakan? A yanzu ki fadamin me Jafar yayi maki a karshe? Wallahi kin bani kunya! Ba shakka kin zamo mini abun tsoro,matukar auren kikeso dole ne ayi maki tunda har zaki iya wannan aikin akan da'namiji!!!!"
A fusace Mama ta fad'a d'akinta. Nan ta bar Ladi tana rusa ihun kuka,tana mai cike da dana sanin biyewa zuciyarta. Ashe ba'a soyayya ta dole? Bata yiwuwa da k'arya? Tabbas mafi yawan son da za'a dunga karyace karyace babu komai a karshensa sai bakin ciki da bala'o'i.
Gaba d'aya taji ta tsani kanta,ta tsani aikin data aikata. Yanzu meye ribarsa? Wane sakamako ta tsinta a karshe?
"Astagfirullah!"
Ta fad'a a fili sannan ta mike tayi d'akin.
******
Allah ne Ya tserar dashi. TaimakonSa ne ya maidoshi gida lafiya. Dakyar ya iya bud'e d'akinsa ya shiga.
Zubewa yayi a k'asa yana mai sauke ajiyar zuciya akai akai. Zafi yakejin zuciyar tana masa, damuwa da bakin ciki sun tarar masa. Har lokacin bai bar ganin yanda lamarin ya kasance ba a idonsa. Wani sa'in sai ya d'auka ko mafarki yakeyi. Ashe daman Ladi ce Hadiyya?!!! Innalillahi
Ya dafe kansa da hannu biyu ya runtse ido a yayinda yakejin ya tsani abunda ta aikata! Ladi kam ta cuceshi. Kafin kace me,tuni kansa ya soma sarawa. Duk da hakan bai bar cigaba da matsawa kwakwalwarsa da tunani ba. Kalamanta suna yawo a kwakwalwarsa,dayanda suke daukar lokuta mai tsawo suna hirarraki duk zantukan soyayya. Oh Jafar! Har tsawon wane lokaci ya dauka yana soyewa da Ladi mai abinci?.
Toh wai ma ya akayi ta samu lambarsa? Yayi shiru yana tunanin,nan da nan ya tuna ranar da Ladi ta nemi lambar wayarsa.
Ya lumshe ido yana dafe goshinsa
"Ya Salam!"
Ya fad'a a bayyane,wayarsata soma k'ara ko kallonta baiyi ba har ta tsinke aka k'ara kira. Ya duba,ganin Siyama ce ya sanyashi d'agawa dakyar.
"Ina jinki Siyama."
Ta ja tsaki
"Bacci ka soma ma? Lallai Jafar,kana sane cewar yau gaba d'aya bakayi kirana ba bayan kasan na kusa arba'in gashi har yanzu bakayi batun dinkunan da akeyi na yawon arba'in ba."
Damuwa ta k'ara yawaita,ya rufe idanuwansa yana mai cije lebbansa na k'asa kafin ya samu damar furzar da numfashi
"Kina neman ninkamin damuwa akan wacce nake ciki. Please whatsoever ki bari da safe sai muyi maganar yanzu ina fama da ciwon kai. Ya Faruk?"
Maimakon ta amsa sai ta hau magana cikin zafi zafi
"Ba damuwarka bace,da ace ka damu dashi ai da babu abunda zai hanaka kirana da safe. Wallahi Jafar duk wasu take taken ka a kwanakin nan ina lura dasu. Duk ka bi ka chanja,yanzu don Hajiya tace ka bar zuwa laifi tayi ne? Na tabbata yanzu baka damu da...."
Yayi azamar kashe wayarshi gaba d'aya domin hakika bashi da wannan lokacin na sauraron shirme da shiriritar Siyama,abubuwandake gabanshi ma matsala ce babba. A daddafe yayi sallar isha'i sannan ya kwanta. Nan ma zuciyarsa tace bai isa ba,bazai barta da damuwa ba idanuwansa su runtsa,duk sanda zai rufe ido fuskarta yake gani. Ga tsananin ciwon da kanshi yakeyi dole saida ya mik'e ya sha magani.(hmm angayamai so wasane!)inbesaniba yatan bayiAbdool......
Lokacin ko karfe tara batayi ba ma hakanan bashi da karfin da zai k'ara fita daga gida.
****
Acan kuwa yana katsewa Siyama kiran,tayi kwafa ta k'ara bibiyarsa saidai cikin rashin sa'a wayar a kashe. Rumaisa wacce bata sati d'aya bata zo gidan ba,tana daga zauna akan kafet ta dubeta fuska a daure
"Ya kukayi?"
Siyama ta dubeta
"Bansan me Jafar yake nufi ba anti,wai cewa yayi na kyaleshi yaji da damuwarshi. A karshe ma kafin nakai ga karasa magana ya kashe wayar gaba daya."
"Kajimin d'an kaza kaza!!!!,(ta antayo mishi ashariya). Lallai wuyansa ya isa yanka! Hajiya da alama bashi da niyyar bada kud'ad'en nan,gashi dai kowa a dangi zuba ido yake yaga irin kwalliyar da zata ci bayan arba'in. Haba Hajiya,kayan Siyama meye mararbarsu da tsummokarai? Banda kala uku na fitar suna da yayi,banga wasu masu kyawun fita unguwa ba a kayanta duk taci ubansu."
Hajiya dake rike da Faruk ta gama goge mishi kashi da wiper ta chanja mishi famfas ta tab'e baki tana mai nuna Siyama sakarce
"Ai kinga wannan! Wallahi duk abunda ke faruwa ita ta janyowa kanta. Ta biyewa soyayyar banza gashinan tana rayuwar bakin ciki. Don ubanta an gayamata yanzu a wannan zamanin ana yin auren wata soyayya? Soyayyar wofi kawai,ke bari kiji na fadamaki nan da kike ganina ban yarda na auri ubanku ba saida na tabbatar yana da gidan rana. Allah Ya jikan indo(mamanta) bata tab'a runtsawa ba saida ta tabbatar na sameshi don hutu take hangomin. Ai d'an hutu sai gidan hutu. Ban tashi nasan wata wahalar rayuwa ba,family namu gaba d'aya,familin Abba Tukur babu inda ba'asan mu ba a fad'in garin nan saidai bak'o. A zamanin marigayi Abba Tukur mahaifina wane irin tashen arziki ne baiyi ba? Shiyasa bana shiri da marasa hannu da shuni. Ke kam kin yiwa kanki,har kunya nakeji kawayena da yan sa idon gidanmu su zo suga yanda kike jego da yaronki. Kin yiwa kanki Siyama,kin bashi fuska ya rainaki."
Siyama tuni ta soma hawaye,ita kam tana son mijinta batajin dad'i zantukan Hajiya saidai fa akan dinkunan nan za'ayita da Jafar. Domin kuwa dole ne ya bayar da kud'ad'e.
Rumaisa tace
"Yanzu Hajiya dai kiyi mishi magana don Allah."
Hajiya ta mike ta kwantar da yaron a gadonshi
"Shikenan,gobe zan nemeshi."
Daga haka suka shiga hira,duk munanan shawarari suke bawa Siyama akan Jafar. Kiran da Abba ya shiga kwalawa Hajiya ne ya sanyata fita da sauri. Sukayi shiru a tsorace Allah Ya baijisu ba dai.
Fuska a had'e ya dubi Hajiya
"Ina Rumaisa?"
Hajiya ta juya ta kwala mata kira,a d'arare ta fito daga d'akin,yaronta na uku,Mannir yana tare da Abba. Ta durkusa
"Gani."
"Wallahi daga yau kika k'ara zuwa gidan nan a kwanakin nan sai na sab'a maki! Wannan ai sakarcin banza ne,ace ganin mijinki matafiyi ne shikenan daga haihuwa kinyita min zarya a gida? Toh ina mai tabbatar maki zan b'ata maki rai wallahi!! Ki tashi ki ja yaranki ku barmin gida.! Munafuka kawai!! Ina sane da halayyarki,duk rashin kunyar da kike yiwa kishiyar surukarki da ita kanta surukar taki duk yana dawowa kunnena! Bari shi Nuran ya dawo,tunda yana tsoranki ni zanyi maganar!"
A fusace yayi d'akinsa ya barsu anan jugum jugum,da gudu gudu Rumaisa ta had'a kawunan yaranta su biyar ras suka tafi.👬👭
Good morning my b loves frnds...!
Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Abdul Mk at 21:15
In Hausa Novels
Title : Kazamar Gida Part 12
Description : Duk da kallon da yake binta dashi na tsantsar mamaki,wannan bai hana Ladi k'ara nufoshi ba dauke da murmushinta wanda ya sauya kama zu...
Rating : 5
Related Posts: Hausa Novels

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Kazamar Gida Part 12"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ►  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ►  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ▼  2015 (2312)
    • ▼  December (182)
      • Kungiyar Kare Hakkin Musulmi Ta Kasa Ta Mayarwa Da...
      • An Sace Wata Yar uwar Goodluck Jonathan
      • Kalaman Buhari Akan Sambo Dasuki
      • Kazamar Gida Part 13
      • Photos: Onazi A Wajen Siyan Kosai
      • Zainab Indomie Tana Raye Ba Ta Mutu Ba
      • Na Sha Jan Kunnen Sheik Zakzaky Kan Tare Hanya A Y...
      • Gobe Za A Yi Tattaunawar Kai Tsaye Da Shugaba Buhari
      • Photos: Anyi Hukunci Ma Wasu Mutane Guda Biyu Da S...
      • Waya Kashe Ta Part 2
      • Majalisar Dattawa Zata Gudanar Da Binciken Zariya
      • Kazamar Gida Part 12
      • Photos: An Sa Ranar Auren Yar Sanusi Lamido Sunusi...
      • Jam'iyyar APC Ta Jihar Kaduna Ta Dakatar Da Sanata...
      • Sanata Shehu Sani Ya Mayar Da Wasu Marayu 60 A Mat...
      • ILLAR Cin Mutuncin Dan'uwanka Musulmi
      • Kazamar Gida Part 11
      • Naushi Daya Na Yi Wa Abokina Ya Mutu
      • Dan Wasan Kwallo Kafa Nassarawa United Ya Rasu
      • Su Dawo Da Kudaden Da Suka Sata Ko Kuma Su Fuskanc...
      • Wa Ya Kashe Ta? Part 1
      • Photos..Nafisah Abdullahi A Dubai
      • Sojojin Najeriya Sun Kashe Yan Boko Haram 10
      • A Kalla Sama Da Mutane 20 Suka Rasa Rayukansu A Ha...
      • Za Mu Baiwa 'Yan Bangar JTF Damar Shiga Soja, - Ja...
      • Ban Je Kasar Dubai Domin Yi Wa Buhari Makarkashiya...
      • Graphic Photos : An Suka Wani Mutum Wuka A Egbeda
      • Tsohon Dogarin Osama Bin Laden ya rasu
      • Man Fetur Zai Wadaci Jama'ar Kasa Har Ya Zarce Buk...
      • Ya Kamata A Haramta Akidar Shi'a, Sakon Mazauna Ga...
      • Photos:An Bawa Aisha Buhari Wani Kyauta Hoton Buha...
      • Gwamna ElRufai Ba Zai Tada Masu Sayar Da Kilishi D...
      • Video: Epl Highlight Southampton 4 Arsenal 0
      • Batun Kudi Bai Taba Shiga Tsakanina Da Dasuki Ba, ...
      • Musulmai Da Kiristoci Sun Taya Juna Murnar Maulidi...
      • Photos:Anyi Bikin Yaron Burutai Yau
      • Video: Highlight Stoke City 2 Manchester United 0
      • Photos: Wanda Yafi Kowa Kiba A Duniya Ya Mutu
      • Photos:Zahra Buhari Da Takalma Dubu Dari Biyu
      • Hotunan Bikin Kirsimeti A Sansanin 'Yan Gudun Hiji...
      • Indan Baki Dawo Min Da Abinda Kika Dauka Ba Na Sakeki
      • Rikicin Yan Shi'a: Bincike Ne Ya Hana Ni Magana - ...
      • Mutane 8 sun rasu sakamakon gobara a matatar iskar...
      • Ladanin Masallaci Makkah Ya Rasu
      • Buhari Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa 85
      • Graphic Photos: Sama Da Mutane 100 Sun Koke Anambra
      • Photos: Aisha Buhari Ta Ziyarci Asibiti A Ranar Ch...
      • Photos: Buhari Da Jikokin Sa A Ranar Christmas
      • Yan Shi' Sun Zargi Gwamnatin Jihar Kaduna Da Rushe...
      • Addu'ar Mu A Kullum
      • Photos: Happy Birthday Ibrahim Birniwa
      • [Photos] Yan Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Jihar Kano
      • Ku Daina Sukar Gwamnatin Buhari, Sakon Jam'iyyar P...
      • Buhari Ya Warewa Tsoffin Shugabannin Kasa Naira Bi...
      • Ana Ci Gaba Da Karancin Man Fetur
      • An Haramta Shagulgulan Kiristimeti A Kasashen Brun...
      • Majalisar Matasan Musulman Nijeriya Ta Lashi Takob...
      • Babu Shugabancin APC A Kaduna, Saidai 'Yan Amshin ...
      • Shugaba Buhari Ya Gabatar Da Kasafin Kudin Shekara...
      • Rashin Taka Rawar Gwamnatin APC Zai Iya Sanya Wa P...
      • Da Akwai Lauje Cikin Nadi, Akan Batun Tsare Zakzak...
      • Buhari ya bayar da hakuri kan matsalar fetur
      • Jonathan Ne Silar Wahalar Man Fetur Da Ake Ciki A ...
      • Video:Download Highlight Arsenal 2 Manchester City 1
      • Dasuki Na Ci Gaba Da Zama A Gidan Kurkukun Kuje
      • Photos: Likitoci Sunyi Nasarar Raba wasu Yara Da A...
      • Kwamitin Bincike Ya Wanke Wani Da Aka Sanya Hotons...
      • Gwamna El-Rufa'i Masoyin Mutane Ne'
      • ATM din Nigeria zai daina aiki a kasar waje
      • Graphic Photos: Sojojin Nijeriya Sun Kashe Amir Di...
      • Bisine Daruruwan 'Yan Shi'a A Wagegen Rami Bayan K...
      • Yadda dan kasuwa ya hallaka matashi wajen cire kod...
      • FIFA ta dakatar da Blatter da Platini na tsawon sh...
      • An Sace Kanwar Gwamnan Bayelsa
      • Video: Download Highlight Real Madrid 10-2 Rayo Va...
      • Sheikh Dahiru Usman Bauchi Yayi Magana Akan Rikici...
      • Maganin Ciwon Sanyi
      • Yan mata Ya Labarin Kwalliya A Lokacin Hunturu
      • Yan Sanda Sun Cafke Masu Kera Makamai A Jigawa
      • yan sanda sun saki mabiya shi`a
      • Photos:Hotuna Daga Wajen Bikin Murna Ranar Haihuwa...
      • Photos: Yan Shi'a Su Na Zanga-Zanga A Jihar Gombe
      • Rundunar 'Yan Sanda Ta Kori Gurbatattun Jami'anta ...
      • Photos: Ambode, El-Rufai Da Sarkin Kano Awajen Wan...
      • El Zakzaky Ba Ya Hannunmu, Inji Buratai
      • Photos: Fasto Mbaka Ya Ziyarci Buhari
      • Graphic Photos: Mutane Biyar Sun Rasa Rayukansu Ya...
      • Photos: Hotunan Yaran Sarkin Kano Akan Doki
      • An Karbi Beli Dasuki Da Saura Mutane 4
      • Tafsir: Tattalin Domin Ranar Mutuwa By Sheikh Ahma...
      • Kyautar Bikin Christmas: Halal Ko Haram
      • Photos: Aisha Buhari Ta Shiryawa Mijinta Bikin Mur...
      • An Cafke Wasu Masu Satar Mai
      • An Yi Yunkurin Juyin Mulki A Nijar
      • Diezani Tana Raye Bata Mutu Ba
      • Photos: Sabin Hotuna Zahra da Halima Buhari
      • Chelsea ta kori Jose Mourinho
      • Abin Da Shugaban Iran Ya Fadawa Buhari Akan Rikici...
      • Mutane 35 Sun Rasa Ransu A Wani Hadarin Kwale-kwal...
      • Sarkin Kano Yayi Magana Akan Rikicin Yan Shi'a
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Suspect - Episode 1 ( Dj Giggs ft J Prince ft Nabs Kid) Hausa HipHop Ser...
  • Innalillahi wainna illaihin rajiun - Allah Yayi Wa Mawaki Aliyu Sharba R...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • (New Music) Reason By Peevibes
      PeeVibes - Reason Williams Akinsola Precious Popularly known as peevibes has returned again with this mind blowing song tagged “Reason”. T...
  • Barrister Aysha Ahmad - Kira Da Babban Muryan ( Akan Fyade Da Cin Zarafi...
  • Yadda Kotu Ta Daure Bobrisky Watanni Shida Ba Tare Da Zabin Biyan Tara Ba
    Kotu ta daure Bobrisky watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba Babbar kotu a jihar Lagos ta yanke hukunci ga Idris Okuneye da a...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger